*_®🌲REAL HAUSA FULANI WRITERS FORUM_*🐄
_{We r thé best}_
🌹
🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
*_DABAIBAYI_*
_rayuwarmu ayau_....*By*
*_UMMI ZEE AFLAM_*_Dedicated to..._
*_Raheenat heenat_*
_and_
*_Mamuh geee_**9-10*
_Alwala ita ma tayi sannan ta jero sallolin da bata yi ba,,,,,,daman halin murja ne tara salloli saboda haka taga innar ta na yi bata damu da sallah ba._
_Zo kiyi sauri ki gama sallah kije gurin malam na kubamu....gaskiya dole ayi aiki akan zainun._
_Uhmmm inna na gaya miki zainun ba sai an je gurin malam ba,saboda na fahimci yana sona sosai ba lallai ya iya rabuwa dani ba"..,,,_
_Inna tace"nifa dadi na dake shashanci da rashin sanin yakamata,,,,yanzu idan ba gurin malam aka je ba komai son da yake miki mahassada zasu iya shiga tsakanin ku,,,,dan haka umarni nake baki ba shawara ba ki hanzarta ki tashi ki tafi kinji na gaya miki."_
_Zumbura baki murja tayi alamun inna ta takura mata,sannan tace"to naji zan shirya shikenan ko?",,,,shikenan mana 'yar lelena ke din ce wani lokacin sai ana nuna miki hanya inna ta fada a yayin da take niyyan fita daga dakin._
_Tashi tayi ta shirya ta fito tace"To inna na tafi sai na dawo".....ko ke fa 'yar albarka ai kinga yanzu ne zamu samu damar tatsar zainun ba sassauci inna ce tayi wannan maganar...._
_Fita tayi daga gidan ba tare da ta tankawa inna ba.....tana tafiya kamar yadda ta saba ko ina najikinta motsi yake gashi kayan da ta saka Sun matseta sosai ko ina ta wuce sai sunyi Allah wadai da shigar tata ,ita batama san sunayi ba sai taunar chingam dinta take kas kasa irin yanda wayayun mata sukeyi...._
_Kai tsaye ta nufi gidan malam na kubamu....shiga tayi ba tare da tayi sallama ba saboda al'adar malam ce bai son idan zaka shiga gurin shi kayi masa sallama._
_Ta sami guri ta zauna kasancewar ta tarar da wasu baqin a gurin shi.....Bayan sun fita ne sai suka gaisa sannan ta zayyane masa abinda ya kawota._
_Malam shiru yayi yana sauraren ta harta idar da bayaninta,sannan yace"a gaskiya zan iya kai kwana uku ina aikin nan,amna idan akwai kayan aiki to zan iya gama wa a kwana biyu kacal"._
_Toh tace mishi sannan tace"malam kamar nawa kake ganin zaka karba kudin aikin?",,,,,malam ya gyara zama sannan yai gyaran murya yace"Eh to aikin ne gaskiya yana da wahala saboda wasu kayan aikin sai an tsallaka nijar ko Cameron,kinga kuma aikin zaici kudi da yawa yanxu dai sai ki kawo dubu dari domin a fara aikin yau,zuwa gobe kuma sai ki kawo cikason dubu dari biyu._
_Batai musu ba ta bude jakarta ta ciro bandir din dubu dari tw miqawa malam,sannan tayi sallama dashi ta tafi gida._
_Sauri tayi ta tari me keke napep tace"Rikkos zaka kaini dai-dai marhaba,amma drop zanyi saboda ban son tsaye-tsaye".,,,,,,_
_Toh hajiya kudinki dari biyar,inji me keke napep din ya fada a yayin da yake qoqarin gyarq parkin,,,,bata musa ba ta shiga suka tafi..._
_Har qofar gida ya kaita sannan ta bashi kudin shi tq fito ta shiga gida._
_Kai tsaye dakin inna ta nufa,,,,inna tace" Murja har kin dawo?"eh wlh inna na dawo sai dai nasha zama saboda na tarar da mutane a gurin malam din,murja ta fada a yayin da take yunqurin zama...._
_Inna tace "toh sannu da dawowa,wanne irin bayani kika yi wa malam din?".....Murja ta gyara zama tace"inna ni wlh cewa nayi ayi min aiki akan shi yanda ba wacce zai dinga gani sai ni kuma sai abinda nace yayi shi zaiyi"._
YOU ARE READING
DABAIBAYI(rayuwar mu a yau)
RomanceBata yi aune ba taji bakin maimuna a cikin bakinta......cikin hanzari murja ta fara qoqarin fizgewa, Allah ya bata sa'a kuwa ta ture maimuna ta tashi cikin sauri ta maida kayanta sannan ta jiyo ta kalle su gaba daya tace"Nagode da irin abinda kuka y...