FATIMA
Tunda ta iso mutane masu siya sukayi mata chaaaa a kai kasancewar kindirmonta mai kyau ne baya tsamami kuma ba'a samun kasa kokuma datti a cikinsa. Saura nata kaman kwano biyu ta gama saidawa kamar daga sama taji muryar shi '' keh yar talakawa mai tsamin nono a zuba mun a kwarya'' saida gabanta ya fadi kasancewar tasan halinshi sarai yana iya zuwa ya zuba mata rashin mutumci kwando kwando ian taki kula shi, ta janyo kwarya da ludayi zata deba mishi ya doka mata tsawa daya firgitar da ita dama gata gwanar tsoro ''keh! ke wata irin kazamiya ce haka da bazaki dauraye kwaryan ba kafin ki saka mun ba? so kike na kamu da ciwon ciki ko cholera? kodashike nasan idan aka biyaki kudink shikenan ko na mutu bakida damuwa , bakauyiya kawai''. Zazzafar hawayene ya biyo kuncinta saboda zafinda ranta keyi sakamakon bakaken maganganun dake fita a bakinshi , takaici duk ya cikata ta soma zanen zuci ''wai meyasa Sinan ya takura mata ne haka? wai shin da arziki da talauci ba Ubangiji bane mai daurawa bawa don gwada imanisa ba? meyasa kowanne rana idan baiyi mata wulakanci ba hankalinshi baya kwanciyabane?kodashike na bar kuka don ganinhawayena bazai sakashi ya daina ba hasalima saidai izigilancin nashi ya karu''. Tayi ajiyar zuciya gameda share hawayenta ta dube tare da tsaki ''wai shin Sinan me na tsole maka ne a duk fadin garin nan da kake takura mun wai laifin me na taba yi maka ne wai? na sha gaya maka idan wani abu nayi maka da sanina ko a bisa rashin sani ka sanar mun dashi don na baka hakuri ka daina wulakantani'' Sinan yayi tafi gameda shewa sanan yace ''iyeh! lallai yarinyar nan kinmayi baki tunda har zaki iya tambayana laifin da kika mun, to dai bari na gayamiki tunda naga kin soma samun guts din mayar mun da tambaya. Laifin ki kwaya daya tal! laifin kuwa shine kasancewarki talaka wanan kadai shine laifinki na rayuwa, da ke mai kudine ai d baza'a dinga jin kanmu ba tunda kema da kin sami makamin kare kanki'' a zuciyarta tace ''to ai ba ni daya na kasance talaka a anguwan nan ba tsabar rainin wayo ne kawai da iskanci'' za tayi magana ya dakatar da ita '' zaki zuba mun nonon na sha da girma da arzikine kokuma sai nazo nayi ball da kwaryar nonon kinyi asara?''. Da sauri ta soma bashi hakuri domin tasan zai iya aikata hakan kuma tayi asara daga it har gdan su, ta zuba mai nonon ta gama dama furan ta zuba akai ta mika mishi ya harari kwaryan yace ''ni na gaya miki da fura nake so kika wani saka mun shi?'' tace ''ai naga kodayaushe kazo shi nake saka maka yanzu kuma kace baka so?'' ''eh ki saka mun dambun da nonon bana son furan'' tayi narai narai da idanu tana neman yin kuka tace ''haba Sinan kaji tausayina mana,idan na dama maka sauran nayi yaya da wanan dana riga na dama bayan ba kowa ya cika son fura ba sai dambu saboda Allah?'' ''au tambayata ma kikeyi? karbi kwaryan nan a hannuna kokuma na kifar miki dashi na nuna miki yaya zakiyi din dashi'', tayi sauri ta amso kwaryan a hannunshi ta ajiye a gefe daya ta rufe da faifai ta kwashe mishi sauran nonon dake cikin kwaryan ta zubo mishi dambun akai ta dama ta zuba mai suga sanan ta mika mishi. Ya karba fuska a yatsine kaman bazai sha ba daga baya ya karbi ludayin daga hannunta wanda tayi saurin daurayewa domin gudun abunda ya faru dazu ya maimaita kanshi domin lallai Sinan bashi da mutumci. Sanda ya gama sha yayi mata jifa dashi a jikinta kadan ya bata mata jikinta, ido ta zuba mishi kawai don rashin sanin madafa har zatayi magana kuma sai ta fasa ''meye kin wani tsareni da bulgy eyes dinki saikace nayi sata, ko da wani abune?'' ta girgiza kanta '' babu, kudin kayana kawai zaka bani'' ya ciro kudinta ya watsa mata a jiki ya mayar da wallet dinshi aljihu ''kinci sa'a mamanki tanada kindirmo mai kyau idan ba haka ba me zai kawoni wajen ki siyan abu, dube ki fa dan Allah ko kwalliya ma kin kasa yi ga kayanki duk a kode ko kande mai aikinmu ta fiki kyawun suturori(jama'a wai shin an sa shi dole ya sha ne? gulma kawai'')uhmm kodashike ke yar maigadi ce so i wont blame ur dressing coz nasan its all ur poor parents can afford'', ganin hawaye nata faman shatata akan kuncinta sai ya kyalkyale da dariya don dama abunda yake buri kenan kuma ya samu. Yadaga mata hannu alamun bye bye ''see u tomorrow same time same place'' ya ja motar sa zuciyarsa fal murna, sai da ta bari motan shi yayi nisa sanan tace ''tsinanne Allah yasa tayarka ta fashe kayi hatsari ka zama gurgu dan ubanka ka bar zuwa wajena da mugayen kalamai'' ta fashe da kuka....
YOU ARE READING
MUSAYA
FantasyThis story contains two sides. The first is of Fatima who hails from a poor background,intelligent,soft hearted and loved by all except her monster Sinan. The other is that of Zahra's who comes from a very wealthy family,beautiful and energetic,fu...