Page 2

1.1K 52 1
                                    

⚜ *_BRILLIANT WRITERS ASSO_* 🖊

*_Jamila Musa { meelat }_*

💃🏻 *RANAR AUREN TA* 💃🏻

_Written by_
*_Jamila Musa_*

02.

*_Dedicated to_* 👇🏻
*_Fatima Shariff { ummu affan }_*

           
         Ban bawa mai dambu amsa ba na fara karanta saƙo kamar haka!

                 Saƙon da naga Halimatu Sadiyya Muhammad { leema } ta turo shine jikina ya fara ƙyarma domin na ƙagara inga miye ta rubuta ta shata wannan shacecen rubutu,!

           Rubutun yamin tsawo sosai kasancewar bana da isashshen lokacin karanta chat idan yayi yawa a group,

Don haka na fara kiran zuciyata wato real mai dambu, nace tawa wai miye ne yake faru wa a  BRILLIANT? Murmushi mai dambu ta sako min ɗan kansa mai wannan alamar 😊

                   Ɗan gajeran tsaki na rubutawa mai dambu domin na ƙagara inji abinda yasa aketa hayagaga a cikin gidan,

                            """ mai dambu ganin abinda na rubuta yasa ta sakeyin murmushi sannan tayomin voice note kamar haka!

     Amincin Allah ya tabbata a gareki zuciyata, da farko dai tuba nake, murmushi na turo mata kamar haka😊 ita kuma tana ci gaba da typing dan turo min ansar tambayata,

Kafin mai dambu ta gama typing na fara gaisawa da mutane kamar yanda na saba dani da "yan BRILLIANT, maryam muhammad hassan ce tace Aunty meelat barka da safiya,

    Murmushi nayi a bayyane sannan nayi typing na tura musu kamar haka,

       _Assalamu Alaikum, ina ma kowa fatan alkairi_

Haka na rubuta sannan na saki saƙon, yana shiga saƙon mai dambu yana shigowa,

_Tawa, ba komai bane sai alkairi, domin ranar nan da aka dade ana jira yau Allah ya kawota!_

                     Wace rana kenan mai dambu? Na tambayeta a gaggauce a daidai lokacin da Surayyahm ta turo nata saƙon kamar haka!

Meelat jibi ne fa bikin ummu affan, shahararriyar marubuciyar nan, marubuciyar,

*SAI NAGA BIRNI*
*RAYUWA CE*
*MAKOMA*
           &
*RUBUTACCIYAR ƘADDARA*

Ikon Allah, haka na rubuta, tare da ci gaba da cewa ubangiji yasa alkairi, sannan na sake typing na tura kamar haka!

          """""Yanzun da waye da waye zamuyi tafiyar nan ne zuwa MAIDUGURI! Haba ai nan fa zance ya sake salo, domin gaba ɗaya brilliant sunce sai sunje,

              Nan fa muka canja tasha, domin tsara yanda zamuyi tafiya zuwa mai duguri dan muje mu nuna farin ciki a RANAR AUREN TA!

Haka dai mukaci gaba da tattaunawa akan tafiya mai duguri daga baya kuma mukayi sallama da juna domin kowa yaje ya kama aikin gaban sa na gida,

                      Bayan nayi sallama da "yan brilliant na sauka daga online, murmushi nayi tare da ajiye wayana a gefen gado,!

Tagumi nayi tare da faɗawa duniyar tunani, ajiyar zuciya na sauke tare da silalewa a hankali saman gado na kwanta, fuska ta yana kallon silin in ɗakina, idanuwa na tsaye a wuri ɗaya kamar ancemin shirya za"ai miki photo,

           """ Tunani nake sosai, hankalina yafi jirgin sama tashi, sai yanzun na gane na ɗirkaka babban kuskure, domin na zarce hukuncin tafiya mai duguri da ƙawaye na amma kuma ba tare da izijina ba,

    Aiki sabo, jinjina kaina nayi daga kwance alamar mamaki ko kuma ince muku jimami, murmushi nayi tare da tashi zaune na naɗe ƙafafuwana sosai a tsakiyar gado,

Sannan na ɗauka pillow na ɗora a saman jikina, na ɗora guyawun hannuna a saman jikin pilown na tallaɓe fuskata da tafukan hannuna!

Nayi nisa sosai a cikin tunani wani ɓangare na zuciyata kuma yana addu"a Allah yasa mai gida ya yadda da buƙata na, na zuwa mai duguri dan taya ummu affan farin ciki na RANAR AUREN TA!

Ina cikin wannan tunani wanda bansan mafita ba, naji ƙarar shigowar saƙo a cikin wayana, ɗan gajeren murmushi nayi tare da taɓe bakina sannan na juya na kalli inda wayarta take ba tare dana taɓata ba! Juyowa nayi da dubana kamar yanda nake a baya', naci gaba da tunani na kamar yanda nake daga farko!

Wani saƙon ne ya sake shigowa, jin ƙarar shigowar sakon yasa na sake kallon inda wayar take, amma saida na ɗan kalleta na wani lokaci sannan na miƙa hannuna na ɗauka, ina ɗauka na shafata, bayan ta kawo haske, maryam muhamma hassan na gani a jikin saƙon,

Murmushi nayi tare da lumshe idanuwana na wani lokaci, bayan na buɗe su ne, na buɗe saƙon na fara karantawa kamar haka!!!!,,,,,,

*_Jamila Musa_*

RANAR AUREN TANơi câu chuyện tồn tại. Hãy khám phá bây giờ