🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*🌼👸🏻 LAILAH-DIZHWAR 🤴🏻🌼*
*_🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷_*
*_ZAINAB NASEER SARKI_*
*_ (ZEENASEER😘)_*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
*_ViaWattpad@Zeenaseer01_*
*(37)*
__________
Washe gari da sassafe Lailah ta saka mota babba ta zo kofar gidan su, dukkan abunda suka san nasune na amfani dashi suka zo gidan nan ko ita ta siya, gaba daya ta saka aka kwashe aka kai can gidan data siya, babu abunda ya rage musu daga kayan jikinsu sai dan abunda ba'a rasa bah.
Abba da Mama bayani kawai suke bukatar ayi musu, dan tasan ko wani lokaci tunda Dizhwar ya nuna baya kaunar s xai iya zuwa gidan yayi musu wulakanci shiyasa ta tattara inata inata tabar masa gidan sah.
Acan ta yi ma su Mama bayani, dan sukam dukkan abunda Lailah take bukata shi zatayi masa.
Duk sunyi wanka ita kawai suke jira ta fito, dan itama sauri take zataje ayi mata kunshi ga Salon tana san zuwa.
Suna falo a zaune suna jiranta ta fito sanye da Jar atamafa tayi mata kyau da Hijabi.
Nuni tayi musu dasu tashi su tafi, ba musu suka biyo bayanta, koda suka fito mukulli tasa ta fara kullewa.
Karan tsayiwar mota yasa ta juyawa tana kallan bakin gate din dan tasan tabbas a kofar gidan ta tsaya.
Ga mamakinta taga maza manya har guda uku kuwanne da makami a hannunsu sun shigo.
Da sauri ta saki kofar ta shiga gaban su Mama,
_"Ku lafiya zaku shigo mana cikin gida babu sallama ko an gaya muku Nan kangone"_
Tana rufe bakinta Dizhwar ya shigo cikin gidan sanye da kananan kaya da bakin glass a idansa.
Har gabanta ya karaso tare da cire glass din.
Kallanta yake ido cikin ido yayin da itama din shi take kallo, ta shiga gaban iyayanta dan bata san kowa ya taba su.
Babu alamun murmushi ko alamun tausayawa a fuskar sa, haka itama.
_"Wato ke dole kin dage dani zakiyi jayayya kin dage saikin aureni ko? "_
Ya fada yana kallantah.Itama shi take kallan batare da tayi masa magana bah, dan tasan any mistakes game over, dan zai iya sakawa a masu duka.
_"Toh tunda abun naki haka ne, ku fitar min daga gidana, in kuma ba haka ba, yan zunnan in saka a muku tsinannan duka"_
Murmushi tayi tare da fadin,
_"Kaji Kunyi kamarka ka rasa da abunda zakayi gori sai gida, ga gidana ka Jika kasha, kuma baka ci bulus ba wallahi in gaya maka"_Tana fadin haka taja hannun Abbanta da Mama suka huce suka fita daga cikin gidan, farin cikine ya kamata gefe daya kuma bakin ciki, domin Allah ya taimaka kamar tasan hakan zata faru tayi dabarar debe kayanta, bakin cikin Kuwa dasu Abba suka ga Dizhwar din yazo Yana neman wulakantata.
Taxi ta tara ta shiga, nan danan ta sanar masa inda zai kaisu, kofar gidan su yayi parking suka fita suka shiga yayin da ita ta mika masa kudinsa.
Gidan babu laifi yayi sosai dan karami daidai su, komai Kuma akan tsari yake ta gyara komai yanda ya kamata.
Nan ta shiga nuna musu tana fada musu ai gidan tane na kanta ta siya.
Murna suka kama suna kallan gidan amma Abba so yake ya mata tambaya kan Dizhwar.
YOU ARE READING
LAILAH-DIZHWAR
Romancelabarin sarauta wanda yake dauke da kishi, mugunta, sankai, butulci da kuma soyayya, yana dauke da tausayi da kuma biyayyah wa iyaye, yana dauke da dunbi fadakarwa, da kuma nasiya akan rayuwa tayau da kullum.