page 3

3.1K 210 2
                                    

     *💅BAKIN RIJIYA....ba wurin wasan makaho bane*💅

   Love story 2018

Billy galadanchi

Vote me on wattpadd@68billygaladanchi.

*HASKE WRITER'S ASSO.*(home of expert and perfect writers.)
 
*Sadaukarwa gareki qawar alkhairi ummie Aisha*

                                 03

  Hafsat kyakyawar yarinya ce fara qal me tsayin gashin kai,siririyace samb'al sedai fa ba gaba ba baya duk da yake bazamu yankewa surarta hukunciba kasancewarta yarinya y'ar shekaru goma sha hud'u wanda har yanzu bata gama hada girman jikinta ba,tana da dogon hanci me tsayin gaske da manya manyan dara daran fararen idanu masu wani d'igon zaiba zaiba aciki koda wane lokaci idanun zaka gansu a lumshe tana da d'an mitsitsin baki amma lips nata suna da dan kauri sedai ba cancanba,sosai takeda gashin gira dana girar ido baki wuluk,sannan kuma suman kanta yazo har k'asan goshinta kwance luf luf gwanin ban sha'awa......

Ilai kuwa lokacin daya fad'a lokacin ta isa jikin motarsa sanye da wando jeans blue da red top ta yane kanta da mayafi red tayi kyau matuqa,batare dayace komai ba yaja suka tafi sanda suka kama hanya sannan yace "Poojah" gabantane ya yanke yayi mugun fad'uwa jinya kirata da wannan sunan ta kasa cewa komai,hannunta ya kamo ya saka a nashi yace "kinaji ina kiranki zakimun banza,ina poojah shine sunan da friends naki suke kiranki kuma karki manta we r now friends arn't we?" murmushi tayi tace "sure mana we are" murmushin ya kuma yi

"Wane kalan waya kikeso kinsanfa ban kawo miki tsara baba shine zan fanshe" itafa sam bata sakin jikinta dashi harga Allah tsoron shi takeyi murmushin takumayi "ko wanne ma inaso" yagano a tsorace take ya sanya be kuma cewa komaiba,dasuka isa k'ofar gidansu leemah seyace tashiga ta gaisa dasu umman leemah inyaso su fito tare,ba musu tashiga gidan,da sallama ta isa har kofar parlor din amma ba wanda ya ansata haka ta danna kai ta shiga dama hafsa ba manners,tana zuwa taga ashe kowama yana zazzaune a tsakiyar parlor din suna zazzaune abinsu suna hira,yan mata ne sunfi su shida se babbar mace a tsakiyansu, kallonta kowa keyi amma ba wanda yace da ita kanzil a kasale tace "Sannunku Aunty haleemah nake nema?" babbar macen ce tace "ke wacece yarinya baki iya gaisuwa bane?" kallon matar take ta qara lumshe lumsassun idanunta tace a wahalce "Namayi kokarin ce muku sannu ai ina tundazu nake ta rafka uwar sallama kukamun banza" da mamajin furucinta umman ta miqe tsaye tace "wacece ke yarinya meye kike nema awurin haleema?" cikeda takaici tace

" yaa shaam ne yace nazo na gayarda umman matarsa daze aura haleemah, kuma yace nace ta fito su tafi inda zasun" ana haka sega haleemah tafito,kallon Hafsat tayi tace "ke meye haka lapiya?" kallonta kurun hafsat tayi tace "yaa shaam na jiranki a waje" tana kaiwa nan ta juya abinta bata ko kalletaba,da gudu taje tariqe rigar hafsa ta baya tasanya hannu ta dungure mata kai tare da kai mata ranqwashi tace "y'ar gidan uban waye me dazaki wa mutane iskanci haka ake fadar saqo" atake idon hafsat ya cicciko tace " Yar gidan uban yaa shaam ceni kuma nice qanwarsa dayake da ita hafsat,akwai wani magana ne??" da sauri leemah ta seseta kanta tace "Allah sarki hafsat kulele,ya kike wlhy ban ganekiba,nasha fitsararrun yaran unguwane ashe babbar sis ce,umma kinga qanwar shaam" tafada tana kallon umman tare da kashe mata ido daya alamar a saisaita zancen,murmushin yaqe umman ta somayi "Laa wai itace kinsan fani nafi ganewa ace shammaz sam datace shaam ban gane wa take nufi ba,kikace hafsat sunanta sannu kinji 'yata zonan kusa dani,kinga munata surutu wlhy bamuji sallamarkiba" ahaka dai suka rinqa zuba uban surutu wananna yace mata wannan wancan yace wannan,dazasu fita kuwa aka rinqa kwaso mata kyaututtuka,itadai shigowar farko dukda tanada kuruciya gidan be mataba wayannan yan matan masu zubin karuwai.....!!!! Amota kuwa leemah se janta takeyi da hira ita kuwa taqi ta saki jikinta gaba d'aya a tsure take hankalinta baya jikinta tunaninta daya yazatayi kar yaya ya auri wannan itafa lokaci daya taji ta tsaneta da yan gidansu gaba daya,haka sukaje siyan wayar yaa shaam ya siya mata iri daya dana leemah wanda atake ta fahimci cewar bataji dadi ba sabida kallonsa tayi tace "Boo me wannan qaramar yarinyar zaka siyawa danqareriyar waya irin wannan a gaskiya kunaso ku b'atata da yawa" a yanda kuma hafsat ta fahimta shima beji dadin yanda tayi ba domin kuwa be kula da zancenta ba,daganan ya siya musu ice cream da kaza ya mayarda leemah gida....tana shiga kuwa tacire mayafin ta fada tsakiyar parlon da sukecin kasuwa tace "Umma wlhy da matsala wannan shekiyar qanwar tasa itace matsalar tamu,baya shayin mata komai,kinga yawan kaza da ice cream  d'aya ya siya mana abin haushin ma wai hatta waya iri d'aya ya siya mana yarinya sekace kishiyata,ina wannan yarinyar ina riqe babbar waya har haka wlhy rashin hankali ne tsantsa,kuma tsaf maganinta zamuyi domin idan ba haka ba ita zata takurawa rayuwarmu ta hanamu cimma burinmu" gyada umman tayi tace "Ai maganin shegiya zamuyi ku barni da ita gashi sam batada kunya ko kadan wlhy amma damu take zancen!!!!

  *Washe gari pooja a bisa rashin sani tashiga interview na wayanda ke neman shiga ss3 kuma abun mamaki tazo na daya acikin su kusan 32 koda suka je bincike aka tabbatar musu taci akan ta soma zuwa on monday,monday tana zuwa taga an kaita ss3 mamaki  ya kamata tace dasu kuskure ne ita ss1 zataje su kuwa suka kafe akan ko exam datayi na ss3 ne kuma itace overall gaba daya,haka ta zauna ita kadai qaramar yarinya acikin manya kowa se tsokanarta yake dukta takura,tana dawowa gida kai tsaye part din yaa shaam ta nufa harda kukanta ta sanar masa "ke wace iriyar sakarai ce dazaki shige exam daba nakuba?" share kwallanta tayi tace "yaa shaam nifa na gaji dajirane inajin ankira badge 3 seniours sena shiga kawai ashe ss3 ne" shiru yayi yace taje se gobe,juyin duniya yayi dasu akan yarinyace amma sun dage akan bazasu mayarda overall student tasu abaya ba,seda aka qara bata exam din lapiya lau ta lashe komai dole haka ya hakura akan ta zauna din,data dawo gida yayi kiranta akan ya akayi ta iya abubuwan ss3 anan yakeji cewar a library na school dinsu har books na nursery take karantawa dana ss3 kuma abinda bata ganeba taje gun malaminsu ko principal idan besan amsaba ya hada ta da malamin dake subject din" gamsuwa yayi da bayanan yamata fatan alkhairi sannan ta juya ciki......

Mom Nua'iym

BAKIN RIJIYA...ba Wurin Wasan Makaho BaneTahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon