Page 7 to end.

1.1K 30 0
                                    

⚜ *_BRILLIANT WRITERS ASSO_* 🖊

*_Jamila Musa { meelat }_*

💃🏻 *RANAR AUREN TA* 💃🏻

_Written by_
*_Jamila Musa_*

07.

*_Dedicated to_* 👇🏻
*_Fatima Shariff { ummu affan }_*


Har yanzun hannunsa na haggu akan bakinsa ya rufe bakin, hannun damarsa kuma yana nuna ni tare dayin dariya sosai! Daina motsa ƙafata nayi ganin abinda yake a ƙafata dan kada ya cijeni,

            A hankali na ɗaga kaina na kalli master da hannuna na nuna masa yazo, cire hannunsa yayi daga bakinsa sannan yayi murmushi lokaci guda kuma ya haɗe ransa yaci gaba da kwallonsa!

     """A hankali kamar ina raɗa da wani a kusa dani nace master ku......na.....ma......... Na ƙarasa faɗar kunamar cikin warwarewar haruffa, da sauri ya juyo yana kallona cikin tashin hankali yace kuna me? Kunama na faɗa, dariya ya ƙarayi sosai sannan yace kuma ke gaki gurguwa yake nan?

     Cikin kuka nace haba master kada ka wani saka maganar faɗarmu a yanzun mu muka sa kanmu kowa yake takurawa kowa nidai kazo ka cire min kunamar nan don Allah my master na, na ƙarasa maganar cikin rarrashi,

      Cikin farin ciki yace saita ɗalleki sau ɗaya inji yanda zakiyi kuka, wayarsa ya ciro daga cikin aljihu yace bara in miki vidio idan ta gama cije ki tunda ke a yanzun bakya gani anjima idan kika samu natsuwa sai in nuna miki,

      Tsoki nayi tare da cewa master kada ka kawo aikin gaba a yanzun don Allah zo ka ɗaukeni, taɓe baki yayi tare da ɓata fuska yace Allah ya sawaƙe ni inzo ta ɗalleni? Ai ta ganni ta tafi wurinki, da sauri na ƙara duƙawa na kalli kunamar nan ta wani ɗage bindi tana ƙoƙarin sakar min harsashen dafin ta,

          Wani irin ihu nayi tare da girgije ta daga ƙafata na tashi na ruga da gudu, master yace innalillahi wa"inna"ilaihir raji"un gurguwa ta ruga ceton rai jama"a ku kawo ɗauki,

           Cikin harɗewar ƙafafuwa nake gudu, master na bina ta baya yana ina zakije? Tuntuɓe naci da wani ɗan kututun iccen da aka cire na faɗi ƙasa feff, ihuna ya ƙaru sosai saboda naji kamar an cire min ƙafata,

          Da sauri master ya duƙa ya kamoni ta baya ya ɗagani wani irin ihu nakeyi tare da diredire kamar damisa ta biyoni na rasa hanyar tsira, sakina yayi daga riƙon da yamin yabi ƙafafuwana da kallo yanda nake diddirasu, tsoki yayi tare da saka hannunsa aljihu ya ciro wata gawasa da yakeci ya riƙo ƙeyata ya tura min cikin bakina,

      '""Ɗiff na ɗauke daga kuka ina kallonsa ina kallon ƙafafuwana, ɗaure fuska yayi sosai sannan yace miye? Har yanzun gawasar tana cikin bakina amma ganin master ya ɓata rai nayi magana da ita a bakina nace kunama ce, na ƙarasa maganar ina kuka, jawoni yayi jikinsa sannan ya cire min gawasar yace ai ta tafi,

        Duƙawa yayi ya ɗauki kallabina ya ɗaura min, sannan ya juya yayi tafiyar sa ya barni a wurin tsaye baice min komai ba, kuka na farayi dan nasan sai master ya linka abinda nayi masa kuma shi yafi iya cuta dan idan ya tashi nashi ɗaya yakeyi kuma idan yamin ɗaya sai inyi sati ina jinya!

         Nan nayi tsaye kamar mill sai ƙafata dake min wani irin zugi kamar ana dandaƙata, ganin banda mafita na haƙura nabi bayan master, a parloun shi na sameshi kwance saman kujera 2siater yana kallon wayarsa ɗayan hannunsa kuma yana riƙe da gawasarsa yana ci,

    Sallama nayi tare da tura kaina ciki gaba ɗayana, nidai banji ba koya ansa sallamar ko bai ansa ba bandaiji ba, dan haka kusa dashi naje na zauna ƙasa na ɗora kaina saman kujerar, shidai baimin magana ba!

RANAR AUREN TAWhere stories live. Discover now