FATIMA
Tayi kusan minti goma hawaye na bin kuncinta idan ta share wani ya gangaro kafin ta hakura tana ajiyar zuci ranta duk a bace, saboda shine kowanne dare take fargaban fitowa da kindirmonta, ko yan shaye shayen da suke lungun gidansu bata shakkar su kaman yanda take tsoron Sinan saboda sharrinsa yawa ne dashi har adu'an mutuwa takeyi mishi idan ya tafi skul saboda kawai bata son ganin shi ''Allah wadaran hali irin na wanan gayen bashi da abun cin mutumci ko zagarwa sai talaka saboda kawai iyayensa sunada bugun abuja? Allah ya sauwaka''. Tana kan zancen zucin ta sai ga wani mutum yazo ya tambayeta koda sauran nono tace ''akwai malam amma matsalar shine an dama shi da fura kanaso haka?'' ya amince ta bashi yana gama sha ta hada kwaryoyinta a kai ta wuce gida tana mai tunanin gobe ma wani kalan wulakanci zata fuskanta daga gare shi. Ta shigo gidan duk fuskanta a murtuke ta sauke kwaryan a kitchen, ta dau buta ta zaga ta fito tana alwala mamanta ta fito ''yar albarka badai har kin dawo ba'' ''na dawo umma'' kallonta tayi a natse sanan tace ''ya naji muryanki duk a shake wani abu ya faru ne?''. Ta ajiye butan don ta idar da alwalan ta dubi Umman wacce ita take kallo sai kawai ta fashe da kuka don dama kiris take gashi batada sanyi wajen kuka, umma ta kamota ''Subahanallah! Mamana keda wa haka kuma? kodai kwaryan ya fashe ne kokuma kudaden sun fadi?'' ta girgiza kai ''Umma kema kinsan a fadin garin nan banida damuwar komi sai na Sinan. Umma ya takura mun, kowanne rana da irin cin mutumcin da zai mun amma ban isa na ce komi ba kawai don iyayenshi nada arziki saboda Allah Umma an kyauta mun kuwa? yaushe zan karbi yan'cina a wajen yaron nan Umma dan Allah'', shashafa bayanta take tayi alamun lallashi ''haba mamana meyasa kodayaushe muke nanata magana daya ne? mamana na sanki da hakuri to dan Allah ki kara akan na da, yaron nan gidan su sunfi karfin mu sanan basu ganin mutumcin dan Adam talaka, kansu kadai suka sani. Babu halin mukai kararsa don ko mun kai iyayen nada gidan rana kinga zasu rufe bakin polisawan da kudi laifin ya dawo kanmu, ba ma wanan ba yaushe muka gama da dawainiyar cinmu da karatunku bare mu samu kudin kai kara? kina sane wanchan karon da yayanku yayi fada dashi rufeshi sukayi ya kusan sati biyu a kulle da kyar da sudin goshi muka samu suka sako shi bayan ya sha bakar wahala da kuma kasedin kada ya kuma shiga sabgar shi, to so kike ya sake fuskantar irin wanan kaskancin a dalilinki?'' ta girgiza kanta saboda bakinta ya kasa furta komi, zuciyarta sai faman tafarfasa yake yi tsabar bakin ciki. Umma tace ''yauwa, to yanzu so nike idan yayi miki wani abu daya bata miki rai kawai ki tuna cewa Allah na nan kuma yana kallon duk abunda ke faruwa shi mai sakayya ne ga duk bawansa da aka zalunta kinji mamana'' '' in shaa Allah Umma daga yau na daina kawo kararsa tunda na gane irin halayyan shi, zan barshi da mahaliccinmu kawai yayi mana magani'' ''ko kefa. Yanzu kiyi sallah ki samu ki ci abincin ki sai muyi bitar karatu kaman kullum koh'' ta mike ta bata waje don taje tayi sallah, bayan ta idar ta debo abinci taci sai ummanta ta dawo tayi mata bitar karatun Al qur'ani sabida washe gari tanada hadda a makaranta...
YOU ARE READING
MUSAYA
FantasyThis story contains two sides. The first is of Fatima who hails from a poor background,intelligent,soft hearted and loved by all except her monster Sinan. The other is that of Zahra's who comes from a very wealthy family,beautiful and energetic,fu...