🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*🌼👸🏻LAILAH-DIZHWAR🤴🏻🌼*
*🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷*
*ZAINAB NASEER SARKI*
*_ (ZEENASEER😘) _*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸'''Editing by : Ameerah Zarewa'''
© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
☆We the best ☆ViaWattpad@Zeenaseer01
https://mobile.facebook.com/Real-Hausa-Fulani-Writers-forum-RHFWF-173984973194167/?refid=52&ref=opera_speed_dial&__tn__=H-REmail:realhausafulaniwritersforum@gmail.com
Facebook:www.Facebook.com/REALHAUSAFULANIWRITTERSFORUM.com*99*
_"Wannan kuma keya dama sabo da haka mude abunda muka sani shine No body is above the law"_
Cikin masifa ta shiga kiran waya, ana dagawa ta fara Kuka tana fadin,
_"Mommy nashiga uku Wai Faisal ne yayi laifi Bansan me yayi ba ga yan sanda nan da yawa a gidana, dole wai tunda basu ganshi ba sai sun tafi dani station dinsu "_Cikin masifa daga can bangaran ta furta,
_"What a disgrace?,bawa Ogan nasu wayar"_Batare da tayi magana ba ta mika masa wayar.
Saida ya kare mata kallo sannan ya amshi wayar.
_"Barka da war haka"_
ya fada bayan ya saka wayar a Loundspeaker,_"Kana magana da Matar sarkin Zamfara,Haba Yallabai, Wannan ai tozarcine, so kake ka bata mana sunan Family din mu"_
_"Ranki ya dade dokace hakan kuma kema kinsan babu wanda yafi karfin ta"_
_"Bana san maganar banza maganar wofi, ka dauki yaranka kubar gidan nan can ku nemi wanda yayi muku laifin ku"_
Shikuwa kashe wayar yayi tare da fadin, ku taho da ita.
Aikuwa suka saka ta a gaba aka fita da ita tana ta surfa bala'i.
Har sun kai bakin kofa Jafar ya kira wayar ogan nasa, Kasancewar an tura masa.
_"Yallabai barka da aiki"_
Jafar ya fada._"Yawwah, wallahi kaga gamu a gidan nasa an duba ko ina baya nan kuma mun tambayi matar tashi taki sanar mana da inda yake, yanzu zamu tafi da ita can station din mu sai muyi masa waya in aka gaya masa tana hannun mu duk inda yake ya dawo"_
_"Amma Hakan babu damuwa ranka ya dade, bana san abun yakai ga haka ade kirasan ba sai an tafi da ita bah, sai a tsareta ayi masa magana"_
_"Toh shikenan babu damuwa"_
Cewar Ogan._"Kuma ku sanar mata da abunda ya aikata inaga hakan zai sa ta fada mana inda yake"_
_"Toh, nagode"_
Nan ya juya tare da fadin, su koma ciki.
Bayan sun zauna itama ta zauna ya kalleta tare da fadin,
_"Kada kiyi tunanin rashin kunyarki da kuma matsayinki yasa aka maidoki nan, sabo da mutum daya nayi hakan, Kuma kina san kisan abunda mijinki yayi, Kidnapping matar sarki yayi wato Memartabah sarkin Zamfara Dizhwar, kuma kema kinsan da hakan tunda naga kema kina da alaka dasu"_
_"Wanene kuma yayi masa wannan sharrin yayi me da ita in yayi kidnapping dinta, wata banza Lailah, toh koma waye ya gaya muku hakan karya yake sabo da haka ku rabu dashi"_
_"Shine ya sace ta mana, saboda da bakinta ta fadi hakan, kuma shi din ne, in yasan bashi bane ya tsaya mana"_
_"Nikuma. Zan tabbatar muku da bashi yayi hakan ba balle harya dinga tsere muku"_
Tana fadin hakan ta mike, suna biye da ita, part dinsa suka nufa inda ta nufi bedroom dinsa, bakaramin mamaki tayi ba ganinshi a bude an lalata kofar.
baki bude ta juyo tana kallan Ogan nasu, da sauri tayi waje suka kuma binta.
Wajan me gadi ta nufa tare da fadin,. _"Malam iliya, Yaushe me gidan nan ya fita bayan nace kada kabar kowa ya shiga koya fita"_
_"Hajiya kiyi hakuri, shine ya kirani ya sanar dani in kira me gyaran kofa ta lalace, bayan an gyara kuma ya dauki dayar motarsa ya fita"_
Kantane ya daure ta kalli Ogan nasu tare da fadin,
_"Wallahi nina kulleshi acikin daki, sabo da akwai abunda yamun tsakanin mu, hakan yasa na kulleshi, kuma kaji ashe ya fita"_Ogan nasu kan megadin ya koma yana masa tambaya akan zaiyi awa nawa da fita, ya sanar musu ko awa daya beyi ba.
Nan suka fita daga gidan,aka nufi kan titina da hanyoyin fita daga gari duk akayi musu waya dasu binciki me Kama dashi.
Nan suka tura pics dinsa daga wayar Fareeda suka baza su aduk hanyoyin cikin garin.
______
Shikuma yana kan hanya ya kira yaransa na office kan yazo ya dawo da motarsa gida inya zo airport din.Jirgin kano yayi booking wanda zai tashi a wannan time din.
_______
Lailah ganin har Lokacin Bata kuma ganin Faisal ba yasa hankalinta ya kwanta dan ba karamin tsoransa take ji ba.Tashi tayi tayi sallah ta zauna tana ta Faman addu'a dan ita kadaice mafita a wannan lokacin datake ciki.
Tana kwance kamar yanda take daga zama sai kwanciya, aka kawo mata abincin dare.
Babu yanda ta iya dan yinwa take ji, dauka tayi taci ta koshi tasha ruwa dan ta rame sosai kamar ba ita bah.
______
Karfe 8pm Faisal ya isa garin kano, Kai tsaye family house dinsu ya nufa dan yanzu kowa kam ya hallara sabo da gobe za'a daura auransa.Amma babu abunda yake tunani sai Lailah yana san yaji yaya take, yana cikin mota ya kira yaransa da suke wajan Lailah dan yana san yaji muryarta.
Nan kuwa aka kai mata wayar.
Tana zaune abakin gadon tayi shiru aka miko mata waya.
Amsa tayi, sannan wanda aka bawa ya kawo ya tsaya daga gefe yana kallanta.
_"Hello Heartthrob, yakike nayi missing komai naki a tafiyar nan da nayi amma karki damu, gobe da sassafe ina tare dake insha Allah kici abinci kafin ki kwanta ki kula da kanki ina sanki"_
Wani bakin cikine ya turkune ta, cikin muryar kuka ta furta,
_"Faisal kaji tsoran Allah, kaifa musulmine kana ganin hakan da kayi wayone ko kuma me?, kaji tsoran Allah ka daina abunda kake, ka maidani wajan yan uwana da dangina, bazan iya zama nan bah ba.... "_Kuka ta fashe dashi dan tama rasa abun fada,
Hakan yasa baiji dadi ba, har lokacin wayar tana jikin kunan tah.
_"Na tsaneka Faisal, bana kaunar ka bazan taba sanka ba har karshan duniya, bana sanka mugu Azzalumi"_
Ta yarda wayar, dauka wancan yayi tare da fadin,
_"Oga ta yarda wayar,"__"Rabu da ita James, ka tabbata taci abinci pls"_
_"Taci"_
Ya bashi amsa._"Ok pls take care of her"_
Sannan yayi musu sallama.
Lokacin da aka saukesa a kofar gidan, saukowa yayi ya bada kudin dan be gayawa kowa zai zo din ba.
Shiga yayi lokacin me gadin ya amshi kayan hannusa, cikin farinciki ya shiga Babban falon gidan.
Duk suna zaune suna cin abinci wasu kuma suna hira ana kallo.
Cikin farinciki da tsalle aka fara murnar ganinsa harda masu rungumeshi.
Zama yayi kan kujera nan da nan aka zagayeshi ana kallansa.
______
Shikuma yaran da Faisal ya bawa motarsa bai maida masa gidansa sa ba sabo da yana da abunyi saida safe zai kai masa.Gidan Faisal kuwa police hudu aka bari su bada tsaro ba shige ba fice har sai an ga Lailah tukun.
________
Jafar yana yin iya bakin kokarinsa, haka zalika ya sanar musu da dukkan abunda ya kamata suyi kuma yana kiran Aliyu ya sanar masa da abunda yake faruwa amma be gaya ma Dizhwar bah.*ZEENASEER*
YOU ARE READING
LAILAH-DIZHWAR
Romancelabarin sarauta wanda yake dauke da kishi, mugunta, sankai, butulci da kuma soyayya, yana dauke da tausayi da kuma biyayyah wa iyaye, yana dauke da dunbi fadakarwa, da kuma nasiya akan rayuwa tayau da kullum.