*®🌲_REAL HAUSA FULANI WRITERS FORUM_*🐄
🌹
🌹🌹
🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹
🌹🌹🌹🌹🌹
*_DABAIBAYI_*
_rayuwarmu ayau_....*By*
*_UMMI ZEE AFLAM_*_Dedicated to..._
*_Raheenat heenat_*
_and_
*_Mamuh geee_*_*Page 3&4*_
_*"S*aurin me kake haka? Ai ni na riga na mallaka maka kaina😊cikin tattausar murya take magana tana yi kamar an takura mata dole tayi magana"._
_Zainun yace"Tun lokacin da na sanya idanuwana akan wannan kyakykyawar fuskar taki kika tafi da hankalina,domin kuwa tun da nake ban taba ganin halitta mai kyan sura irin taki ba,gaskiya Murjanat kin haďu babu qarya."_
_Wani far da ido tayi wanda ya qara jan hankalin sa ya kasa jurewa ya kuma janyota jikinsa "baby wlh ina son ki,ki yarda dani ina sonki!kin riga da kin mallake min zuciyata❤I love you, ya kara matseta a jikinsa" yayinda ita kuma taja wani dogon numfashi._
_Uhmm nima ina sonka zainun,,na mallaka maka zuciyata,dafatan zaka riqeta amana_?
_Karki ji komai babyna ya faďa yana lumshe ido alamun yana jin daďin hira da yake da ita....babyna ina son gobe mu hadu a S.F.C domin ban gaji da ganin ki ba,ta ragwaďa kai tayi qasa-qasa da murya karka damu ka jira ni zuwa dare zan gaya maka idan da yiwuwar haďuwar mu._
_Ok!toh ga wannan kisa kati,,,rafar en dubu-dubu ya miqa mata,,,,tasa hannu ta karba tace"Nagode"_
_Karki ji komai baby komai nawa naki ne,,,,ta rausaya da kanta tace"toh ni zan shiga gida".Toh shikenan ga wannan complement card din ki kira ni akwai nombana a jiki._
_Karba tayi ta fita daga cikin motan a zuciyarta tana faďin gaskiya yau na sami mijin aure_...
_Zainun saida ya tabbatar ta shiga gida sannan ya juya da motan shi ya fita a layin yana kisama abubuwa dadama acikin ranshi._
_Wannan Kenan!!!_
_Inna na ganin shigowarta sai ta fara washe baki😊oyoyo 'yar kirki daga ni yau kinyi mana babban kamu😵._
_Uhmm inna wlh yau irin mijin da kike mafarkin inyi gamo dashi na samu,,gayen ya haďu ba qarya wlh inna ko ke kika gan shi sai kin qyasa😘._
_Inna ta rike baki tace "Kin jini da mara kunyar yarinya?" Murja tace"inna ai ba rashin kunya bane gayen kina ganin shi kin san bai saba da wahala ba._
_Yanxu dai me kika samo mana domin yau naga kamar da nauyinki,,,,uhmm Inna ai sauran kayan na qofar gida bazan iya dakkowa gaba daya bane shi yasa nazo in gaya miki._
_Daďina dake wani lokacin shirman ki yayi yawa,,inna ta faďa a lokacin da ta miqe ta nufi qofar gida domin shigo da ragowan kayan._
_Bayan sun gama shigo da kayan ne sai Murja ta buđe jakanta ta ďakko kuďin da zainun ya bata ta miqawa inna._
_Inna ta kuma wangale b'aki kamar wacce aka yi ma kyautar kujerar makka😊Ah lallai kya ruďe! Wannan kuďi haka🤔gaskiya Murja dole asan yanda za ayi a k'ama shi a hannu domin irin waďannan ba a barinsu à haka._
_Hmmm inna wannan fa ba sai anje gurin wani malami ba domin kuwa ya riga da ya kamu da tsananin sona sosai,,,dan karki ga yanda yake zumuďi akai na._
_Eh kuma fa haka ne! Saboda ba kowa ne a ranar da kuka haďu dashi yayi maka wannan hidimar ba,,,,,gaskiya yaron nan kika mashi hannu bibbiyu ki nuna masa ke ďin ma baki da dama kamar yanda nasan ki._
_Inna kenan! Ai karki ji komai yanda kike nuna min so tun bayan mutuwar Mama Dole nima nayi abin da zai faranta miki rai, kuma bazan taba baki kunya ba,,zan yi iya qoqari na domin g'anin na fidda ki kunya....._
*Tofa Ashe dai Inna ba Mahaifiyar Murja bace ,shiyasa take dorata akan mugun hanya 🙊muje zuwa yan uwa yanzu muka Fara shiga labarin*.!!!
~*WASHE GARI*~
_Qarar wayarta ne ya tashe ta daga bacci,,,,tsaki taja sannan ta ďauki kiran tace "Hello!cikin murya me ďauke da alamun bacci,,,,daga can bangaren aka ce"Hope u wakeup with a smile on ur face? Sunana zainun nasan baki gane muryana ba saboda na lura da yanayin da kike magana k'amar wacce ta tashi daga bacci."""""_
_Eh wlh kiranka ne ya tashe ni daga bacci,,,,jiya na kira kuma sai wayana ya ďauke babu chaji,d'afatan hakan bai sa ranka ya baci ba,,,,haba-haba baby ai ke bakya laifi zainun ya faďa daga bangaren shi,,,ya qara da cewa"baby ya maganar fitar mu yau ďin?._
_Eh toh ina ga mu barshi zuwa 4:30 ko sai mu haďu,,,,domin yau wlh a gajiye nake kamar wacce aka yi mawa duka...Murjanat ta faďa tana jujjuya ido kamar wacce suke tare dashi._
_Toh duk yanda kika ce ranki ya daďe haka za a yi,,,,,,kinga bari nima naďan yi baccin koda na awa ďaya ne saboda kwana nayi jiya ina tunanin ki na kasa bacci,,,gaskiya Murjanat kin shiga raina da yawa,,,plsss ki Amince gobé muhadu yayi maganar cikin tattaushar muya mai kashe jiki._
_Uhmmm toh kaje kayi barccin idan ka tashi sai muyi waya ko? Toh kawai yace amma ba a son ranshi ya katse kiran ba....Murja ta ajiye wayar ta kuma juyawa barcci abinta......._
*Muje zuwa Zee Aflam ce*💋💃🏻
CZYTASZ
DABAIBAYI(rayuwar mu a yau)
RomansBata yi aune ba taji bakin maimuna a cikin bakinta......cikin hanzari murja ta fara qoqarin fizgewa, Allah ya bata sa'a kuwa ta ture maimuna ta tashi cikin sauri ta maida kayanta sannan ta jiyo ta kalle su gaba daya tace"Nagode da irin abinda kuka y...