🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*🌼👸🏻 LAILAH-DIZHWAR 🤴🏻🌼*
*_🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷_*
*_ZAINAB NASEER SARKI_*
*_ (ZEENASEER😘)_*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸*_ViaWattpad@Zeenaseer01_*
*(9)*
*Assalamu Alaikum*
*Ina neman afuwa a gareku masoyana, abun alfaharina, kwana biyu nayi rashin lafiya ne, shiyasa bakwa ganin posting dina, ina fatan bakuyi fishi dani bah.*
_~ina muku fatan alkhairi a duk inda kuke~😍__________
Koda Laila ta dawo daga wajan aiki zowa tayi ta zauna tana kallan abunda Dizhwar ya kawo Musu, su Mama sunata murna.
_______
Yaseer kuwa tun ranar daya je wajan Laila ta sanar masa da abunda take so da kuma wanda bata so be kuma zuwa wajan ta ba dan baya san bacin ranta.
Yau yana kwance cikin dakinsa, yaji Kiran Daddyn sa, wayar ya dauka ya sanar masa yana zuwa.
Tashi yayi ya fita daga dakin ya hau sama dakin sa.
Koda yaje Mommy ya gani zaune da Daddyn sai kuma Saudat, ko ba'a fada ba yasan ko maganar menene.
Zama yayi kan carpet Bayan yayi musu sannu da gida.
Daddyn ne ya kalle shi tare da fadin,
_"Yaseer ina maganar da mukayi dakai akan yarinyar nan?"_Shiru yayi ya kasa ya magana dan bema san abunda zaici masa bah.
_"Magana fa nake maka kana jina"_
_"Dan Allah Daddy kayi hakuri kadan karamin lokaci"_
_"Bana san wani dogun bayani, zabin da muka maka shine baka so Kenan,yarinyar yar uwar kace, taya zaka ce baka santa?"_
Shiru yayi kafin yace,
_"Dad ni ban taba gaya mata bana santa bah"__"Toh in baka gaya mata bah, amma ai alamu sun nuna"_
_"Yaseer"_
Daddyn ya kuma kiran sunan sah._"Naam"_
_"Meyasa kake san maidamu kananan yara? "_
Shiru babu amsa, Daddyn yaci gaba da magana.
_"In har da gaske baka furta kalmar daka furta bah, toh ina so Kafin ka koma ayi auranku da Saudat kafi da matar ka"_
Wani iri yaji kamar an kwada masa guduma a tsakiyar kansa
Shiru yayi dan bashi da bakin magana.
_"Magana nake maka kayi shiru"_
_"Dan Allah Dad kadan dada min lokaci, ni akwai wanda nayima alkawarin aurene shiyasa"_
Kallansa suka tsaya sunayi har Saudat din.
_"Wacece? "_
Tambayar data fito saga bakin Daddyn kenan.
_"Daddy yar gidan malam Muktar kurma nake So Laila"_
Shiru Daddy yayi, Mommy ce ta fara badin,
_"Wallahi baka isa ba, wannan yaran fa bashi da hankali, taya zaka auri wannan yarinyar da bata da gata, wallahi bazamu hada zuria da kurame bah, Allah ya kiyayye"_
_"Dakata mariya"_
Daddy ya fada yana kallan Yaseer da kansa yake a kasa._"Yaseer da gaske kana san yarinyar kuma itama tana sanka?"_
ESTÁS LEYENDO
LAILAH-DIZHWAR
Romancelabarin sarauta wanda yake dauke da kishi, mugunta, sankai, butulci da kuma soyayya, yana dauke da tausayi da kuma biyayyah wa iyaye, yana dauke da dunbi fadakarwa, da kuma nasiya akan rayuwa tayau da kullum.