Ahaka one month ya shude ba tareda wani improvement bah. Koh gaisuwanta da yake amsawa yanzu ma ya daina. Batada abokin hira se violet, ko kuma ta dauki wayarta tayi ta kiran mutanen Nigeria, sai game sai chatting a WhatsApp. Sam baya kulata. Maganar naeemah kuma bata qara dawowa bah amma suna waya fiyeda da ma.
Yau tun ta tashi barci bata koma bah ta gama aikinta ta sa turaren wuta kamar kullum.
Tayi kwalliya cikin riga da wando wanda ya kamata sosai farare ne riga da wandon sai ta yi packing gashinta da farin ribbon.
Tana parlour tana kallon morning news ya fito da shirin office. Murmushi tayi mishi amma ya batsar yaja tsaki ya wuce dinning.
Bata damu ba ta tashi taje tayi serving dinshi. Kallonta yakeyi cikin tsana harta gama. Dashike shi ba mai wasa da cikinshi bane yasa baya fushi da abincinta.
Da sauri ya gama breakfast ya tashi zai tafi. Miqa mishi jakar shi tayi sannan ta raka shi har motan shi. Ko kallonta baiyi ba ya figi motar shi ya fice. Inda sabo ta saba da irin wannan ita kuma tayi alkawari bazata daina performing duties dinta bah amatsayin matar shi.
Haka ta wuni ranar cikin kewar sa, har dare around 10:30 ya dawo.
Da wuri ta tashi ta karbe jakar shi ta wuce ciki. Binta yayi da ido, yau tayi mishi kyau ba kadan ba. Favourite colourn shi tasa wato green. Wando neh iya cinya da riga armless tayi parking gashinta da green ribbon, hannunta dauke da zobbuna masu stones green da bracelets green.
Tsayawa yayi yana kallonta da yadda take rausaya.
Ita kuma zuciyarta ne yake bigawa, dan musamman ta kira qanwarshi ta gaya mata duk abinda yakeso.
Zuwa tayi ta dafa kirjin shi, su duka suka ji wani shock. Janyewa tayi da sauri tace;
"Abincin ka na kan table"
"Sai nayi wanka zanci"
Binshi tayi har dakin taje ta hada mishi ruwan wanka.
Tana nan tana jiranshi rikeda towel dinshi har ya fito. Miqo mishi towel din tayi sannan ta fito mishi da kananun kaya, green tee shirt da black three quarters.
Sannan ta fita. Bayanta yabi da kallo. Wai me yarinyar nan take nufi da shi neh, take ta wani dawainiya akanshi, bata san ma shi haushin ta yakeji bah.
❤💗💓💖💝💞💕💔
Yauma kamar ko wanne wata idan period dinta ya zo da ciwon ciki kamar zata mutu. Tun safe take ta birgima a daki koh leqo parlour ba tayi bah har yamma.
Da kyar ta iya dauko intercom ta kira violet ta kawo mata tea.
"Ina sadik?"
"Yana dakinshi i guess dan ban ganshi a parlour ba amma ya dawo"
Daga mata hannu tayi ta fice. Da kyar ta iya saukowa daga kan gado ta zura kafarta a cikin fluffy slippers dinta ta sauko.
Dafe da cikinta taje ta kwankwasa masa kofa.
"Waye neh?"
Ya tambaya ba tareda ya dago daga kan computer dinsa bah.
"Ni ceh"
"Ki shigo"
Tana shiga ta wuce ta zauna a gefensa akan gado, hawayen azaba na sauka daga kan kuncinta. Kauda kansa yayi ba tareda ya damu da abinda yasa ta kuka ba.
"Dan Allah yaya sadik ka nemo min magani zan mutu!"
Ta fada tana kuka tana yarfe hannu.
Tsaki yaja ya tashi ya koma kan gado ya kwanta tareda kashe wutan dakin, yana jin sheshekanta amma yayi banza da ita. Ni da nake gefe har na zubda kwalla ji nayi kamar naje na taimaka mata amma gudun kar ya makeni yasa na rike kayana😉