🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*🌼👸🏻 LAILAH-DIZHWAR 🤴🏻🌼*
*_🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷_*
*_ZAINAB NASEER SARKI_*
*_ (ZEENASEER😘)_*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸*_ViaWattpad@Zeenaseer01_*
*(20)*
*Dedicated This page to all my Whatapp Fans, love you irin sosai sosai din nan, Allah ya bar zumunci Nagode sosai da irin soyayyar da kuke nuna min Nagode*😍
__________
Cikin sauri ta shiga, tare da janyo Husna gefe, hular ta nun mata tare da fadin,
_"Wannan Hular Kamar ta Dizhwar"_Amsa tayi tare da fadin, _"itace mana"_
kamar ta nuna mata abun hannun, sai kuma tayi tunanin kar tajI kunya, aje watace ta yarda shi tunda bashi kadai yake bin hanyar bah.
_"Amma ya akai, hularsa ta fadi kamar wanda bashi da hankali be sani bah"_
_"Toh kode da gasken bashi da lafiya, kuma ina ya tafi"_
Husna ta fada.Wayarta ta amsa ta shiga kiransa amma harta gama ringing dinta be daga bah.
_"Anty Salima barshi kawai koma menene maji da safe, sabo da dolansa ai yaje wajan daurin aure, babu damuwa"_
Tana fadar haka ta shige cikin jama'a, batare da ta nuna wata damuwa sosai bah.
Binta Anty Salima tayi tana so ta tuno inda taga wannan abun hannun.
_____
Haka aka sha shagali aka tashi daga wajan Party kowa cikin farin ciki amma Banda Amarya Husna, shima Jafar ya duba amma be gansa ba, amma be nuna damuwa ba tunda yasan ai yana nan saide in waje suka fita.
Itama haka Husnar duk jarabarta ta hakura, amma tasan koma ina ya tafi gobe ahine karahe, tuda za'a daura musu aure kuma dole yaje wajan daurin auran, in yaso in sukayi auran dolansa ya gaya mata ko ina yake zuwa._______
Dizhwar kuwa saida yaji ya gamsu dari bisa dari babu wani sauran ciwo da yake ji,
Gefe ya koma ya kwanta yana maida numfashi, saida yayi kusan awa daya tukun hankalinsa ya dawo jikinsa.Da sauri ya mike zaune ganin inda yake, da sauri ya kalli gefansa, ganin Lailah yasa yayi saurin matsawa gefe.
Ganin kamar bata numfashi bare motsi yasa yayi sauran matsowa ya shiga marin fuskarta Ahankali yana saka kunansa kan kirjinta amma shiru.
_"Innalillahi wa'inna illaihir raji'un, shikenan na kashe Lailah, ashe dama nine ajalin yarinyar nan shiyasa na gaiyaceta wajan nan"_
Gaba daya hankalinsa ya gama tashi, haka yaci gaba da tashinta amma babu abunda yake motsi ajikinta, ga fyade da yayi mata, gaba daya daga shi har ita da kuma wajan ya bace da jini.Da sauri ya mike ya dauki wandansa duk da jinin da yake jiki ya saka, ya nemi kayanta ya saka mata,yanayi yana kuka dan yasan bashi da yanda zaiyi, gashi Anata sallah yama rasa yaya ziyi, gashi kayansa duk sun bace da jini balle ya fita.
Haka ya dauka ya saka,Ahankali ya bude dakin ya leka ganin babu kowa yasa ya dawo ciki, jin yataka abu ya durkusa ya dauka ganin wayarsa yasa yayi saurin dauka, dubawa yayi yaga lokacin karfe 4:03am, cikin aljihunsa ya saka tare da daukar Lailah ya matsar da ita can gefe cikin kaya ya rufeta da bargunan wajan ya fita daga cikin sakin.
Ahankali ya fita yana sauri harda gudu gudu ya nufi part dinsu, kana ganin yanda yake dube dube kasan bashi da gaskiya.
Yana zuwa dakinsu ya bude tare da shiga falon, babu kowa dan haka da sauri ya nufi bedroom dinsa.
Yana shiga yasa key ya kulle tare da cire kayan jikinsa ya shiga wanka, ya jima a bandakin kafin ya fito, alwala yayi, yayi sallah anan dan bama yasan fita daga Dakin.
Bayan ya idarnne yaji wata irin kasala ta saukar masa, amma gaba daya hankainsa baya jikinsa, banda tunanin halin da yake cike ga kuma kisa da yayi.
Mikewa yayi ya koma kan gadon ya lullube dan zazzabi yake ji ajikinsa.
______
Koda gari ya waye, Jafar fitowa yayi daga dakinsa ya nufi wajan Dizhwar dan ko ya dawo.Yana shiga kuwa ya gansa kwance cikin bargo, da sauri ya karaso wajansa tare da budeshi ya taba shi.
Zafi yaji sosai ajikinsa.
_"Dizhwar"_
Jafar ya kira sunan sa.Ahankali ya bude ido yana kallan Jafar din.
Ganin yana rawar sanyi yasa yayi maza ya rufe shi tare da kiran dr. A wayarsa.
Koda yazo ya auna shi magani ya bashi da kuma allura.
Sannan ya samu bacci.
Jafar yana nan yana faman kallansa ganin duk ya rame lokaci daya, zuwa yayi ya sanar ma da Mami abunda ya faru, nan da nan hankalinta ya tashi gaba daya gida ya dauka Dizhwar bashi da lafiya.
Nan da nan part dinsu ya cika dan ganinsa.Husna kuwa kuka take dan ganin halin da ya shiga.
Koda Anty Amarya taji labari bakin cikine ya kamata sabo da kasancewar da batayi dashi bah, itama abunda ya faru da shi itama ya faru da ita, dadde ita tana da yan iskanta waya kawai zata musu su ,suzo su biya mata bukatar tah,bakin cikinta shine da bata san dawa Lailah ya kasance bah, dan tabbas da be kusanci wata ba saiya mutu, dan haka bokanta ya gaya mata.
______
Lokacin da ya farka, nan Jafar ya lalabashi danya shirya aje wajan daurin auran.Breakfast yayi dan yaji kafin jikinsa, bayan ya gama ci, gaba daya hankalinsa yana wajan gawar nan, fita yayi waje ya samu wani yaran sa,nan ya sanar masa da wata matsalace ta faru yana so, yaje cikin dakin, yayi masa kwatance, ya dauki gawar mace kuma ya dauke dukkan wata sheda yaje ya yarda ta acan nesa da gari batare da kowa ya san da hakan ba.
Nan kuwa yayi Naam da abunda ya gaya masan._____
Bayan sun gama shirinsu cikin kayansu na alfarma suka nufi wajan daurin Auran anan masallacin gidan sarautar inda manyan mutane suka halarci wajan, dan babu masaka tsinke.Bayan an gama dukkan abunda Za'a yi, aka hada wata babbar walima.
Amma duk abunda ake Dizhwar dauriya kawai yake dan bayajin dadi har lokacin.
_______
Ita kuwa Lailah abunda aka saka wannan bawan shi yayi, ya dauketa ya nufi can hanyar Sokoto da ita ya yarda ta cikin wani daji, ya dawo gida ko ajikinsa, sannan yasa a gyara cikin dakin da Abun ya faru,
Bayan ya dawo ne ya sanar da Dizhwar din aikin gama Ya gama, sai lokacin hankalimsa ya kwanta, sannan yayi masa alkawarin kudi masu yawa, sannan karya sake ya gayawa kowa.*ZEENASEER*
YOU ARE READING
LAILAH-DIZHWAR
Romancelabarin sarauta wanda yake dauke da kishi, mugunta, sankai, butulci da kuma soyayya, yana dauke da tausayi da kuma biyayyah wa iyaye, yana dauke da dunbi fadakarwa, da kuma nasiya akan rayuwa tayau da kullum.