04 Tausayi

3K 225 0
                                    

*🅰MRAH NAKE SO!* ♥

(Labari mai taba zuciya, soyayya, sadaukarwa da kuma ban tausayi.)

            Na Amrah A Msh
            _(Princess Amrah)_
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*

_Sadaukarwa ga masu cutar amosanin jini (sickler)_

                          0⃣4⃣

Sai dare sannan mahaifinta ya dawo, a gajiye lis yake, wanda kallo d'aya zaka masa ka tabbatar da baya tattare da walwala.

Duk da cikin halin da nake, na tausayin ciwon Amrah, bai hana ni tashi na tarbe sa ba.

"Sannu da dawowa Mallam. Zauna ka huta kafin na kawo maka abinci." Na fad'a ina mai k'ara dubar yanayinsa.

"To Murja." Ya fad'a jiki a sab'ule.

Kitchen na nufa na zubo masa dafadukar shinkafa da na ajje masa, na d'ibo ruwa daga tulu na kawo masa.

Sai da ya ci ya yi nat, na tabbatar ya samu natsuwa sannan na ce,

"Allah dai Ya sa an yi nasara."

Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce,

"Babu nasara Murja. Abin dai sai hamdala kawai." Ya kalle ni ya gyad'a kai, sannan ya ci gaba da fad'in,

"Duk yinin nan guda da muka sha, wai Alhajin ya fasa zuwa. Har fa lokacin da na ga magrib ta yi na ce ni dai zan tafi, wasu suka ce in dai k'ara ha'kuri, an tabbatar cewa yana gari wai zai zo. 'Yar d'ari biyun da nake da ita, da ita na ci abinci da rana, naira ta hamsin d'aka da waje yanzu haka. Ban san ya zan yi ba Murja. Talauci babbar cuta ce, wacce samun maganinta yake da matuk'ar wahala." Ya dafe kansa.

Cike da tausayi na ce,

"Sai hak'uri Mallam. Ta ko wace hanya Allah Yana jarrabtar bayinSa. Hakan kuma ba wai yana nunar da baYa sonmu ko kuma Ya manta da mu ba ne, a'a, na tabbatar cewa mun fi wasu, tun da mu da wuya mu rasa abin da zamu ci. Wasu kuwa babu, abin da zasu saka ma cikinsu ma wata wahala ne. Fatana dai kawai Allah Ya bamu ikon cinye wannan jarabawar."

"Ameen. Wai duk jiran nan da muka yi, sai bayan isha'in nan wani d'an korensa ya zo yana fad'in mu tafi, wai Alhaji ba zai samu zuwa ba, sai kuma wani lokacin. Dama kyauta ce ya yi niyya ba rok'arsa aka yi ba, kuma wani uzuri ya sha gabansa."

"Shi ke nan ai Mallam. Ka cire damuwa daga ranka. Allah Yana tare da mu..." tun ban rufe baki ba Amrah ta fasa kuka tare da tashi zaune, saboda dama tun d'azu ta yi bacci.

Da sauri na kama ta na d'ora a bisa cinya, ina rirrigarta a hankali had'e da tofa mata addu'o'i, dan a tunanina ko firgita ta yi ne. Abin mamaki sai d'ago min hannunta ta yi, cikin maganarta da bata gwanance ba ta ce,

"Umma hannu ciwo.." ta kuma fashewa da wani kukan.

Gyad'a kai na yi cike da tausayi, na kama hannun nata a hankali ina mammatsawa ina tofa mata addu'a har na samu ta yi shiru.

Bayan kamar mintuna biyar ta ce,

"Umma ya daina ciwon." Ta sakar min murmushi.

"To ki gode wa Allah kin ji 'ya ta? Allah Ya baki lafiya da duk kan 'yan uwa musulmai." Na fad'a ni ma ina mata murmushin.

Bakinta dama ya dad'e da sabawa da furta amin, hakan ya sa ta ce,

"Ameen Umma." Ta sauka daga jikina da sauri ta nufi mahaifinta, saboda sai a lokacin ma ta kula da shi.

Saurin kawar da damuwarsa ya yi ya d'auke ta,

"Amrah 'yata sannu kin ji? Insha Allahu zaki samu lafiya ke ma kamar kowa."

AMRAH NAKE SO! (Completed✅)Where stories live. Discover now