Part two

23 1 0
                                    

ASALIN FATIMA

Malam Sulaiman wanda akafi sani da malam sule haifaffen bafulatanin garin bauchine tun kakkaninsa, auren saurayi da budurwa sukayi da matar shi Sa'adatu wacce yar makocin su ce, sunada ya'ya hudu mace daya maza uku. Abbas shine dansu na fari sanan Fatima sai Anas sanan auta Ibrahim. Mallam Sule maigadi ne a gidan kaji a garin itakuma Sa'a fura da nono take sayarwa da dare, da rana kuma zogale da dambu da dinkim takeyin kwadon su harda lattas idan ta kama kuma ba laifi tana samun ciniki ba laifi saboda ta kasance mai tsafta, a gida ake zuwa siya kasancewar yaran duka suna zuwa makaranta. Abbas dan taxi ne, ta wannan hanyar yake samu ya ciyar da gidan kuma ya biyawa kannensa kudin makaranta amma banda Fatima saboda gwammanati ta dauki nauyin karatunta tun daga aji daya har ta gama saboda ta kasance mai kwazo, sunje competition din inside out a lagos ita tazo ta daya wa makarantar su harma a nigeria gabaki daya, a gidansu babu mai kokarinta ba wai hakan na nufin babu mai kokari bane ah ah sunada shi amma kwakwalwarta nada mutukar ja a cikin su . Iyayenta sunada rufin asiri amma ba chan chan ba kasancewar a wasu lokutan sau biyu suke cin binci a rana saboda ayi amfani da kudin abincin a biya musu kudin makaranta saboda daga Ummansu har Abban suna mutukar kaunar karatu, Malam Sule yakan ce ''me za'ayi da da rashin ilimi idan ba rashin kai ba? domin ko manzon Allah saw yace kunemi ilimi koda kuwa nisan zai kai birnin sin ne'' shiyasa yayi tsayin daka don ganin iyalen shi sunyi karatu. A yanzu haka tana ajinta na hudu a secondry, Anas yana aji daya while Ibrahim yana primary, wanan dai shine takaitaccen tarihin Fatima mai nono.

MUSAYAWhere stories live. Discover now