*🅰MRAH NAKE SO!* ♥
(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)
Na Amrah A Msh
_(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_
0⃣2⃣
A k'agare take ta iso gida domin tafiya Islamiya, amma wani Malaminsu ya rik'e su har kusan k'arfe biyar na yamma. Yi take tana duba agogon wayarta, baki d'aya hankalinta ya koma ga ta tafi, har wasu hawaye take ji suna k'ok'arin fito mata.
Jin hak'urinta ya k'ure ya sa ta tattara ya-nata ya-nata ta mik'e tsaye, tun kafin ta fito daga row d'insu ta ji muryar malamin yana masu bankwana alamun ya gama lecture d'in ke nan.
Ajiyar zuciya ta sauke, had'e da godiya ga Allah sannan a hanzarce ta fita, ko k'awar tata ma bata tsaya jira ba.
Course mate d'insu Saifullahi ta gani bisa mashin d'inshi da alama yana jiran wani ne, amma Maryama sai da ta rok'e shi a kan ya taimaka ya tafi da ita sauri take.
Bai ko musa mata ba ya ce ta hau su tafi.
A maimakon ta kwatanta masa gidansu sai bata yi ba, islamiyyarsu kai tsaye ta sa ya kaita.
Cikin mamaki Saifullahi ya ce "Yau Friday ana Islamiyya ne Maryam?"
"Ba darasi zamu yi ba Saif, akwai abin da muke ne." Ta bashi amsa tana mai k'ok'arin sauka daga bisa mashin d'in. "Na gode k'warai Allah ya bar zumunci."
"Ameen Maryama. Allah ya bada sa'a. Sai anjima." Ya tada mashin d'in ya tafi.
A gaggauce ta isa bakin gate d'in, ta samu mai gadin zaune da radio rik'e a hannunsa.
"Sannu Baba. Mun yi da kai da an yi la'asar zan zo kuma sai gashi na kasa cika al-k'awari ko? Yi hak'uri, wallahi wani malaminmu na tsaya ya sallame mu."
Murmushi dattijon yayi ya ce "Babu komai ai. Kina lafiya ko?"
"Lafiya lau Baba. Mu tafi gidan nasu ko?" Ta tambaye shi.
D'aga mata kai ya yi tare da jawo 'yar k'aramar k'ofar da ke jikin gate ya rufe da kwad'o sannan ya soka makullin a al-jihunsa.
Mashin d'insa ya hau sannan ita ma ta hau daga baya suka kama hanyar unguwar Gidan dawa da ke cikin Birnin Katsina.
Tafiya mai nisa ce ta sada su da gidan, kasantuwar akwai 'yar tazara daga Islamiyyar.
Bayan sun isa Malam Sallau ya kashe babur d'insa sannan ya ce "To Maryama mun iso, kin ga gidan nan."
K'ok'arin sauka ta yi a hankali bisa rashin sani har k'afarta ta d'an gogu a salansar mashin d'in, ta k'one kad'an.
"Subhanallahi!" Ta furta a hankali bayan ta k'arisa saukowa.
"Bi a hankali dai Maryama." Ya fad'a bayan ya gyara tsayuwar babur d'in.
"Mu shiga ko?" Ta fad'a cikin sanyin murya.
"Anya kuwa? Ki shiga dai, ki sanar da su idan sun bani izinin shiga sai in shigo."
Kallonshi ta yi kamar kar ta yi magana kuma dai ta daure ta ce "To Baba ai kuma basu san ni ba."
Da murmushi ya ce "Babu komai ai. Ki shaida masu cewa tare kike da Mallam Sallau, ba damuwa."
D'aga kai ta yi tare da shiga cikin gidan da sallama k'unshe a bakinta.
Gida ne ginin har k'asa irin na da, wanda kallo d'aya zaka masa ka tabbatar cewa gidan mabuk'ata ne.
Shiru ba'a amsa ba hakan ya bata damar sake yin wata sallamar nan ma dai shiru.
YOU ARE READING
AMRAH NAKE SO! (Completed✅)
Romance"Sickler gare ta, kuma ku kuka ja mata." Ta yi shiru daga nan, dafe da goshinta, tana jin yadda kanta ke sara mata. "A kullum dad'a wayar wa mutane kawuna ake game da awon genotype, amma wasu sun kasa ganewa, sun kasa sanin darajarsa."