ASHIRIN DA BIYU.

4.4K 502 3
                                    


(☆_☆)

Nanne ta tsirawa fuskarta ido a mudubin toilet tana nazari. A cikin sati d'aya kawai ta wani irin zabge kuma idanunta sunyi fari fat! sun d'ashe, kamar masu shirin fad'awa duk wanda ya kallesu irin adadin hawayen da suka zubar, ta kai hannu ta tab'a wuyanta a hankali inda wani rami ya fito tsakanin k'asusuwanta biyu.

Watakila na rashin cin abincin da bata yi ne, ko kuma  na yawan tunanin dake faruwa a cikin kanta. A sati d'aya kawai, kwakwalwarta tayi sak'a da warwara akan dubunnan abubuwan da a gabad'aya shekarunta na baya bata yi ba. A kullum zata tashi da fatan cewa wannan zaman da akayi na falon baffa bai faru ba, amma cikin awa daya kawai fatanta zai ruguje saboda irin hada-hadar da inna keyi kamar a satin ne za'a d'aura mata auren.

Aure. A kullum ta fadi kalmar ta sake maimaita ta tasan cewa bata shirya masa ba, don wani abu ne da kwakwalwarta bata taba hasko mata shi nan kusa, bama haka ba, ba zata iya tuna ranar da wai ta hango kanta a gidan aure ba. Balle kuma yanzu da akace za'a tura ta cikinsa nan kusa.

Kwallar da ta taru a idonta d'aya ta ziraro kan kumatunta, tasa bayan hannunta da sauri ta share. Ta riga ta yiwa inna alkawarin daina kuka, tayi mata alkawarin karbar al'amarin nan hannu biyu tun ranar data tasa ta a gaba da rok'on ta taimaka ta dawo da rayuwarta kamar da.

Don tun bayan fitowarta daga falon baffa a waccan ranar komai nata ya canja, ta daina magana, ta daina dariya, ta daina shiga mutane, bata da aiki sai ta dukunkune kanta a gado tayi ta turkar kuka. Ba irin magana da bin bakin da kowa a gidan bai mata ba amma bata ko fahimtar abinda suke fad'a.

Sai da inna taga abin nata na neman d'orewa ne yasa ta sameta ita kadai ta ajiye duk wani fad'anta a gefe ta rok'e ta akan ta taimaka ta yiwa mahaifinta da ita biyayya, tace su iyayenta ne, bai kamata su nemi abu a wajenta ba amna da sunan baffa da kuma ita yau tana neman alfarmata da ta basu had'in kai wajen gyara rayuwarta, don abinda suke k'ok'arin yi d'in taimako ne ga ita kanta.

Abin ya bata tsoro ganin innan na shirin durk'usa mata, a lokacin sai ta manta da komai tayi mata alkawarin cewa ta amince baza ta sake nuna damuwarta ba, tana hawaye itama innan nayi. Kuma tun daga wannan ranar, take kokarin ture duk wata damuwarta ganin ta farantawa innan. Bata k'ara kuka ko nuna b'acin ranta ba, sai dai kuma ta koma wata sabuwar halittar daban.

Bata magana, sai bada amsar abinda aka tambayeta kawai, bata dariya bata kuka, abinci ma tana cin iya wanda ta san zai hana ta galabaita ne kawai. A kullum zuciyarta cikin tarawa da d'ebe tunani kala kala take kawai.

Tunanin yadda zata yi ta fad'akar da kowa cewa ita ba wasu bak'ak'en aljanu dake shirin shafarta, rashin lafiyarta cuta ce kawai ba komai ba. Musamman baffa, tasha  had'a irin kalaman da zata je ta tsugunna a gabansa ta fada masa ya gane cewa ita lafiyarta kalau, ya taimaka ya janye maganganunsa rayuwarta ta koma daidai, amma a kullum ta tashi taga wannan farin cikin na fuskar inna, sai tunani ta ya karye ta shiga lalubar wata hanyar da zata fitar da ita.

"Yanzu Nanne har yanzu kina cikin band'akin nan?"

Muryar inna ta dawo da ita cikin zahirin da take.

Da sauri ta bude fanfaon sink d'in sannan ta taba butar dake gefe da kafarta, jin k'arar yasa innan tace.

"Toh Allah kuwa ya sawwake miki. Kiyi ki fito Rahman tun dazu take zaman jiranki, ga dare nayi."

Jin sunan Rahma yasa ta tuna da cewar yau zasu je can gidan malaman ta karbo magunguna, abinda yasa dole saida ita saboda akwai wani turare da malamin yace za'a dinga mata duk sati, kuma matarsa ce take yi. Sunje wancan satin anyi mata saura na yau kenan. Ta ja tsaki a k'asan numfashinta. Allah ya sani bata ko son ganin mutanen nan. Don a tunaninta, sune silar duk wani hali da take ciki a yanzu.

Waye Shi? Complete✓Donde viven las historias. Descúbrelo ahora