Page 5

582 34 0
                                    

⚜ *_BRILLIANT WRITERS ASSO_* 🖊

*_Jamila Musa { meelat }_*

💃🏻 *RANAR AUREN TA* 💃🏻

_Written by_
*_Jamila Musa_*

05.

*_Dedicated to_* 👇🏻
*_Fatima Shariff { ummu affan }_*

Yana zuwa a parlour ya zauna, ransa a jagule yake zuciyarsa kuma tana cike da ɓacin rai amma yayi alƙawari a daren yau sai ya koyamin hankali! A bayyane ya faɗa yace wasa an fara,

           Ni kuma ganin ya fita yasa nayi dariya tare da buɗe dater na, da sauri na shige brilliant writers association, Asmeenat Xeeyan na fara bawa labari cewa har na shirya kayana yanzun ma zan kwanta bacci ne dan in tashi da wuri kada in makara,

              """Leema tace da kyau my meelat Allah ya haɗamu lafiya, dariya na rubuta sannan nayi typing cewa lallai gobe akwai ɗaukar solfie a maiduguri,

      """Naci gaba da cewa lallai zanji daɗi gaskiya ina tare da ɗaukacin marubutan brilliant zanga kowa da kowa muyi hotuna,

          Nan fa fira ya canja tako, kowa yana faɗin yanda zai kasance cikin farin ciki idan yaga ɗan uwansa!

               Murmushi yayi da yaga ina online, agogon wayarsa ya kalla yaga har 11:49pm, a bayyane yace duk ki gama chat ɗin, yana faɗin haka ya ajiye wayarsa a gafe ya fara shan lipton insa!

Ni kuma sallama nayi da "yan brilliant dan bacci nakeji bana wasa ba! Nayi musu saida safe sukace Allah ya kaimu sai mun haɗe maiduguri, nace insha Allah! Ina faɗin haka na rufe dater na,

          Ajiye wayana nayi na nufi toilet na watso ruwa bayan na fito na saka kayan bacci na! A gajiye na haye gado sai hamma nakeyi ta bacci, ina hawa nayi kwanciyata abuna na rufe idanuwana ina jiran zuwan bacci!,

            """A bangaren master kuwa bayan ya gama shan lipton insa, wayarsa ya ɗauka ya duba last seen ina murmushi yayi tare da cije leɓonsa na ƙasa,

             Ajiye wayar yayi tare da kallon agogon dake maƙale a jikin bangon parloun sa! 12:22am, shiru yayi na wani lokaci ba tare daya yayi komai ba! Yana nan zaune zugum har 12:39am, ganin lokacin da yake jira yayi yasa ya miƙe ya nufo ɗakina,

Ni kuma a lokacin naci rabin baccina cikin jin dadi da mafarkin mai duguri, gamu nan munje gidansu ummu affan ana ta shagali ga ɗaukacin marubutan brilliant muna ta hotuna, na ware dani da Asmeenat Xeeyan munayi hoto wayata a sama yanda dai ake ɗaukar solfie, Feehdorm ce take magana sai anyi da ita, nace bamayi dake duk dai a cikin wasa,

              Ji nayi ana taɓamin jiki dan haka na ɗauka fiddausin ce, na fara gocewa, zuuu naji an jawoni daga saman gado ba tare dana buɗe idona ba nace haba miye haka nace bamayi dake ke wai dole sai anyi dake ne? Na ƙarasa maganar ina dariya!

                       """Gaba ɗayana ya saukoni daga saman gadon da sauri na buɗe idona tare da dunƙule hannuna zan kai nushi 👊🏻, ɗaure fuska yayi tare da cewa to daki, nace dakeni, turo baki nayi tare da kwace jikina daga riƙon da yamin, na fara cewa haka kawai mutum na baccinsa an wani tasheshi, a daidai lokacin da nake komawa saman gado na kwanta,

                  Ƙara jawoni yayi wannan karon toilet ya nufa dani, ina ta ƙoƙarin kwacewa amma na kasa, jikin famfo ya tsaya dani bayan ya kunna ruwa ya fara zuwa ya tara hannunsa, ni kuma sai gunguni nakeyi tare da ƙara rufe idanuwana sosai!

           Bayan ruwan ya taru ya wanke mun fuska dashi, kai kai kai kaiiiii, haka na faɗa da ƙarfi na fizge hannuna na dawo da gudu na haye saman gado, shima biyoni yayi yana zuwa ya sake jawoni cikin fushi nace baka san idan ana tashin mutum bacci ba yana samun warwarewar tunani idan dai ba shine ya tashi da kansa ba? Duk idona yana rufe nake wannan maganar,

RANAR AUREN TAWhere stories live. Discover now