⚜ *_BRILLIANT WRITERS ASSO_* 🖊
*_Jamila Musa { meelat }_*
💃🏻 *RANAR AUREN TA* 💃🏻
_Written by_
*_Jamila Musa_*03.
*_Dedicated to_* 👇🏻
*_Fatima Shariff { ummu affan }_*Abinda Maryam Muhammad Hasssan tace shine,
Aunty meelat ina cikin zaƙuwa domin ummu affan tana da mutunchi sosai, dan haka bayan mun gama chart da ku, nayi tambaya zuwa mai duguri an barni inje,
""Murmushi nayi bayan na gama karantawa, sannan nayi typing kamar haka na tura mata,
_Kai maryamu amma nayi farin ciki sosai Allah ya kaimu rai da lafiya, nima ina nan ina jiran dawowan master nima Allah yasa ya barni!_
Bayan na gama na saki saƙon ya tafi zuwa cikin wayar maryamu kamar yanda ta turo min,
Bayan na tura saƙon na ajiye wayana da sauri na tashi na fara aikin gidan,
A gaggauce nakeyin aikin gida, inayi ina saƙe saƙen abubuwa da dama, haka dai har na ƙarasa abinda zanyi,
Bayan na gama komai na dafa abinci na ajiyeshi a tebirin cin abinchie na shige toilet dan yin wanka!
Bayan na fito daga wanka ina tsaye a gaban mirrow, naji hayaniyar yara sun dawo daga school, da sauri na ɗaga kaina na kalli agogon dake maƙale a jikin bangon ɗakina, naga ƙarfe 1:45pm,
"""Ɗaga bedroom na ɗaga muryana yanda zai kai har parlour nace Abdulrahman, baiyi magana ba, dan haka na koma kiran ja"afar danshi nake jiyo maganar sa a parlour,
Ja"afar haka na faɗa, mother Abdul yana jinki yayi shiru, kai duk kuzo kuɗin dukanku, haka na faɗa cikin fushi, naci gaba da cewa shine kuna ji ina magana duk zaku basar dani ina ta yage baki ina magana!
Kafin in rufe baki suka shigo cikin bedroom da sauri su dukansu, mother swry inji Abdul, ina shan ruwa ne kikeyin magana, shi kuma ja"afar yanaji kina magana ya basar,
Ɗan gajeran tsaki nayi tare da maida dubana wurin ja"afar, da sauri ya sauƙe kansa ƙasa don yaga mother tashi a cikin fushi kuma babu alamar wasa,
"""""Dan gidanku kai baza kace min yana shan ruwa ba? Duƙawa yayi ya kama ƙafafuwana tare da cewa mother don Allah kiyi haƙuri, insha Allah bazan sake ba!
Duƙawa nayi na kamashi na miƙar dashi tsaye sannan nace to nayi, amma daga yau idan kunji nace ɗaya a cikinku yazo, idan yanayin wani abu ya faɗa cewa yanayin kaza, basai ya gama yayi magana ba!
Gaba ɗayansu suka jinjina kansu alamar gamsuwa, murmushi nayi tare da zama a gefen gado nace albishirinku? Gaba ɗaya suka cemin goro, nace yara mai dugiri zani,
Idanuwa suka zaro gaba ɗayansu, 😳 ja"afar ne ya fara kuka tare da rungumeni mother nidai bana so kije, yana maganar yana ƙara kuka sosai, murmushi nayi tare da cewa miyasa kada inje?
Bakwaso inje bikin momynku? Abdulrahman yace momy Asmeenat? Nace A, a, ita a sokoto take, yace to momy mai dambu? Nace ita a bauchi take, cikin kuka ja"afar yace mother, Momy Ummuharrny? Nace ba sweety ummu harny ba,
""Ummu Affan, Abdulrahman daya ɓata fuska shima rungumeni yayi tare da cewa mother don Allah kedai kada kije wata mai duguri, nace wai miyasa bakwasan maiduguri ne? Abdulrahman yace mother faɗa akeyi a can pha,
YOU ARE READING
RANAR AUREN TA
ActionLabarin mata da miji ne, wanda kowa yake cusa ma abokin rayuwarsa bak'in ciki, ku dai shiga cikin labarin danjin abinda wannan ma'auranta sukeyi.