PAGE 1

1.1K 22 1
                                    

⚜ *BRILLIANT WRITERS ASSO* 🖊
_-{{Pen of freedom, home of exceptional and magnificent writers}}-_

                       *KWARATA*
      _{{Kalu bale gareku matan aure}}_

*JAMILA MUSA* _{ meelat musa }_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIR*

*GABATARWA:•* _Yabo da godiya da'iman wa abbadan na Allah ne. Salati da sallama su ne na fiyayyen halitta, shugaban annabawa kuma jagoran manzanni Annabi Muhammad, da iyalansa da sahabbansa baki daya._

      *Shafin farko sadaukarwa ne ga kungiya mai albarka da marubutan cikinta, BRILLIANT WRITER'S ASSOCIATION Allah ya kara hadin kai.*

*Bazan manta da ku ba aminan albarka ina alfahari daku saina tunaku ko ina a bakin kura* 🐆

*HALIMATU SADIYYA* _{{ My Leema }}_

*HABIBA IDRIS* _{{ Hubbie }}_

*HAUWA'U USMAN* _{{ Smasher }}_

*MAIMUNA O . G*

                _Gaba daya littafin nan sadaukar ne gareku,_

*ASMA'U ZAYYAN* _{{Asmeenat }}_

                           &

*RABI'ATU AMINU MAMMAN DEE*

🅿 ------ 1

        ^^Shekaruna goma sha bakwai cas a duniya. Babana yana da mata hudu da "ya "ya hamsin da bakwai.^^

          Mahaifina ya kasance dan auri saki ne, bakin abinda kunne na yaji mahaifina ya auri mata ashirin da takwas.

     Babana ya kasance talaka ne baya da wata sana'a wadda ta wuce "yan bige bige, ya gwanance wurin iya karya sannan kuma babu abinda kware dashi sai cin bashi.........

Talaka ne amma baya saka sutura irin tasu, idan kika gansa zaki rantse da Allah yana iya kyautar naira miliyan biyar, yasan dadin kudi sosai amma a sutura baya tausawa naira.

        ^^°Baya da gidan zama haka kuma baya da fili ko taki daya, munyi zama a anguwanni da dama sosai wanda duk anguwar da muka sauka suna mana lakabi da gidan inna ratata, ko kuma suce gidan yawa...

             Baya da aiki sai shaye shaye sannan kuma duk gidajen cacar dake garin katsina babu inda ba'asan shi ba, ya saka kansa caca wanda ake kira da nigerful, caca ce wacce take cinye tattalin arziki kuma ba kananan talakawa keyinta ba sai masu kudin gaske saboda idan har za'a buga wasan cacar mahaukatan kudine ake zubawa.

        Baya bayar da abinci haka kuma babu abinda ya damesa da rashin lafiyar "ya "yansa ko matansa, idan dai caca tayi masa dadi zai siyo kwanon shinkafa daya da kuma rabin doya,

Da safe idan zai fita zai bayar da kudin kalaci ko wane daki naira talatin babu wani abinda ya damesa da yawanku.

       {}{{{}}} Wata rana can wurin wasan caccarsa aka cisa, amma baya da kudin da zai biya daga cikin abinda aka saka masa, dan haka suka cire masa sutura, tun daga inda ya buga wasan har zuwa gidanmu daga shi sai gajeran wando haka ya ratso mutane saboda tsabar shi tantirine har ya iso gida.

         Babu ruwansa da tarbiyar dan sa ko yar sa, shi yasa muka mayar da gidanmu kamar gidan karuwai, domin dai kowa abinda takeso shi takeyi dan babanmu yace sana'a itace tafi cancanta ga duk diyar daya haifa, ya daina biyan kudin haya yace mu zamu rika biya tunda kowa ya kawo karfi, dan haka duk yayuna suka tashi dan neman na kansu kowa ya kama sana'a amma banda ni,

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Aug 19, 2019 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

RANAR AUREN TAWhere stories live. Discover now