🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸
🌷🌷🌷🌷🌷🌷
*🌼👸🏻 LAILAH-DIZHWAR 🤴🏻🌼*
*_🌷🌷🌷🌷NA🌷🌷🌷🌷_*
*_ZAINAB NASEER SARKI_*
*_ (ZEENASEER😘)_*
🌸🌸🌸🌸🌸🌸🌸*© REAL HAUSA FULANI WRITER'S FORUM🐄*
*_ViaWattpad@Zeenaseer01_*
*(31)*
__________
Kasan cewar yasan unguwar sosai yasa be dauke tsawan lokaci ba ya iso, dan bemayi tunanin gidan nan bane inda su Lailah suke zaune bah.
Waya yayi mata ya sanar mata da yana kofar gidan nasu.
Kallo kawai yake yaga ta inda zata bullo.
Hijab din ta,ta saka tare da takalmi ta fito daga gidan, ganin ta fito daga gidan da beyi tsammani bah, mamaki ya kuma kamasa, sai yanzu ya kara yarda akan cewa Dizhwar yasanta ba tun yanzu bah,
Yana hango ta nufo motar yayi saurin fitowa, murmushi ta kumayi tare da gaida shi, tare suka shiga cikin gaidan,Kai tsaye inda Dizhwar yake zama in yazo ta nufa dashi.
Zama yayi ,itama ta zauna gefansa,
Shiru babu wanda yayi magana,ganin kamar da magana a bakinsa yasata fadin,
_"Wanann gidan Dizhwar ne ya bamu shi akan ku zauna na dan lokaci,kuma nasan yanzu babu abunda zaisa muci gaba da zama acikinsa, na yanke hukuncin zan kama Mana haya kamar yanda muka saba muje mu zauna har zuwa ranar da Allah zai hore mana gidan mu na kanmu."_
Ta fada tana wasa da yatsun hannunta.
Shiru Jafar yayi Batare da yayi magana bah, sai zuwa can tukun ya furta.
_"Be kamata ku tashi ba, zaman haya bashi da dadi, wahala Kike san dorawa kanki Lailah kefa mace ce ba namiji bah"_
Murmushin takaici tayi tare da fadin,
_"Tun kafin nakai haka nake wahala, sabo da bamu da wanda zaiyi mana, ina aiki tukuru dumin na samu abunda zamuci, musha mu saka da kuma mahalli, ni nake biya mana kudin haya tun bayan na gama Secondary school dina,ina ma yanzuma dan nayi wahala ba wani sabon abu bane, zan kara samun wani aikin kamar wanda nayi a baya domin mu rufama kanmu asiri"_Sosai Jafar yake tausaya mata, baya san yaga mata suna shan wahala, musamman yara kamar Lailah, amma tana burgesa sabo da hakan zaisa baza'a rainata bah ko kuma a mata wulakanci sabo da ta tashi ta nema, ga kuma uwa uba soyayyar da take yima iyayanta, da shi kansa hakan yana furgesa, duk da kasancewar ita take musu komai ga halin da suke ciki, amma be hana ta musu biyayya bah, sabanin wasu yaran da sun fara tara abin duniya zasu dinga yima iyayansu yanda suke su, su maidasu tamkar masu aiki ko kuma wasu yan maula,wasuma su gujesu.
_"Hakane Lailah, kuma Gaskiya inajin dadin yanda kike da kokari da kuma jajir cewa wajan neman nakanki, amma mutuncinki shine aure, kamata yayi kiyi aure wallahi suma iyayyan naki zasuji dadi"_
Shiru kawai tayi dan bata san amsar da zata bashi bah.
Yanzu in tayi aure zata shiga damuwa ba karama bah._"kinyi shiru, dan Allah nide akan maganar da mukayi jiya itace de yauma nazo da ita, zan iya durkusawa a gaban kima, dan Allah ki amince da Auran Dizhwar din mana"_
Shiru tayi, dan tabbas tana da burin yin hakan yanzu tunda ta canza shawara amma, Matsalar anan itace, ina zata kai iyayanta kuma basu taba jin dadin rashin ta bah, babu me gane abunda suke nufi sai ita, basu da wanda suka shaku dashi sama da ita, itace komai nasu inta tafi ta narsu wani hali zasu kasance.
YOU ARE READING
LAILAH-DIZHWAR
Romancelabarin sarauta wanda yake dauke da kishi, mugunta, sankai, butulci da kuma soyayya, yana dauke da tausayi da kuma biyayyah wa iyaye, yana dauke da dunbi fadakarwa, da kuma nasiya akan rayuwa tayau da kullum.