Page 1

2.9K 117 1
                                    

⚜ *_BRILLIANT WRITERS ASSO_* 🖊

*_Jamila Musa { meelat }_*

💃🏻 *RANAR AUREN TA* 💃🏻

_Written by_
*_Jamila Musa_*

*_Gargaɗi ban yadda wani ko wata ba ya juya min littafi ta ko wace siga, yin hakanfa akwai damuwa dan haka a kiyaye idan kunne yaji tou fa lallai sai a zauna lafiya_*

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

01.

*_Dedicated to_* 👇🏻
*_Fatima Shariff { ummu affan }_*

***

Cikin bacci naji wayata tana ta kururuwa alamar tana ɓuƙatar in bata ɗauki,

            Cikin yanayin bacci tattare da sigar gajiya na miƙa hannuna na ɗauko wayata amma har yanzun idanuwa a rufe suke!

        ""ba tare dana duba mai kirana ba na ɗauki wayar kasancewa na san inda zan shafa dan ansa kiran masoyana,

Assalamu Alaikum, na faɗa cikin muryar bacci, dariya mai sauti akamin daga ɗayan ɓangaren cewa,

        Meelat baki tashi bacci ba? Umm na faɗa a taƙaice amma har yanzun idanuwana basu daina bacci ba, murmushi tayi tare da cewa to ki tashi hakan nan domin bakina yana ɗauke da magana,

           "murmushi nayi tare da fara ƙoƙarin buɗe idanuwa amma hakan ta faskara,

Asmeenat Xeeyan tace ke nake sauraro meelat, Ehem ina sauraronki,

      Murmushi Asmeenat tayi tare da girgiza kanta, sannan tace albishirinki! Cikin zaƙuwa nace goro,

        "Asmeenat Xeeyan tace kinsan shararriyar marubuciyar nan? Hannuna a sama idona ina shafawa nace wace kenan? Murmushi Asmeenat tayi har haƙoranta suka bayyana, sannan tace min wa kika sani ne?

   Murmushi mara sauti nayi tare da cewa ai shararriyar marubutan suna da yawa, amma na baki gari faɗamin a daidai lokacin da nake gyara kwanciyata,

Asmee tace fatima sharif mana, nace wace kenan? Asmeenat tace min shararriyar marubuciyar nan? Ta ƙarasa maganar cikin yanayin tambaya!

    Nace Asmee daga wace ƙungiya ta fito ne? Dariya Asmee tayi sosai sannan tace anan ma gari zan baki, murmushi nayi ba tare da nace komai ba ita kuma asmee.

      "Taci gaba da cewa ƙungiyace data tara shahararrin marubutan zamani, bugu da ƙari suna rubutu cikin tsari da natsuwa, littafansu suna da armashi akwai faɗakawar ilimantarwa gami da nishaɗantar da masu karatu, akwai darissa sosai a cikin litattafan marubutan ƙungiyar ko kin gane yanzun?

Ajiyar zuciya nayi tare da cewa ai inagnin wannan ƙungiya bai wuce *_BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION_* ba domin gaskiya sun kware sun koma zaga sosai a faɗin duniyar online,

         "Murmushi Asmeenat tayi tare da cewa to tunda dai na samu kin gane maza tashi bacci ki hau online domin gani ya kori ji, tana faɗin haka ta kashe wayarta tare da cewa a shafamin kan yarana, Abdulrahman & Ja"afar,

    Ai kamar jira nake Asmeenat Xeeyan ta kashe wayarta, da sauri na sauko daga saman gado idanuwa suna ƙoƙarin ƙara liƙewa dan bacci sukeji sosai, hannuwana biyu nasa na buɗe su da sauri na nufi toilet,

A gaggauce nayi wanka tare da wanko bakina fess sannan na fito ɗaure da towel a jikina,

           """Ina fitowa na ɗan murza mai tare da shafa powder sama sama na shafa man baki, turaruka na ɗauka masu kyau da tsada na fara ɓalɓaɗawa jikina, saida na tabbatar na fara aman ƙamshi sannan na dakata,

       Bayan na gama na matsa jikin wedrof na buɗe na ɗauko riga da skart na atamfa na ɗame a cikinsu, jikin madubi na matsa na kashe ɗauri irin na "yan matan zamani!

Bayan na kammala ne na koma a gefen gado na kashe, wayata na ɗauka tare da buɗe dater na don hawa online,

          Tunda na buɗe wayana saƙonni suke bararowa daga lambobi da groups da dama, kallo kawai nakeyi fuska ta ɗauke da murmushi, amma idanuwana sun kasa tsayawa wurina ɗaya kawai so nake in gano *_BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION_* uhum ajiyar zuciya na sauke mara sauti ganin sunan ƙungiyar a farko,

         Idanuwa na zaro ganin tarin chat in da suka tara, saƙone yafi 800 da wani abu, jikina har rawa yakeyi na fara buɗewa dan ganin wace magana ce akayi wanda tasa aka tara wannan ɗinbin magana!

         " bayan na buɗe da sallama na shiga, real mai dambu ce ta sako hoto mai wannan alamar 💃🏻 oyoyo tawa, ban bata amsa ba na fara karanta saƙon kamar haka,!


Ku kasance dani domin jin labarin ranar auren ta, wato ranar auren ummu affan, tare dani jamila musa, da kuma ɗaukanci marubunta *_BRILLIANT WRITERS ASSOCIATION_* ni meelat musa nake cewa ku kasance tare dani,

Domin nayi muku alƙawarin kawo duk abunda ya faru a RANAR AUREN TA, yanda ta rubuta labarin auren wasu muma muna gdan ummu affan har sai ango ya kwashi garaɓasa zan dakata, ku kasance tare dani,

Jamila Musa!

RANAR AUREN TAWhere stories live. Discover now