5

98 10 0
                                    

   "Makeeyah dan Allah ki bude kofan nan!"

   Tashi tayi ta bude wa mummynta ta koma ta zauna ta ci gaba da kukan da takeyi.

"Haba makeeyah, kuka sai ka ce an aura miki makiyinki, ko wani wanda baki sanshi bah?! Kiyi hakuri, wannan auren shine mafi alkhairi insha Allah"

   "Mummy baki fah ji me ya ce min bah! Wai ni ba kalarshi bace kuma yana da wacce yakeso. Taya xan iya zama dashi bayan yana son wata?"

   Dafata mum tayi tana bata baki harta daina kuka. Abinci ta kawo mata da kanta ta bata taci.

    Bayan ta fita ne ta jawo bargo ta kwanta, tana tunani.

  Yanzu ne ta tabbata tana son shi. Ta kasa samun nutsuwa tun sanda yace mata yanada wacce yake so. Yana nufin naeemah kenan, wacce ta taba rakashi gunta sukayi ta rashin kunya.

   Hawayenda ya sauko kan cheeks dinta ta goge sannan ta jawo wayarta ta kira salmah.

"Besty yane?"

"Salmah please gobe kizo gida i want to talk to you"

"Ok"

Bata jira taji me zatace bah ta yanke wayar. Ta koma ta kwanta ahaka har barci ya kwasheta.

   ❤💗💓💖💞💕

    Agefen sadik ba wani preparation da yakeyi, abokanshi neh masu shiri. Bayanda baiyi a daga auren ba amma sam mummynshi taqi yarda.

    Saura sati daya a daura auren.

  "Sadik wai ya maganan kayan lefe neh?"

Mummy ta tambaya lokacinda suke cin abincin dare.

  Shiru yayi kafin ya ce;

"Mum ai kudi zan bayar ku ku sayo koh?"

  "Ah ah, kaje ka sami ita amaryar taka inyaso kuje kasuwa ta zaba duk abinda takeso. Ita zatafi sanin abinda ya fi dacewa da ita"

  Shiru yayi bawai dan yaso bah.

  Da yamma mum ta tursasahi yaje suyi maganan lefe da makeeyah.

   ❤💗💓💖💞💕

Da kyar mummy tasa makeeyah fitowa gun sadik.

Sallama tayi a hankali ta shiga motar.

  Kallonta yayi ya hade rai kamar bai taba dariya bah.

   Shiru sukayi su duka na yan mintoci kafin yace;

  "Meyasa jiya kika min rashin kunya?"

Ya fada yana kallonta.

  Sunkuyar da kanta tayi tace cikin muryan kuka;

"Am sorry, but kayi hurting feelings dina neh"

"Okay am sorry too. Ke qanwata ce bazanso wani ya zageki ba bare ni. Amma please ki gayawa daddynki bakyaso ki aure ni. Kinga hakan bazai bata mana relationship dinmu ba"

Da sauri ta dago ta kalleshi. Bai san yanda take sonshi bane da bazai ma fara gaya mata hakan bah.

"Ni bazan iya bah."

"Toh shi kenan. Ashe kuwa sai ki shirya zaman wahala da ni.!"

Bundle din dubu daya guda goma ya wurga mata.

"Kije kiyi lefen ki!"

Mayar masa tayi.

"Banaso!"

Ta fita ta banko mishi kofar.

Binta yayi da kallo. Lallai yarinyar nan ta raina shi.

Motarshi ya figa ya wuce gida.

MAKEEYAHWhere stories live. Discover now