9

146 9 0
                                    

   Da safe ta tashi da kuka kamar yanda ta saba. Yau kam yasan shi ya tabota.

  "Yi hakuri kinji. Tashi in miki wanka muyi sallah"

Tashi tayi tana tafiya da kyar ya taimaka mata tayi wanka sannan suka yi sallah. Addua ya shiga jero mata har saida tayi hawayen dadi.

"Allah ya baki aljannah, ya baki ya'ya da zasu miki biyayya su faranta miki rai. Banida abunda zan biya ki da shi makeeyah"

  Kwanciya tayi ajikinshi tana murmushi.

  Ahaka sukayita hirarsu akan sallaya har saida suka fara jin yunwa. Violet yasa ta musu breakfast suka ci suka koma barci, office dinma ya fasa zuwa wai a Dole yana amarci.

   ❤💗💓💖💞💝💕💔

   "Wake up sleepy head!"

Meekee ta fada tana shafa fuskan sadik. Yana bude ido ya sauke akanta. Tayi mishi bala'in kyau cikin atampa riga da skirt.

  Dagata yayi yana kare mata kallo. Kashe mishi ido tayi tana mishi murmushinta da yakeso sosai.

   "Keh har yaushe kika tashi harkinyi wanka?"

"Ai ni tun 4 na farka. Banson in dameka neh shiyasa ban tashe ka ba kasan kayi aiki jiya ai"

  Dariya yayi ya shige toilet ita ma ta bishi abaya. Tooth paste ta matso mishi akan brush dinshi ta mika mishi, sannan ta fara hada mishi ruwan wanka. Saida ta tabbatar ya fara wankan neh ta fito ta zo ta canja bedsheets ta sanya fari pes mai kyau.

   Gyare dakin tayi tsab ta fesa room freshener.

  Yana fita ta goge mishi jiki da towel, tanayi tana mishi hira.

   "Wai kina shiryani da wuri haka kam ce miki akayi ni akwai inda zani ne?"

  Ya tambaya yana jan kitsonta.

  "Bazakaje aiki bane"

"Baga aiki inayi agida ba?"

"Aikin me kakeyi mun agida?"

Ta fada tana hararashi.

Capkota yayi yana kissing dinta.

"Wannan ne aikin da nakeyi miki"

"Point of correction Mr.Sadik, kake yiwa kanka dai"

   Dariya yayi sannan yace;

"Ah ah fadi gaskiya dai nakeyi miki."

"Toh ni ko ma menene ka tashi ka tafi yau fah Monday ne"

"Ah ni fah ban gama cin amarci na ba"

Ya fada yana janta kan gado.

"Wani amarci ne kuma sadik, tun Thursday fah"

  Kallonta yayi har cikin ido yana murmushi.

  "Me akayi din tun Thursday"

  Rufe idonta tayi tana dariya.

  Kayanshi yasa suka fito tare. Burger tayi warming a microwave ta hado mishi tea.

  Zama tayi akan laps dinshi tana bashi abaki.

"Babe kinsan yanda nake sonki kuwa"

  Dariya tayi tayi kissing din goshinshi.

"Nasan kanaso na sosai, nima ai ina sonka"

Goge mishi bakin tayi sannan ta jawoshi suka fita wurin motarshi.

  "Ka dawo da wuri fah kaji"

  Tafada tana rungumoshi. Ai kawai saiya fara kissing dinta. Tsabar rikicewa kuka ta farayi tana qara rikeshi, a takaice jamaa aikin kenan da ba'a jeh, dogota yayi yana sauri ya kaita dakinshi sukasha soyayyarsu, ni kuma tsabar kwakwab saida na labe a bayan labule, ko da dai bana ganinsu amma naji yana zuba mata albarka. 😉😂

"Ka ga koh yaya, yanzu duk ka bi ka bata min make up dina"

Ta fada tana buga kirjinshi. Muumushi yayi ya qara rungumota.

"Mu sake second round neh?"

Tayi saurin girgiza kanta.

Dariya yayi sukaje sukayi wanka sannan ya wuce office.

  ❤❤💞💕💔💓💖

     Makeeyah na zaune akan sofa ga plate din fruits a kan cinyarta, tanasha tana kallo.

"Salamu alaiki ya habibty!"

Ai koh da gudu ta tashi ta fada jikinshi. Dagata yayi yana juyi da ita a parlourn kafin ya direta akan tiles din.

  "Sannu da dawowa. Ya aiki?"

Ta fada tana jan hannunshi.

  zama yayi a gefen gado.

  Durkusawa tayi ta fara cire mishi takalminshi. da socks.

  "Ya aiki?"

"Ta tambaya yayinda ta fara kunce mishi necktie dinshi.

  "Aiki Alhamdulillah. Amma na gaji kamar me wallahi"

"Eyyah sannu koh. Ka samu kayi wanka kaci abinci sai in maka tausa"

    Murmushi ya sakar mata ya janyota jikinshi.

  "Bakiyi kewana bane?"

"Nayi mana."

   Dagashi tayi suka fita parlour ta zuba mishi coconut juice mai sanyi yasa sannan suka fara cin abinci suna hira.

  Ruwan wanka ta hada mishi yayi wanka sannan ta fara mishi tausa har yayi barci.

  Murmushi tayi ganin yana barcinshi hankali kwance. Taje ta kashe wuta tazo ta kwanta a kirjinshi tana shafa gashin.

  Ajiyar zuciya ya sake ta kara tamke ta a qirjinshi yana shafa gashin kanta.

   "Dama bakayi barci bane?"

Ta tambaya cikin murya qasa qasa mai sanyi.

  Kissing din kanta yayi yace;

"Bayan kin wani zo kin kakkamani kin rikitani ya zanyi barci"

Ya fada yana lakutar hancinta.

  "Meekee"

Ya kira sunanta a hankali.

"Naam yaya sadik"

"Inason babies. Inason ki haifamun yara da yawa masu kyau kamarki. Ki basu tarbiyya sosai kamar yadda Fav Aunty ta baki."

"Yayanah nima ai inaso in haihu. In haifa maka yara wanda in ka dawo gida su maka oyoyo."

   Ahankali ya fara kissing dinta. Sannan ya dago yana kare ma fiskanta kallo, dukda wutan dakin a kashe amma hasken lamp yana shiga ta window.

   "Ameen Allah kawo su my meekee. Good night baby doll."

"Good night my prince charming"

     Ahankali sukayi barci, tana kwance a kan kirjinshi.

  Pls vote and comment...😘

MAKEEYAHWhere stories live. Discover now