Part one

23 2 0
                                    

FATIMA

A hankali take takawa sabida gajiyar da tayi, kafafunta duk sunyi tsami ga uwar yunwar daketa faman addabarta, tayi sallama a daidai soron gidan su sanan ta cusa kanta ciki, Ummanta tana zaune a tsakar gida tana ta faman tankade garin masara, dago kanta tayi ta kalle ta tana murmushi ''ah lalle mamana har kun tashi daga makarantar '' tace ''eh Umma'' ''amma yau naga kunyi saurin dawowa''ta nemi waje a gefenta akan benci ta zauna saboda yunwar dake dawainiya da ita har biyu biyu take lgani idan bata zauna ba jiri sai ya kayar da ita ''Umma kin mance yau Jumma'a ne?ai ranar Jumma'a muna saurin dawowa saboda zuwa massalaci'' Umman tace ''to sannu da dawowa gashi ban karasa abincin ba kuma nasan da safe baki karya ba kafin kika tafi, na sha gaya miki banason yawan zama da yunwa dinnan idan ba wai babu abinci bane a gidan da zamu hakura saboda yunwa nayi wa dan adam babban lahani a jikinsa'' ''Umma kiyi hakuri zan daina sauri nakeyi da safe shiyasa ban tsaya nayi karin kummalon ba gudun kada ya bata mun lokaci nayi lattin assembly amm kiyi hakuri zan daina'' ''ai aikin ki kenan da kinyi abu ba dai dai ba zaki zaki soma wa mutum dadin bakinki na fama nidai shawara na ne a gareki ki idan kinso kin dauka toh son ranki idan kinki kuma shikenan, kinsan dai bamuda kudin da zamu soma jigilar zuwa asibiti dake gaki gwanar kin maganin gargajiya''. Fatima ta wuce daki ta cire uniform dinta na makaranta ta sako riga da sket dinta na material wanda kallo daya zaka mishi kagane ya dirzu sosai a ruwa, ta fito ta karbi tankaden daga hannun Umman ta karasa ta zuba a roban na tuwo sanan ta debi tsakinta juye a tukunyar daketa faman tafsa akan murhu ta jira kadan sanan ta jira kadan sanan tayi mishi hadin gwate bayan ya nuna ta sauke shi a lokacin kannenta Anas da Ibrahim suga shigo tace ''kuyi maza kuje ku chanja kayan jikinku kuci abinci sanan kuzo ku wuce massallaci kada ku makara'' suka ce ''toh addah'' sua shige dakinsu. Jim kadan sai gasu nan sun fito ko wannesu ya sha shadda amma ya kwana biyu amma kasancewar shine kadai mai kyau a cikin kayayyakin nasu shiyasa suka zabe shi, cikin hanzari suka gama ci Ibrahim ya suri taburma sukayi sauri suka fice massalacin, ita kuma ta cinye cikin hanzari sanan ta hada kwanukan ta dauraye su. Tana alwala Umman ta fito tace '' mamana idan kin idar sai kizo kiyi mun tsifa da kitso kaina ya tusfa dayawa duk ina jin kaina a takure'' ''to Umma bari na kammala nazo''. Tazo ta zauna tana y mata tsifa, tana kan kitsa mata kan sai gasu sun dawo tareda babban yayan su Abbas, tayi musu sannu da dawowa suka amsa Abbas yace ''Faty kiyi mun rai dan Allah ki samo mun abunda zan saka a cikina yunwa nake ji kinji yar kanwata'' ta ce da Umma ''Umma naje na zubo mishi sannan na dawo na cigaba mikida kitson'' ''jeki ki bashi, akwai sauran nono cikin kwarya a dakina ki dauko ki bashi amma babu sugar, sai kin aiki Ibro ya siyo mishi'' tace to. Taje ta hado mishi komi ta kai mishi tace ''amma yaya babu sugar a ciki sai an aika Anas ko Ibrahim dayansu yaje ya siyo'' girgiza mata kai yayi ''kada ki damu akwai guntun dana rage na kokon shekarnjiya ina ganin zai isheni ma, jeki kawai'' ta gyada kai ta fice domin ta karasa wa ummanta kitso. Bayan sallan Mgrib malam Sule yayi sallama ya shigo ya tarad da Fatima da Umma a tsakar gida, dukkansu sukayi mishi sannu da dawowa ya amsa taje da sauri ta amshi ledan daya shigo dashi yace ''yar albarka yau bazaki je sayar da nonon bane?'' tace ''Abba yanzu zan tafi,jiran Ibrahim nake ya kawo mun sugar tun dazu na aikeshi amma haryanzu shiru, nidai dana sani da ma naje da kaina naje nasiyo don gashi zai ja mun makara har customina su gama tafiya gida'' malam Sule yace ''ai dama idan kika aika wadanan yaran kafun ki daura ruwan tuwo to kuwa zaka sauke hara a cinye basu dawo ba, saidai hakuri kawai''. Sallamar Ibrahim ne ya dakatar dasu ''wai kai a ina ka tsaya haka tundazu nake ta jiran kaamma shiru bayan nace maka kayi sauri don kada na makara bane wai?'' Ibrahim ya marairaice fuskan shi alamun tausayi ''Addah fati yi hakuri takalmina ne ya tsinke shine abokin abba malam  iro yace na tsaya mai gyaran takalmi ya dinke munshi kada na dinga tafiya da kafa daya kafin na karaso dan Allah kiyi hakuri kinji addah'', ta mika mishi hannu ''bani sugan don idan ma na tsaya sauraran ka zan cigaba da bata lokacina ne, ka kirawo mun Anas kuzo ku dauki kwaryar dambu da furan ni na dau na nonon don kada ku zubar mun dashi irin na ranar '' ya wuce da sauri ya kirawo Anas suka kama kowa ya dau kwarya dai-dai a kanshi ita kuma ta nada gammo da dau na nonon ta rike bokitin kananun kwaryoyin da za'a dinga sha a ciki ta kalli iyayenta ''Umma,Abba, ni na tafi sai mun dawo kusa mun albarka ko nayi saurin sayarwa'' ''suka hada baki wajen yi mata Allah ya tsare sannan Allah yay mata albarka tace amin suka dau hanya.. Kasuwar yan kasa babban kasuwa ne a garin toro lgc a cikin garin Bauchi, kasuwan ya tra dimbin jama'a kasancewar ana sayr da ababe kala kala wanda ya shafe girki kokuma kayan sawa da dai sauran su kuma sanan abunda ke kara mishi armashi shine rashin yi wa kayan su tsada shiyasa suke samun mutane dayawa sunzo siyaya a kasuwar. Tana isowa wajen zamanta ta samu gefe daya ta sauke kwaryar dake kanta sanan ta taya kannent ta sauke nasu suka mata sallama suka koma gida ita kuwa ta samu guri ta zauna tana jiran mutanenta su fara siya..

MUSAYAWhere stories live. Discover now