13

139 12 12
                                    

Ba Makeeyah ce ta fito daga daki ba har saida taji ana kiran sallar magariba.

Kallonta sadik yayi duk idonta ya ciko sun kumbura. Shima tun safe inda ta barshi haka yake, ko wanka baiyi ba.

Naeema kuwa tana daki ta shirya kayanta har ta yi barci.

Ko kallon inda yake Makeeyah batayi ba ta wuce kitchen. Indomie ta dafa ta soya kwai tasa a plates guda uku.

Jerasu tayi akan dinning table ta dauko juice daga fridge.

"Sai kaje kace mata ta sauko taci abinci ai ko".

Ta fada tana mai zama akan kujera.

Banza yayi da ita ya zauna kusa da ita.

Dukkansu ba wanda yaci wani abin kirki. Komar da abicin tayi kitchen kafin taje tayi wanka tayi sallah.

"Makeeyah, please dan Allah ki saurare ni..."

Hannu ta daga mishi hawaye yana tsiyayowa daga idaninta.

"Bakada abinda za ka ce min kuma yaya sadik. Kayi shiru kawai".

A hankali ya tashi ya fita daga dakin ya koma nashi, zuciyarsho yana quna yana mai nadamar haduwarshi da naeemah,
.
Cikin gidan dukka babu wanda ya yi barcin kirki in ba naeema ba.

Da safe bayan ta hada breakfast tana jerasu akan dinning naeema ya sauko.

Kallonta Meekee tayi daga sama har qasa. Sanye takeda wani arniyar rigar barci iya gwuiwa ga duk kirjinta awaje.

"Dan Allah hada min
tea".

Ta wani yatsina fuska tana zama akan kijera.

"Ce miki a kayi ni baiwa ce ko kuma hannu ne bakidashi".

Makeeyah ta fada cikin masifa, tana riqe kugu.

"Ke bazaki tausayawa halin da nake ciki ba ne? Ko da shike ba laifinki bane dan baki taba ciki bane".

Wani zafi makeeyah taji akirjinta. Lebenta na qasa ta ciza cikin takaici ta girgiza kanta kafin ta ci gaba da jera abincin.

Sadik ne ya sauko yana gyara necktie dinshi. Suna hada ido da meekee sukayi saurin cirewa.

Zama yayi agafen Makeeyah ta zuba mishi abincin ya fara ci.

"Uhm sweetheart, dan Allah in ka fita ka siyo min ice cream kaji".

Shiru yayi bai amsa ba.

Ahaka suka gama cin abincin ya fita ya tafi aiki.

Makeeyah na zaune a parlour tana kallo a tashar zee world. Hankalinta gaba daya ya koma kan kallon da takeyi sai ji kawai tayi an canja channel din zuwa African Magic.

"Me haka naeema baki ga ina kallo bane?".

"Dan kina kallo sai ni kar inyi kome kike nifi?".

"Nan gida na ne so zanyi abinda naga dama".

Manna mata hauka naeema tayi ta zauna ta fara kallo abinta.

Cikin dacin rai Makeeyah taja tsaki ta haura upstairs.

Zama tayi akan gadon ta tana jin haushi.

A iya tunannin ta Sadik yana sonta bazai kuma kallon wata mace ba, amma ba haka abin yake ba. Har ciki yayi wa naeema.

Hawaye ne masu zafi suka sauka akan kuncinta. Wa zatayiwa kuka, wa zai share mata hawaye a yanzun. Gashi Asiya suna practicals sosai a school sai weekend zata dawo.

Pillow ta janyo ta kwanta akai tana share hawayenta.

"Haka rayuwata zai kasance kenan?".

Ta tambayi kanta tana girgiza kai.

MAKEEYAHWhere stories live. Discover now