FATIMA
Waye Sinan???Muhammad Sinan da' ne ga Alh Aminu mai kwai wanda aka fi sani da AK mai kwai da haj Maimunatu. Mahaifin nashi dan kasuwa ne sanan ya samu inkiyar mai kwai ne ta hanayar saida kaji da kwai don wanan nema sana'arshi kuma ta karbe shi ssai saboda manyan farms dinshi a nija sun kai guda hudu a gari gari, matar shi haj Maimunatu kuwa yar banki ce a wajen take aiki kuma saboda sanin kan aikinta shiyasa aka bata babban matsayi a wajen. Yayan su uku Muhammad Sinan shine babba yana karatunshi a ABTI sai mai bi mishi Nafisa akwai tazarar shekaru shida a tsakanin su da Kabiru wanda suke kira da khalil saboda saida suka fidda ran samun wani haihuwa sanan sai ga cikin shi ya bullo, yana pri schl haryanzu don shine sa'an Ibrahim. Alh Aminu mutumne da ya daura wa kanshi jaraban son yayan shi, a rayuwa baya taba so ya ji wani yayi korafi akan ya'yan shi wanan shine sanadiyan lalacewan Sinan, shi kuwa Sinan ya dauki jarababben tsana ya daura wa Fatima tun a lokacin da aka bata scholarship ne saboda makarantar shi tayi suna jss1 tare da Nafisa shi kuwa yana final yr dinshi a makarntar. Abunda ya sa ya tsaneta shine wai ta rasa makarantar da zata zaba a duk fadin nigeria sai makarantar shi, wai ai abin kunya ne a ganshi da ita a makaranta daya, baban shi mai kudi ita kuma mahaifinta maigadi, maigadin ma bana mutum ba ah ah na dabba, a ga ya shiga tamgamemen gida a tsadaden mota ita kuma kaskatacciya amma a ce makarantar da suke zuwa daya? haba abun ba tsari. Shine ya koya wa classmates dinta tsokanarta don ita ba kowa bace yar kowa, yar maigadi suke kiranta, wasu kuma yar talakawa sauran kuma yar arha suke kiranta sakamakon ita daya ce ke zuwa makarantar da kyauta, ta kasance yarinya natsatsiya mara son hayaniya shiyasa duk abunda zasu mata bata kula bare ta tanka idan tayi tsamari kokuma ya kai ga taba lafiyan jikinta kuwa ta kai kara wajen principal ya tsawata musu ya kuma bata hakuri kasancwar makarantar na yan masu kudi both gov da vice akwai yayan su a wajen, koda yayi grad ta zata abun nasu zai tsaya amma inaaa sai ma karuwa da yayi. Idan yana zaune a kofan gidansu karkashin umbrella dinnan har tsoron fita takeyi saboda sai yasan yanda zaiyi ya cusguna mata, haka kawai ya dau tsanar duniya ya dora mata bisa kanta, ya tumurmusa ta da kasa muddin kuwa ruwa ne a kanta to kuwa rabi a jikinta rabi a kasa dolenta ta zaba daya ko ta koma wata hanyar ko da hakura. Ta sha dawowa da fasashiyar bokiti gida Umma bata cewa komi saboda itama haka take da rashin son hayaniya hasalima wanan shine musababin zuwan Abbas cell saboda dawowa tayi jikinta duk yashi tayi dumu dumu ga bokiti a fashe ya dawo cin abincin rana ya sameta haka, komawan da baiyi aiki ba kenan ranar don nade kafan wandon shi yayi ya riko hanunta har zuwa kofan gidan yace ayi mai sallama dashi, Sinan na fitowa ya tambaye shi meye dalilinsa na yi wa kanwarshi haka kodon yaga sunyi shiru ne, Sinan ya buge da zaginsa ai kuwa ya mauje bakin nan suka soma bawa hammata iska saida Abbas ya likide shi ssai saboda dama a cike yake taf dashi saida akayi namijin gaske sanan aka babare shi daga jikin shi mahaifin shi ya dawo bai tsaya jin ba'asi ba ya daure shi sai da aka sha wahala sanan aka sako shi, Umma bakinta alaikum ta siyo mata bokitin karfe kawai saboda ko ya fadi saidai ya lankwashe babu batun fashewa lankwashewar ma idan ya ci bugu maii karfine ta haka aka tsira da siyan sabbin bokitan roba, koda aike akayi mata ta leko ta ganshi zaune bakin kofa tofa ta koma kenan saidai ta aiko kannenta suje su siyo Allah yaso ba hanyar zuwa islamiyanta bane bare nan ma ya samu daurewan baya, wanan shine sanadin gabar dake tsakanin Sinan dan mai kwai da Fatima yar gidan maigadi yanda yake kiranta.....
YOU ARE READING
MUSAYA
FantasyThis story contains two sides. The first is of Fatima who hails from a poor background,intelligent,soft hearted and loved by all except her monster Sinan. The other is that of Zahra's who comes from a very wealthy family,beautiful and energetic,fu...