*🅰MRAH NAKE SO!* ♥
(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)
Na Amrah A Msh
_(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_
2⃣1⃣
_*AMRAH NAKE SO* the book, everywhere you go. I don't even know what to say but Thank You very much. Am very very sorry for the last chapter, cuz, every soul shall taste death kaman yanda Allah mad'aukakin sarki Ya fad'a. We're all waiting for it, now, tomorrow, next tomorrow or even next year. Allah kad'ai Ya bar ma kansa sani. Fatanmu dai, Allah Ya sa mu cika da imani._
***
Shiru kake ji a kaf ilahirin gidan, in banda shesshek'ar kukan Annur babu abin da ke fita. Kwana biyar ke nan da rasuwar Amrah, amma kamar yau aka yi ta, kullum d'anya shar take dawo mana.Nannauyar ajiyar zuciya Hajiya Suhaila ta sauke, cikin muryar da ke nunar da tausayi ta ce,
"Ka fad'i abin da kake son fad'i, Annur. Ka ga baka da lafiya, mu samu mu koma ka kwanta, Islam ta duba lafiyar zuciyarka. Dan wannan halin da kake ciki, babu wuya zuciyarka ta samu matsala. Though bama fatan haka."
"Gaskiya fa." Na furta had'e da share k'wallar da ta sake fito min. "Amrah ta riga da ta tafi, duk wata damuwa ko kuka namu, ba zasu tab'a dawo da ita ba. Ta tafiya inda ni, da ku duka sai mun je, komin daren dad'ewa.
Addu'armu kawai take da buk'ata, ita ce kawai zata nunar da zallar soyayyar da muke mata. Ta nan kawai zamu saka mata da kyawawan halayen da ta kasance tana da su sanda tana raye."
Kyarma yake sosai, zuciyarsa na tafarfasa da kalamaina. Na yi da nufin ya yi shiru, amma sai k'arfafa kukan nasa ma da ya yi.
Da k'yar cikin wata murya ya ce,
"Ya zan yi rayuwa ba tare da Amrah ba? Ya zan ci gaba da numfashi a doron k'asa ba tare da baiwar Allah'r da aka gina rayuwarmu domin mu so junanmu ba? Ta yaya? Ta ya zan iya Umma? Momy ku fad'a min, ya zan yi da rayuwata? Wallahi *Amrah nake so,* ita kad'ai. Amrah nake k'auna, bata da kishiya..."
Ya sake dafe zuciyarsa, yana wani irin kuka, wanda ban tab'a jin irinsa ba. Ba wani sauti ne da shi ba, sai dai ya bayyanar da yanda yake fitowa kai tsaye daga zuciyarsa.
"...Baki d'aya rayuwata na sadaukar da ita ne gare ta. Hankalina, tunanina duka tare suke da nata. Jini da jijiyoyin jikina duka tare suke gudanya da na Amrah."
Yana kaiwa nan ya runtse idanuwansa, yana mai k'ok'arin danne sabbin hawayen da ke fitowa,
"Mutuwa dan Allah ki zo ki d'auke ni, ki zo ki tafi da Annur, ki kaishi inda Amrah take..."
Saurin dakatar da shi na yi, cikin kuka na ce,
"Kar ka yi sab'o, Annur. Dukkanmu nan ko ba dad'e ko ba jima zamu tafi, zamu je inda Amrah ta je. Dukkan mai rai mamaci ne, haka Allah mad'aukakin sarki ya fad'a a cikin littafinsa. Baki d'ayanmu jiran lokacinmu muke yi. Ita d'in kanta Amrah ba wai gaggawar tafiya ta yi ba, a'a, iyakacin lokacin da ta d'ibo wa kanta ke nan. Dan haka mu sakawa zuciyoyinmu salama, mu mik'a lamurranmu ga Allah, mu ma Amrah addu'a. Ka ci gaba da addu'a ma kanka kai ma, insha Allahu, Allah zai had'a ka da kamar Amrah, wacce zata soka, kaima kuma zaka so ta kamar Amrah..."
"Ba dai a duniyar nan ba, Ummah. Bana jin akwai mai irin halaye da d'abi'u irin na Amrah. Ko da ma akwai, bata dame ni ba. Ba ma sai idan zan iya ci gaba da rayuwar ba, bare har na had'u da wacce kike fad'i? Mutanen da komai nasu yake a had'e, Umma, kina tunanin lokaci guda zasu iya rabuwa? Bana tunanin haka."
YOU ARE READING
AMRAH NAKE SO! (Completed✅)
Romance"Sickler gare ta, kuma ku kuka ja mata." Ta yi shiru daga nan, dafe da goshinta, tana jin yadda kanta ke sara mata. "A kullum dad'a wayar wa mutane kawuna ake game da awon genotype, amma wasu sun kasa ganewa, sun kasa sanin darajarsa."