Part 8

9 1 0
                                    

ZAHRAH

Wacece Zahra?

Alh Mahmud Sulaiman haifafen dan garin Adamawa ne cikin garin mubi, auren soyayya sukayi da matar shi Murjanatu, yayi ambasador wato jakadancin nija ma shekaru hudu sanan ya sauko aka mayar dashi ministry of federal affairs, kasancewar a london suke da zama dama gashi yanata fama da kewar kasanshi na haihuwa shiyasa ya tattaro iyalanshi suka dawo gida, dawowanshi da wata bakwai aka bashi mukamin CBN governor saboda yarda da amincin dake tattare dashi. Ya'yansu biyar Salim shine danshi na fari yanada aure da ya'ya biyu Umul khair da (Murja)siyama, Abubakar shine na biyu shima yanada aure da ya'ya hudu kasancewar ya riga Salim aure, twins Amrah(Murja) da Afrah(Maryam) sai Abdul fatah da Ahmad, Sa'ad shine na uku yana aiki a NNPC na kaduna refinery sai Abdulhameed dake NYSC dinshi sai auta Zahra tana Nurain academy tana aji hudu. Suna zaune a garin kaduna da iyalan shi banda Abubakar daya zabi zaman garin abuja, haj Murja yar kasuwa ce bata kwakwarar sati biyu a nija saboda yanayin kasuwancin ta, wanan kadai shine matsalar Zahra na rashin samun kulawan uwa amma tana mutukar samun kulawa daga wajen mahaifi da yayunta kasancewarta auta mafi soyuwa a zukatan su....

Tanan gama cin abincin ta kwashe kwanukan tayi kasa ta nufi kitchen ta ajiye ta fito kenan sukayi kicibis da Sa'ad rankwafawa tayi kadan gami da cewa ''yaya sannu da dawowa ina wuni?'' ''lafiya auta, ya karatun'' '' wlh kalau, yauwa yaya dama kai nake jira dan Allaha an bamu assignment a physics ko zaka iya taimaka mun'' '' dauko shi idan yaso bayan nayi wanka na ci abinci sai mu duba tare don nasan ba karami bane tunda har kika tambayeni'' jinjina kai tayi shi ya wuce shashin su na maza ita kuma ta haura sama ta dauko mishi takardan ta da essential physics ta sauko ta samu waje ta zauna tana jiran shi, saida ta bari ya kammala da abunda yakeyi sanan ta dawo gefenshi tare da litattafan, saida ya gama nuna mata komi ta gamsu ya bude wajen da ake saka question akan kowanne topic ya bata ta amsa ya duba duka kuma ya gamsu da amsoshin banda gyara biyu dayayi mata akan formulas sanan ya kyaleta ya koma kan system dinshi don aiyuka na gaban shi. Bayan sallan isha tana zaune bata tashi ba tana bitar karatun al qur'aninta saboda washe gari malaminta zaizo kuma a duniya idan tana so taga bacin ran mahaifinta dana yayunta to tayi wasa da karatunta duka biyu, duk gatan da suke bata basuyi sakacin da zai saka tarbiyanta ya lalace ba, ta tsinci karan motan babansu, saida ta leka ta window din dakinta taga an bude mai kofa ya sauko, sadaqallahul azeem tayi ta cire hijabinta sanan ta sauka da dan gudu gudunta don ta tarbo shi, karban jakan hannunshi tayi ta rataya ta kwace takardun sanan shima ta rage tsayinta kadan tana mishi barka da dawowa, shafa kanta yayi cikin jin dadin halin kulawan da take gwadawa mishi a kodayaushe yace ''yauwa auta na ya makaranta? da fatan kina kan kokarinki dana sanki dashi'' murmushi tayi tace ''trust me mana daddy bayan ka sha gaya mun kwalkwalarka na dauko ai kaima kasan bana wasa da takarduna'' gyada kai yayi suka soma hawa matakala yace ''yar albarka Allah ya raya mun ke'' ta sunne kai don kunya a hankali ta furta amiin sanan ta dago kanta ''daddy muje kayi wanka sai ka sauko kaci abinci nasan kana tattare da gajiya'' ya cire hular kansa saboda sanyin ac dake wajen ya ratsa shi yace ''ashe kin gane auta don kuwa yau meeting mukayi da manejojin banki na branches daban daban, kaina duk ya dau zafi'' cikin jimami tace ''ayyah daddy sorry ko, kaje kayi wanka kayi sallah sai na tanada maka magani idan kaci abinci sai ka sha hadi dana basir dinka kaje ka huta'' yagyada kai a lokacin har sun kai bakin kofa ta bude suka shiga ''kin fadi gaskiya bari nayi niyya, sauke labulayen dakunan tayi ta kulle tagogin sanan ta kunna ac ta fice daga dakin ta nufi kitchen don samar masa mai zai saka a cikin cikinsa. Bayan yayi wanka ya sauko ya tarar da komi a shirye akan dinning table shi kawai take jira, zama yayi ta zuzzuba mishi tare da mishi bismillah ya kai chokali biyu baki ya hadiya sanan ya kalleta ''auta, mommynku bata dawo ba kenan'' ta fahimce me yake nufi kasancewar babu abunda ya tsani ci kaman abincin yar aiki da dama ma idan ita zahran ce ta girka saboda yasan banbancin abincin su uku a gidan dukda babu makusa a girkin asabe saidai bakinshi dama ya riga ya banbance tsakanin su, ta dan susa bayan wuyanta tae '' bata dawoba haryanzu amma naji yaya abdul yana cewa tace mishi jibi zata dawo wai bata gama hada kayayyakin bane tukunna'' bai sake cewa komi ba saida ya cinye abincin daya kurba coconut juice din dake gabanshi sai yayi murmushi yace ''wanan aikin autana kenan ko ba ke kikayi ba'' dariya tayi ''kai daddy! komi a gidan nan idan har ni nayi kana saurin ganewa bansan ta yaya ba'' saida ya gama kurban juice din cup din ya dire sannan yace ''haba auta, nida ya'ta bansan abunda ta iya da kuma wanda bata iya ba na yi wa kaina adalci?'' girgiza kai tayi tana murmushi ''to kingani, yau ko abinci kika girka nasan naki bare ma juice? ai shi yafi ma komi ganewa. Kinyi kokari Allah yayi miki albarka ya kuma basu maki yi miki fiye ma da haka'' ''Amiin daddy. Wlh shiyasa a kodayaushe nake son faranta muku rai saboda adu'oin ku a gareni, a kullum nayi maka abunda ya faranta maka rai sai kayi mun shi nima Allah ya barmu tare da kai daddyna'' ''amiin autana idan iyaye basuyi wa ya'yansu adu'a mai kyau ba wa zamuyi ma wa? kune duniya na duk abunda nakeyi a kullum saboda ku ne idan babu ku babu farincikina'' ta mika mishi magani ya karba bayan ya hadiye tace ''to yanzu sai kaje dakinka ka kwanta saboda ka huta, maganin ma zai ji dadin bin jikinka yayi aiki'' ''to auta naji bari naje, nyt my daughter'' ''nyt dad'' ya wuce dakinshi ta kwalawa asabe kira tana fitowa ''ki kwashe kwanukan ki kai muku ku karasa shi kunsan banson abinci na kwana bare ya lalace ki hada duk da snacks din fruit salad din kawai zaki saka mun a fridge saboda su yaya'' ''an gama hajiya'' ta wuce dakinta....

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Nov 04, 2018 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

MUSAYAWhere stories live. Discover now