MAKEEYAH

437 26 0
                                    

  Makeeyah ce zaune a kan sofa da mug din tea wande ke kan side table.

    Remote din tv ta janyo ta chanja channel.

Dan tsaki taja ganin still ba asa program din da take so bah.

    "Anty meekee"

Kanwar tace yar shekara goma sha uku take kiranta daga daki.

"Ke ki daina kwala min kira haka"

Ta mayar mata hade da kwabe fuska.

Sahiba (kanwar ta) ta fito da gudu rike da wayar meekee dake ringing.

Meekee ta karba, ganin mummy ce ke kira tasa tayi saurin dauka tareda sallama.

  "Makeeyah kizo daki na ki kawo min tea in kina haurowa"

  Yanda taji muryan mummy kamar bata da lafiya. Tayi saurin wucewa kitchen ta hado mata tea sannan ta haura upstairs.

Knocking tayi a kofar dakin sannan ta shiga.

   Mummy ce kudundune acikin blanket. Da sauri meekee ta karasa kusada ita tare da dafe goshinta.

"Sannu mummy."

Gyada kai mummy tayi ta karbi tea din ta hadiye magani dashi.

Meekee ta kara gyara mata bargon tareda manna mata kiss a goshi, ta fita taje dakinsu.

   Tasan by this time daddy ya riga ya wuce office.

   Tana shiga daki ta cire kayan jikinta ta fada toilet. Wanka tayi sannan ta fito ta shafa mai.

Xama tayi agaban mirror ta fesa make up mai kyau, ta feshe jikinta da turare sannan ta saka red colour gown mai dogon hannu.

   Packing gashinta tayi da red ribbon sannan ta dauki wayanta ta koma parlor bayan ta duba jikin mummy.

    Zama tayi akan two sitter sofa ta kunna tv tana kallon tashan zee world.

Doorbell ne taji yayi ringing ta tashi ta je dubawa saboda ba kowaa gidan, sahiba da sauran kannenta sun wuce school, daga ita se mummy.

    Tabude kofar tareda amsar sallaman da akayi.

Zuciyanta ne ya buga ganin wani kyakyawan saurayi wanda ya hada fiska kamar bai taba dariya ba.

  Matsa mishi tayi yashigo.

"Sannu da zuwa"

Ta fada cikin muryanta mai sanyi.

Gyada kai kawai yayi sannan ya wuce ya zauna.

Kitchen meekee ta wuce ta dauko tray ta sa cake da drinks a kai sannan ta kawo ta dire agaban shi.

"Ina kwana"

Nan ma gyada kai yayi kafin ya ce;

"Ina Anty Safiyya?"

Wato,mummynta kenan.

"Tana upstairs bataji dadi bane"

"Ayyah kice mata Sadik ne yazo"

Ashe ma sunansa sadik.

Ta fada aranta sannan ta mike ta nufi dakin mummy.

"Mummy kinyi baqo fah. Waishi sadik"

"Ohhh dan Aunty Aisha neh. Ayyah kice mishi ya iso"

Mummy ta fada dauke da murmushi a fuskanta.

Fita meekee tayi tayimishi jagora zuwaga dakin mummy.

Yana shiga ya je yayi hugging mummy tareda manna mata kiss a goshi.

"Ayyah favorite Anty nah i missed you a lot"

MAKEEYAHWhere stories live. Discover now