TALATIN DA DAYA.

5.3K 972 10
                                    

Dan Allah idan kuna tunanin yaya ake voting ba wani abu ne mai wuya ba, kawai ku danna wannan 'yar star din dake k'asan page din nan...voting d'inku shi zaisa in cigaba da updating a wattpad.

In da sauran na baya ma da baku yi ba, ku d'an taimaka ku ara min minti d'aya a lokacin ku, ku d'an koma kuyi voting...it will really made my day wallahi!😔

Na d'ebe muku kewa...atleast make me happy mana dan Allah..😁

Nagode muku!🙏

(☆_☆)

"Kin min shiru Sa'adha don Allah kiyi  magana, ko har yanzu fushin ne?"

Nanne ta sake tankwashe k'afarta akan gadon tana nannad'e bakin rigar filon dake kan cinyarta, a hankali tace.

"Kana lafiya?"

"Ina lafiya kuma yanzu da kika tambaya sai na k'ara jin lafiyar ta kama ni."

Tayi murmushi mai fad'i.

"Ina jinki ki fad'a min sau nawa kika tuna ni bayan lokacin da kika ce min sai da safe?"

Bata ce komai ba kamar yadda ya zata.

"Ko sau d'aya ne kawai sanda kika yi min flashing?"

Da sauri tace.

"Ni ba flashing nayi ba ban sani bane kawai kiran ya shiga na zauna a kusa da wayar."

"Irin wannan bayani haka kamar laifi kika yi?...yanzu toh ba wannan ba, baki tambayeni sauran bayanin jiya ba."

Ta d'an hade girarta kad'an.

"Wane bayanin?"

"Bayanin koni WAYE mana, ko ba kya sonp kiji abinda nace wa baffa ya bani aurenki? ko kuma ki san wane irin miji zaki aura?"

"Na san zaka fad'a min ai."

"Ta yaya kika sani? saboda kin san ina sonki?"

Kamar baza ta amsa ba sai kuma tace.

"Mhmmm.."

"Toh mhmm kema kina sona?"

Ta sake yin shiru.

"Ya Allah! Sa'adha kin mayar dani d'an jarida sai tambaya nake tayi akai-akai."

"Toh ina jinka, ka fad'a min."

"Shikenan mu ajiye wannan a gefe zamu dawo kansa daga baya, bari in fara baki tarihin mijinki tukunna.

Sunana Imran kamar yadda kika sani, amma full name d'in Imran Siddiq, ni d'an garin bauchi ne iyayena sun mutu tun ina yaro saboda haka a hannun k'annin mahaifina na tashi, A bauchi nayi duk karatuna da komai, sai daga baya na samu aiki anan garinku.

Aiki a company ORZ dake kula da harkokin talla na media platforms, shi yasa nake zaune ni kad'ai ba tare da kowa ba, don dukkan 'yan uwana suna can."

This is it! just simple kamar yadda suka tsara a farko zuwansa, haka normal rayuwar matashi irinsa ya kamata ta kasance.

Jin tayi shiru yasa ya cigaba da cewa.

"Tun daga bauchi 'yan uwana suka zo nema min aurenki kwanansu biyu a garin nan, kuma a duk kwanakin suna ta yabawa da irin tarbiyyar gidanku, sunce baffa mutumin kirki ne zanyi sa'ar auren 'yarsa."

Ta cigaba da nannad'e rigar filon a hannunta.

"Tun da suka koma kuma ake ta min waya daga gida, masu son ganinki na da yawa Sa'adha, basu san cewa ni kaina an hana ni zuwa ba."

Waye Shi? Complete✓Tahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon