⚜ *_BRILLIANT WRITERS ASSO_* 🖊
*_Jamila Musa { meelat }_*
💃🏻 *RANAR AUREN TA* 💃🏻
_Written by_
*_Jamila Musa_*04.
*_Dedicated to_* 👇🏻
*_Fatima Shariff { ummu affan }_*Haba matsalar chargy yasa ban rubuta muku yanda muka ƙare da master ba a other room!
Da safe bayan master ya dawo daga masallaci sallah asuba a parlour ya zauna yana karatun alkur"ani mai girma kamar yanda ya saba a kowa ce safiya!
""""Ni kuma ina gama sallah da sauri na koma saman gado na kwanta! Ina kwanciya na jawo wata na buɗe dater na!
Tab maganar dai ɗaya ce jama"a, dan tunda safe su mai dambu maganar mai duguri sukeyi, ikon Allah haka na faɗa a bayyane, sannan na fara typing kamar haka!
Fatan kowa ya tashi lafiya? Haka na rubuta na tura! Ai kamar jira sukeyi inyi magana dan babu wanda ya bani amsar gaisuwa ta, suka fara cewa meelat ai gobe Ewar haka muna can muna cin kwalta,
Wannan alamar na tura musu 😬 daga haka ban sake cewa komai ba na sauka online,
Da sauri na sauko daga saman gado nayo parlour da sauri kamar ana ingizoni gaba, kallo ɗaya yamin ya maida hankalinsa ga karatun da yakeyi,
Nesa dashi na zauna na fara soso kaina, sannan na koma wasa da "yan yatsuna, da wutsiyar idonsa ya kalleni, har yanzun dai baicemin ƙala ba!,
"""Ɗan yage bakina nayi na nuno haƙorana kamar mai tallar makilin, uhum haka kawai ya faɗa tare da rufe alkur"ani ya tsareni da kallo!
Ganin kallon yayi yawa da sauri nace ina kwana, na ƙarasa gaisuwar kamar zanyi kuka, bai ansa gaisuwar ba yaci gaba da kallona babu ƙafta idanuwa,
Ganin kallon yamin yawa yasa na sauke kaina ƙasa ina ci gaba da wasa da yatsun hannuna! Bayan wani lokaci na sake ɗagowa na kalleshi har yanzun ni yake kallo,
A hankali na sake sauke kaina ƙasa, hmmm Allah ya kyauta haka ya faɗa a daidai lokacin da yake miƙewa tsaye, da sauri na tashi nabi bayansa,
""""Jin ina binsa yasa ya dakata da tafiyar amma bai waiwayo ba! Nima tsayuwa nayi tare da juyawa da sauri na kalli hanyar fita, ɗan gajeran tsaki yayi sannan yaci gaba da tafiya, jin ya fara tafiya yasa na sake juyowa nabi bayansa sauri na,
Ba tare daya sake juyowa ba, yace wuce ki tafi sai anjima bacci zanyi, ba tare da nayi magana ba na raɓa ta gefensa na rigashi shiga bedroom in, bayan ya shigo shima ya ajiye tarkacen wayoyinsa a saman bedsite, ni kuma lokacin tuni na daɗe a saman gado,
Zama ya farayi a gefen gado sannan yace yarancan baza kije kiga sun tafi school ba! Nasan wayau zaimin ina fita zai rufe ƙofa yayi bacci, dan haka nace ai Iya zata gani basai na gani ba!
Saida yayi dogon nazari sannan ya kwanta, ba tare daya kalloni ba, ni kuma wayata na ɗauko na fara latsawa, da sauri na taɓosa tare da cewa kalli ikon Allah, kalli mai ciki tana exercise dear kalli yanda takeyi kamar cikin zai faɗo ƙasa,
Ba tare daya kalleni ba yace na gani, an ɗauki lokaci mai tsayi, sannan na sake cewa dan Allah wani mafarki nayi, wai mafarki nayi ina ta tafiya a motar ga hanya ta miƙe tsaye sosai tafiya akeyi babu ji babu gani tunda safe har rana tayi har dare bankai inda zanje ba!
STAI LEGGENDO
RANAR AUREN TA
AzioneLabarin mata da miji ne, wanda kowa yake cusa ma abokin rayuwarsa bak'in ciki, ku dai shiga cikin labarin danjin abinda wannan ma'auranta sukeyi.