Chapter 9

12 2 0
                                    

......
6 months later.

A cikin filin jigin sama na murtala muhammad, bangaren domestic watan masu fita da zuwa iya kewayen nigeria, mutane keta zirga zirgar su. Ta taho tana ta duba wa koh xata gansu, domin suna sauka ta kira su suka ce mata suna wajen jira suna jiranta. Sanye take cikin doguwar riga mustard yellow har qasa me dogon hannu sai ta yane kanta da coffee color veil, tana rataye da side bag dinta me kalan mustard yellow, sai loafers coffee brown, tana tafe tana jan baby pink trolley dinta.
Gani tayi ana ta waving mata hannu, nan da nan ta gane ta, anty amnah ce da uncle kareem suka zo daukan ta, hajar ta tako xuwa wajen su da murmushi dauke a fuskar ta, ba yabo ba fallasa ta dan ciko akan ramar da tayi watannin baya da suka shude. Sannu da xuwa yata fadar anty amnah, ya hanya, alhamdulillah na iske ku lafia. Lafia lao. Barka da rana uncle kareem yawwa hajar ya kika xo.
Amnah kanwa ce a wajen mahaifiyar hajar, itace auta a gidansu, ba wata babba bace can kasan cewar shekarar ta 33, tana auren Arc kareem sajid, dan asalin kasar Sudan mazaunin nigeria, suna da yara biyu suhail dan shekara 15 da suhailah yar shekara 12, suna zaune a garin lagos.
Isowar su gida ke da wuya, anty amnah ta nuna ma hajar dakinta sannan tace ta dan watsa ruwa taxo suyi dinner xasu jira ta, ta amsa mata sannan ta shiga wankan. Tana fitowa ta saka riga mara nauyi saboda yanayin zafi ake.

....
Hajar POV.
It's already been a week now since I came to Lagos, well zamana anan is so okay alhamdulillah, uncle kareem and aunt amnah are so nice and caring.
Ina zaune sai abun da ya faro wata 6 da suka wuce ya dawo min...
Bude ido nayi sai naganni kwance a kan gado ga drip an makala min, nan take naji kaina ya juya sai tsananin sara min da ya fara yi. Ba shiri na saki wata yar qara sai naji an dameni sai aka fara hamdala ana ta tashi a kira likita, duk abunda da akeyi baki na ya kasa furta kalma koh da guda daya ce, komai ya kulle min na kasa gane meke faruwa dani.
Likita yaxo ya duba ni ya fara min tambayoyi amman sai dai na bishi da idanu dan magana taki yiyuwa, ya dan yi rubuce rubucen sa ya kalli matar dake tare dani wadda ban gane ta ba har yanxu yace hajia ina so ayi monitoring rashin maganar ta ta, ina suspecting 'Selective mutism' due to shock data samu. I hope dai ba shi bane, matar tace cikin sanyi Allah ya sa. Ta kalle ni nima dai ina ta kallan su.
Minti 30 da fitar likita sai ga wasu sun shigo su ma suna ta murmushi suna hamdala sai naga wata mace ta xauna kusa dani da murnar ta ta shafa kaina, sai na maxa na kauda kaina na tashi xauna, suka ta bina da kallo cikin mamaki, ni kuma cikin dimaucewa nace dasu, "su waye ku ne, me nake yi a nan wacece ni ma yake faruwa" duk a numfashi daya. Suka rikice sai wani dan saurayi da bai wuce saana ba ya fita a guje ya je ya dawo da wannan likitan. Likitan ne ya kalle ni yace min ya nake ji nace masa ni lafiya ta kalau. Yayi murmushi yace kin gane wadannan nace ban san su ba kwata kwata. Yace zaki iya tuna wani abu wata daya da ya wuce nayi shiru nace masa aa. Sai ya juya ya kalli wani mutum babba ne yace masa Alhaji sai mun mata MRI da ina tunanin selective mutism ne amman yanzu nafi ga suspecting 'selective amnesia' ne.
And it was confirmed that selective amnesia ne, Likitan yace brain dinta ya xabi ya manta da painful memories, but in her case it seems har da mutanen da ta gani last lokacin da ta samu tashin hankalin da ya sa ta suma.
Akwai wanda baya wajen time din da abun ya faru ne, inji likitan, sai mutumin nan yace eh akwai mutane uku, toh suna kusa yanxu kafin ya rufe baki sai ga noor da hamma mutasim da hamma kabeer sun shigo, ai suna shigowa na fashe da kuka nace hamma na kama hannun hamma kb, su waye wadannan a ina nake me yake faruwa, na kalli noor nace noorie ina kika je. Likitan ya kalli babban mutumin nan yace In Shaa Allah memories din xasu dawo. A test result din mun ga temporary ne not permanent.
Two weeks later memories dina were back and many sad confessions were mentioned. Ummin jawad told me everything about tafiyan jawad, that it was not a business trip but a medical trip. Jawad was diagnosed with leukemia, duk 6months yana xuwa India ana masa blood transfusion, last trip dinsa ne ya je aka ce masa babu hope, baxai wuce 1 month ba. So he came back unfortunately a airport ya suma shine aka kawo shi hospital directly.
After I fainted due to shock na samu miscarriage, I was 3weeks pregnant, amman ban sani ba saboda I was unconscious for a month.
Ummi tace min kafin jawad ya cika ya bada sako cewar naje na duba home office akwai safe dinsa suna na ne password na duba akwai message daya bar min.

.....
Poor hajar, she's been through a lot.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: May 24, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

HAJARAH (ON HOLD) Where stories live. Discover now