3

102 15 0
                                    

Abu kamar wasa meekee ta kasa nutsuwa. Ta rasa meyasa amma she couldn't get him off her mind.

Yau kasancewa ranar asabar ne, alarm dinta ne ya tasheta tun asuban fari.

Tashi tayi ahankali ta sauka daga kan gado. Straight toilet ta shiga tayi brush tayi alwala sannan tafito tayi sallah.

Tadan dade tana jan carbi kafin ta shafe addua ta koma ta haye kan gado.

Ai ko mintuna goma batayi ba barci ya dauke ta.

Mummy ce ta shigo ganin har yanzu tana barci yasa ta tasheta

"Wai keh makeeyah bazakiyi breakfast yau bane?"

"Zanyi mummy"

Ta fada tana sauqowa daga kan gado."

Dinning ta nifa ta fara bude flasks din. Pancakes ne akayi da tea ita kuma she doesnt feel like ta ci.

Kitchen tawuce ta hada strawberry sandwich da custard ta dawo dinning tana ci.

Sallama sadik yayi sannan yasa kai ya shigo.

Babu kowa a parlon qannenta sunje weekend agidan bappansu, daga ita se mummy daddy ma yayi tafiya zuwa Italy.

"Sannu da zuwa yaya sadik"

Tafada tana cixan sandwich dinta.

"Yauwa"

Ya fada ya zauna a kusa da ita.

Turamishi flasks din pancakes din tayi mishi taci gaba da cin sandwich.

Ni bazan ci wannan ba"

Dagawa tayi ta kalle shi sannan tace;

"Toh me zakaci yaya"

"Wanda kike ci"

"Toh ai guda daya nayi."

"Toh kije ki min wani"

Ya fada yana hade fuska.

Ajiye na hannuta tayi ta tashi taje ta yi mishi wanni sandwich guda biyu.

Ajiye plate din tayi agabanshi zata zauna yace "toh haka zanci ne. Je ki hada min custard"

He was expecting taqi amma sai yaga ta wuce kitchen tahado mishi.

Murmushi yayi ya fada aranshi "tanada haquri"

Ajiye cup dintayi aganshi zata wuce parlour ya sake tsayar da ita.

"Zoki zauna muci tare"

Ba musu taje ta zauna kusa da shi.

Yanka sandwish din yayi ya bata ta karba ta fara ci.

"Wani school kikayi graduating?"

"UNIMAID"

"Course?"

Ya tambaya yana daga gira.

"Microbiology"

"That is good."

Yafada yayinda ya gama cin abinci, ya goge bakinshi da tissue.

Kwashe plates din tayi taje kitchen ta ajiye.

Zata wuce taji yana kiranta. Dawowa tayi ta zauna. Kallonta ya keyi har taji wani iri.

"Do you have a boyfriend?"

Dagowa tayi da sauri tana mishi kallon mamaki. Ina ruwanshi ko tana dashi.

"Inada shi"

Ta fada tareda dauke kanta.

MAKEEYAHWhere stories live. Discover now