Page 6

740 39 0
                                    

⚜ *_BRILLIANT WRITERS ASSO_* 🖊

*_Jamila Musa { meelat }_*

💃🏻 *RANAR AUREN TA* 💃🏻

_Written by_
*_Jamila Musa_*

06.

*_Dedicated to_* 👇🏻
*_Fatima Shariff { ummu affan }_*

Kallo ɗaya yayi ma inda nake kwance ya kauda kansa! Haka yaci gaba da jagwalgwal laptop in sa, ni kuma ina nan ƙasa zube kamar wata kayan wanki!

                       Sai 2:09am ya gama abinda yakeyi, yana gamawa ya rufe laptop insa anan ya barta ya tashi a wurin!

                ""Inda nake kwance yaje ya ɗagani, saman kujera 3siater ya kwantar dani, shi kuma ya nufi bedroom insa, yana zuwa toilet ya shige yayi alwalla bayan ya fito ya fara sallah kamar yanda ya saba a ko wane dare!

               Ni kuma ina nan kwance ban farka ba saida aka fara kiraye kirayen sallah asubu sanyin asuba ya bigeni na farfarɗo!

""""""""""A hankali na fara buɗe idanuwa na ina mai kai hannuna a saman cikina, lafiyanshi ƙalau bai wani fashe ba!,

          Murmushi nayi tare da komawa a hankali na kwanta saman kujera, rufe idanuwa na nayi, inajin fitowar sa ya nufi masallaci, dan haka yana fita na tashi da sauri naje nayi alwallah nayi sallah, bayan na gama da gudu na dawo saman kujerar na kwanta kamar yanda ya ajiyeni a daren jiya,

              Ina kwanciya na fara hawaye dan nasan zuwa mai duguri kam a yaudai tasha kara kila dai saidai ko gobe dan nima nayi alƙawarin sai na rama abinda master yaimin,

      Ina nan kwance ina matse hawayen baƙin ciki, goge hawaye na nayi tare da tunowa yanzun pha dana ɗauko wayana na hau online nasan yanzun "yan brilliant sunci rabin tafiyarsu zuwa mai duguri lallai ummu affan zatace ban kyauta mata ba, dan nasan yanzun da zan ɗauko wayana nasan akwai tilin saƙonni kila ma har da wanda suka kirani ban ɗauka ba, lallai na cika maƙaryaciya!

          A hankali naci gaba da kukana mara sauti na ɗan wani lokaci daga baya nayi haƙuri nayi shiru dan bana so master ya gane na dawo daga duniyar suma,

                    Ban daɗe da goge hawayena ba ya shigo cikin parlon da sallama, haka ya wuce abunsa har ya kusa shiga  ɗakin baccinsa ya juyo ya kalli inda nake kwance ni kuma gaba ɗaya na ɗauke lumfashi na kamar wata matattar gaske,

         Dawowa yayi kusa dani da sauri yana zuwa ya ɗuƙo hannunsa ya sa daidai hancina wai yaji idan ina numfashi niko na ɗauke shi ɗiff,

                Ya kai minti ɗaya bai cire hannunsa ba, ni kuma na ɗaukarwa raina alƙawari idan dai bazai cire ba saidai in sheƙe daga haka, janye hannun yayi ya dawo da hannunsa daidai gabar hannuna ya taɓa wannan jijiyar,

          Dariya nayi a raina nace zaka gane nasha boom, yaji dai tana halbawa lafiya qalau, dan haka ya sakemin hannun tare da gyara min kwanciyata, ya nufi ɗakinsa, yana wucewa nayi murmushi,

           Bai wani daɗe ba ya fito da kayan training a jikinsa, a can gefe ne ya duƙa ya ɗauki makullin moter sa ya fice daga parlon, yana fita na tashi da sauri na leƙa ta window ina kallonsa har yasha kwana inda zaije ya ɗauki moter sa,

"""""Ina nan tsaye har naji ya fita daga gidan, tsalle nayi na ruga da gudu na nufi kicin da sauri na fara fere dankali ina gamawa na fara soyawa ga ruwan tea na ɗora a ketil,

            Inayi inajin daɗina, saida na gama komai sannan na nufi ɗakina, ina zuwa toilet na faɗa na wanke bakina fess da "yar rawata na fito daga toilet inajin daɗi, taf lallai saida na zauna inda zanyi kalaci na, hankalina yafi jirgin sama tashi,

RANAR AUREN TATempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang