*💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅
Love story 2018
Billy galadanchi
Wattpad@galadanchi
*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)
*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*06
Jiki ba k'wari ta juya zuwa d'akinta,sam hankalin hafsat beyi yawan dazatayi zurfin tunaniba ta kasa tariyo komai,wayarta ta ciro daga k'asan filo ta kira huda,d'agawar farko tace"Huda dan Allah kina ina yanzu??" da mamaki hudan tace "Ina kan hanyar zuwa gun Ashraf tela" to yayi nima ganinan zuwa da maganar danike so muyi" kan huda tayi magana ta katse wayan,da sauri ta zari hijab tayi k'asa a hanya tayi karo da yaa shaam ko kallonshi batayiba sabida hankalinta sam baya jikinta,driver din momy ta gani tayi kiranshi da hannu,ta fada mota sukayi gaba....a shagon janyo hannun huda tayi suka dawo mota ta kalleta bayan tayiwa driver din umarni daya fita waje tace
"Huda wai da gaske sosai ni Hafsat ina san yaa shammaz??" kallon ta huda tayi cikeda nutsuwa tace
"Ban fahimce kiba?" kwashe komai tayi dataji su momy na fada ta gayawa huda ta qara da cewan "ke kadaine zaki iya fadamun gaskia dan Allah waida gaske wannan abun danaketaji gameda yaa shaam shine so? Kuma shi din suwaye iyayenshi??" sosai huda ta gano hafsat kuruciya ya mata yawa, banda haka ina zatasan su waye iyayen shaam,ni sawa tayi tace "poojah ki nutsu mana,zancen gaskiya ko shakka banayi kina san yayanki kuma sosai bawai kadanba,amma abunda nakeso dake shine kibi komai a hankali sabida kinga already an kusa aurenshi kuma tunda su momy basusan kinji maganar suba karki fadawa kowa karkuma ki nuna musu,wannan abun dakikeji idan yana waya da wacce ze aura da kuma idan ana zancen aurenshi shi ake kira kishi,kuma kishin ya miki yawa ina tausaya miki sabida tunkan kisan meye so da kishi kika fara
VOCÊ ESTÁ LENDO
BAKIN RIJIYA...ba Wurin Wasan Makaho Bane
RomanceMeya sanya arayuwa nayi rashin sa'an zuwana duniya gaba d'aya? Mesa zanso mutqaunar mutuwarsa akan Koda k'wayar idonsa ya sauke Akaina?? Mesa nayiwa Kaina wannan rashin adalcin?? Mesa wannan bakar zuciyar tawa bata dasamun San waninkaba yaa shammaz...