ZAHRAH
PEEP! PEEP! Wata 206 golden colour keta faman doka horn a kofan wani tangamemen gida cikin sakwanni da basu kai 20 ba maigadin mai suna Idi yazo da sauri ya tura gate din motar ta turo hancinta ciki daidai tsakiyar faffadan filin dake tsakar gidan yayi parking, cikin kasaita ta sauko daga motar makale da skul bag mai tyre da drawing din barbie pink colour shafe da kyalli kyalli a kafadanta, sanye take cikin uniform maroon sket dan kasa da giwanta kadan da slit a bayan shi sai farar shirt mai guntun hannu ta sha tukking dashi sai neck tie maroon a kanta kuma barret ne shima maroon colour kitson two step manya dake kanta ya kwanta har bayan wuyanta kafafunta a cikin white stockings da brown sandals daya sha polish tamkar ba wacce ta fito makaranta ba, ta janyo flask din abincinta daga bayan motan mai hawa biyu hannun damanta kuma rike da eva, saida ta sha ruwan ta koshi tayi gyatsa gami da yin kyakyawan mika daga gani kasan akwai gajiya a tattare da ita ta kalle driver dinta dake jiran umurnin ta gudun kada ya sake aikata wani laifi wa uwargidan sa akan wanda yayi dazu tace ''Abdallah da fatan ka ji abubuwan dana fada ma dazu a mota ko ba wai yana shiga kofa daya yana fita ta dayan kofan bako'' jikin shi na rawa yace ''eh haji naji, naji komi'' ''to na dai gaya maka kada ka kuskura a fadin zamanka na direbana a gidan nan kayi latti wajen dauko ni yanda yau na sha wahala ga yunwa duk ta addabeni itama asabe zamu je mu hadu da ita ta saka mun dankalin hausa da kwai ko miya bata saka mun ba ta sa na zauna da yunwa, idan ka kuskura ka sake maimaitawa to a bakin aikinka don bazan dinga barin babana na biyan ka ba kai muma kana sakaci da aikin ka da fatan kaji me nace '' '' naji ranki shi dade in shaa Allah zan kula da wanan dokoki naki baza a sake maimaitawa ba'' ta jinjina kai ta janyo cardigan dinta daga cikin motan tace ''wanan kuma matsalarka, ka ma maimaita mana ka gani, idan ka kula ka tsira da kanka idan kuwa akasin haka to kuwa zakayi waje road kaji dai na gaya maka'', ta juya tayi cikin gida shikuma ya koma cikin motan yayi ribas zai fice bayan idi ya wangale mai kofan ya tsaida shi daidai windon ya leko yace ''ya mutumin yau kuma me ya hadaka da yar daru, autan autanni'' tsaki yayi cikin takaici '' hmm.... kaidai barni da kayan haushi, waifa naje makaranta daukanta shine hold up yayi yawa a hanya ban samu na karasa da sauri ba shine ta hauni da masifa wai ta dade a tsaye bayanfa ko minti talatin fa bai kai ba amma wai na shanyata ta a rana ga yunwa na cinta wai na kuskura na sake maimaita makamacin hakan wai a bakin aikina kokuma ta sa su alhj su hanani albashina na watanni biyu a matsayin horo na, don Allah ji fa'', idi ya girgiza kai ''kaima da laifin ka, ya ci ace ka saba da halayen auta tunda ba jiya ko shekaranjiya wanchan ka soma aiki a nan gidan ba, yar rikici ce ssai muddin aka tabota kuma kasan idan aka tabota to an tabo duka yan gidan don so da kulawan da suke bata ya wuce misali. Yanzu dai ga shawara a gareka ammafa idan zaka dauka, tunda dai ba wani aiki kakeyi ba a gidan nan banda wanan to ka dinga duba agogo idan sauran awa daya ko 45mins a tashe su sai ka dau hanya, ta haka zaka tsira da kanka da kuma aljihun ka'' yayi mishi godiya ya fice don kai motan wanki gudun taga ba'a wanke ba ta hau sirfa masa bala'i da wani masifanta a wajen..........
YOU ARE READING
MUSAYA
FantasyThis story contains two sides. The first is of Fatima who hails from a poor background,intelligent,soft hearted and loved by all except her monster Sinan. The other is that of Zahra's who comes from a very wealthy family,beautiful and energetic,fu...