🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*🌼👸🏻 LAILAH-DIZHWAR 🤴🏻🌼*
*_🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷_*
*_ZAINAB NASEER SARKI_*
*_ (ZEENASEER😘)_*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄
*_ViaWattpad@Zeenaseer01_*
*(30)*
__________
Cike da mamakin Lailah Dizhwar yaban asibitin nan, tare da kunar zuciya akan abunda tayi masa.
________
Bayan fitar Dizhwar Lailah zama tayi bakin gadan tana ajjiyar zuciya, dan tabbas cikin tsoro da Tarad dadin abunda zai biyo baya, tayi karfin halin yima Dizhwar din hakan, dan tasan any mistakes game over, shiyasa zata tattara inata inata tayi nisa dashi inda daga shi har Jafar din babu wanda zai kara jinsu.Ranar de kusan kwana tayi batayi bacci bah, ga kuma soyayyar Dizhwar din a gefe daya dan tasan ita kam, bazata taba daina sanshi ba saide in numfashi ta dena a doran kasa shine wannan tasan zata dena.
_________
Koda safiya tayi, bata da burin daya huce Dr. Ya shigo ya sallame su.Hakan yasa tayi tsuru tsuru tana jiransa, amma har kusan 10am amma bezo bah hakan yasa ta fara kosawa.
_______
Shima Dizhwar tunda yaga Lailah jiya hankalinsa ya kasa kwanciya domin duk da yana tsanar ta, amma gefe daya ta tsaya masa cikin ransa, ko kadan ya kasa bacci abun yana damunsa, hakan yasa ya kuma tsanar kansa, tabbas yasan inba daina ganinta yayi ba bazai taba samun kwanciyar hankali bah.Gari kuwa yana wayewa ya dauki number dan kiran Dr.
Koda suka gaisa, ya shiga tambayar Dizhwar ko lafiya yaga kiransa da wannan time din.
_"Ko kana Asibitinne, ina san ganinka ne"_
Dizhwar din ya fada._"Wallahi bana nan, ina airport, akwai matsala ne? "_
Dr. Din ya tambaya._"Maganar gaskiya aiki nake san kayi min, wanda dole saika yi hakuri da hakan, duk da nasan ba aikin ka bane"_
Shiru Dr. Yayi kafin daga bisani ya furta,
_"Ina jinka babu matsala"__"Lailah nakesan ka kashe"_
Dizhwar din ya fada masa._"Wata irin magana kake haka Dizhwar, kisan kaifa kake san nayi kenan? "_
Dr. Ya fada cike da rudewa._"Eh nasani mana shiyasa na gaya maka, in baza kaiyi bah, amsar me sauki ce, abu dayawa, sai in samu wani"_
Shiru Dr. Yayi dan yana mutukar jinjina abun.
_"Shikenan babu matsala, yaushe kake San ayi hakan kuma a nawa?"_
Dr. Ya tambaya, jikinsa a sanyaye._"Yau nake bukata, kuma bana san kowa ya gane hakan, sannan maganar biyanka in ka dowa sai muyi magana, ko nawa kake bukata"_
Murmushi Dr. Yayi tare da fadin,
_"An gama ranka ya dade, Allah ya kara girma magajin sarki"_Dizhwar kashe wayarsa yayi dan, sai yanzu hankalinsa yake shirin kwanciya.
_______
Kasan cewar Dr. Zaiyi tafiya hakan yasa, ya kira Sister Zainab tare da sanar mata inda wata allura take, akan ta dauko taje ta yima Lailah, babu musu kuwa ta yi biyayyah bisa abunda ya fada, taje ta dauki allura tare da nufar dakin da Lailah take,dama ya sanar da ita 12pm tanayi za'a sallamesu.
YOU ARE READING
LAILAH-DIZHWAR
Romancelabarin sarauta wanda yake dauke da kishi, mugunta, sankai, butulci da kuma soyayya, yana dauke da tausayi da kuma biyayyah wa iyaye, yana dauke da dunbi fadakarwa, da kuma nasiya akan rayuwa tayau da kullum.