ZAHRAH
Hawa matakala biyu tayi ya sadata da main door din turawa tayi kasancewar tasan ba'a cika rufe shi ba saboda a wajen falon saukan baki yake a hannun hagu, tayi dan tafiya da bai wuce taku tara ba ta hau matakala guda hudu sanan ta sakala mukullin hannunta ta bude kofan daya kasance glass door, a hankali ya sliding da kanshi bayan yayi wani dan kara tare da nuna red colour ta cusa kanta ta wuce corridor wanda shima ba nisa ne dashi ba sai gata a falo, ta cire barret da shirt dinta sai sandals sanan tayi gaban tv ta kwaso remote ta dawo ta zauna akan daya daga cikin manya manyan kujerun falon, ta kunna tana jira yayi booting ta duba agogo tayi hamdala ganin la'asar da saura, tanata faman chanje chanje har ta kamo tashan da take so na cartoon din star worlds rebels sanan ta soma kwalawa mai aikinsu kira, sau biyu tana kira amma bataji ba kwai ta janyo kan landline dake an connecting dinshi zuwa sauran shashin gidan gudun tsautsayi sabodaa gidan ya kasance mai girma da kuma fadi, tana daukawa tace ta sameta a falon daddy ta kashe. Nan da nan sai gata nan ta gabato a gabanta ta dan rankwafa tace ''hajiya karama gani nan'' ba tare da ta kalleta ba tace '' kinsan awowi na nawa a falon nan tun dawowana?'' cikin inda inda tace ''ah ah ranki ya dade'' '' mintuna 15 nayi a nan zaune amma banji fitowar ki ba, duk uban karar da kofan chan keyi idan an shigo amma duk da haka baki leko ba hasalima saida na kiraki a waya wai ban ja miki kunne akan irin haka ba?'' ta soma bata hakuri '' kiyi hakuri wlh banji shigowarki ba kasncewar in bandaki, fitowana kenan naji tarho yana ringing shine nayi saurin fitowa ki gafarceni'' ta juyo suka hada ido tayi saurin saukar da kanta saboda tasan halinta sarai tana iya cewa ta raina ta shiyasa take kalont ido cikin ido a yayin da take magana da ita. Tace ''nifa kinsan banson dogon zance saboda nasan ba yau kika soma hakan ba da nayi magana zaki soma ban hakuri. Idankin gaji da aikin ne ki fada mun nasa a nemo mun wata wace zata daraja aikinta da kyau kuma ta kula da lafiyan cikina don kina matsayinki na musulma
shiyasa naki barin mabel na zabe ki, kinzo kin wani loda mun abinci babu miya ko ta yaya kike so naci shi haka oho'' ''hajiya kiyi hakuri kuskure ne kuma zanyi kokari wajen ganin na kiyay dokokin ki'', saida tayi shiru ma dan mintuna sanan tace ''shikenan ta wuce a wajena amma a kiyaye na gaba bar ganin na saba da ke, me kika dafa yau?'' cikin jindadin saukowanta tace '' cous cous da miyan ganye sai farfesun kan rago sai tuwon sakwara da miyan danyen kubewa danayi wa su yayunki don nasan ke baki cika son tuwo ba, wanne zan zubo miki'' ''cous cous din nafi muradi ki ajiye mun a dinning na sama don zan shiga nayi wanka tukunna naga ma lokacin la'aar ya gabato'' tace ''an gama ranki shi dade autan autanni na mummynta da daddynta harda ma yayunta'' tayi murmushi kasancewar tana son kirarin batace kala ba ta haye saman bene ta wuce dakinta...
YOU ARE READING
MUSAYA
FantasyThis story contains two sides. The first is of Fatima who hails from a poor background,intelligent,soft hearted and loved by all except her monster Sinan. The other is that of Zahra's who comes from a very wealthy family,beautiful and energetic,fu...