11

309 6 0
                                    

      Auren sadik da Makeeyah yanzu nada shekara daya cur. Zama sukeyi mai dadi cike da so da kaunar junansu. Ko da suna samun matsala amma ita meekee kwantar da kai takeyi ta bashi hakuri, koda kuwa shike da laifi.

   Yanzu saura shekaru biyu Asiya ta gama hado first degree dinta a medicine. An samata rana itada wani kyakyawan saurayi wanda suka hadu anan, shima dan Nigeria ne. Tana gama karatu za'a musu aure.

Jamaa baku tambayeni labarin Naeema bah!!!

  ❤💗💓💖💞💝💕💔

   Sadik ne zaune a office dinshi yana aiki yaji an turo kofar an shigo. Bai dago kanshi ba ya cigaba da aiki.

  A hankali ta zauna a gabanshi, sannan tace;

"Sannu da aiki sadik"

Dagowa yayi jin muryar da bai sake tsammanin jinshi ba.

  "Naeema?"

   Murmushi tayi mishi wanda ta tabbatar yanaso.

  "Me kikeyi anan?"

Mamaki ne karara a fuskanshi.

  "Na samu aiki ne a nan, shine nace bara na kawoma ziyara na ga kai ka manta dani"

Ta fada tana mai fari da ido. Dauke kanshi yayi sannan yace;

 
  "Ohhh dole in manta ai naeema, kinsan yanzu ba da bane ba, inada Mata yanzu"

   Dariya tayi tace aranta;

"Mata koh? Sai nayi sanadin rabuwarku"

"Haka neh sadik, kanada aure yanzu. Nima Allah ya kawo min miji, amma ni kamarka kawai nakeso. Saboda har cikin raina ina sonka"

  Murmushi yayi ya jingina kanshi a kujera.

  "Allah ya baki kamar ni din. Kinga ni am busy ina da aiki sosai, please idan bazaki damu ba ki fita"

   Cikin mamaki ta tashi.

"Ni kake kora daga office dinka sadik? Ka manta yanda muke da kai da? Wallahi sadik ni kadaice nasan sirrinka, ni kadai ce macen da zata iya dakai. Sadik nice mace na farko daka sani, kuma kaine namiji na farko dana sani.

Wallahi ka cuceni idan ka barni. Kasan ina sonka. Ka lalata min rayuwa sadik. Ka maidani kamar matarka. Kai ka nuna min menene so, kace min zaka aure ni amma ba haka abin yake ba.

  Saida kabarni na baka jikina, ruhi na da zuciya ta sannan ka guje ni? Kamin alkawari cewa koda ka auri Makeeyah zaka dawo ka aure ni amma duk karya ne.

  You broke my heart sadik. Ban taba tsammanin zaka min haka bah!"

  Ta fashe da kuka harda durkushewa akasa, tasan sadik nada tausayi bayaso yaga mace na kuka.

  Ai da sauri yazo ya dago ta ya rungume a kirjinshi, tausayinta na shigarshi sosai.

Bari na gaya muku yanda suka hadu...

    Sadik ne yake zaune a wani garden, lokacin tun yana Canada yana hada first degree dinshi, yanada shekaru 23 a lokacin.

    Yana nan zaune wata yar budurwa kimanin 18 years ta zo zata wuce a gabanshi tayi tuntube ta fadi.

   Shimai tausayi ne sosai shiyasa yayi saurin zuwa gareta ya dago ta yana mata sannu.

  ita kuwa naeema tunda ta kalleshi taji duk duniya ba wanda takeso sama dashi.

    Dagota yayi yana mata sannu itako tasa kuka cikin shagwaba ta na cewa;

"Wayyo qafata zafi!"

MAKEEYAHWhere stories live. Discover now