Chapter 24

1.6K 109 5
                                    

Meeral❤🌺

24

Tsugunna yayi gaban ammi sai faman bata hakuri yake whilst ita kuma Tamasa shiru Ido tazuba masa ganin yarda duk yarame kaman ba zayn din taba,
Veil dinta ta jawo daga bedside tace idan kagama zaman bada hakurin kan na wofi ka biyo ni,,
Da saurin yabiyota a parlour yasameta tan bama husna sakon mai zata girka,

Parking space ta nufa tabude black rolce royce da sauri ya karaso yace ammi let me drive,
Noo kasan ai ba iyawane banyi ba tabasa amsa tareda shiga driver seat..
Bashida choice so kwai yashiga dayan side din,.
Tafiyan 1 hour sukayi sabida traffic da yayi yawa,  gidan uncle dinta sukaje, uncle illu
Dattijo ne sosai kuma babban malami wanda yayi suna, dalibansa suka Tarar a harabar babban gidan sa, gaisawa sukai inda suka shaida musu yana ciki,.

Gaba ammi tayi dan she's familiar with the house riko gyalanta yayi tabaya and ya tsaya ya ki cigaba da shigowa,
Wani kallo tabasa tace what's the meaning of that mai kakeyi hakan,
Dan marairaice murya yayi yace ammi mai zamuyi anan din,
Sakan baki tayi tana kallonsa dan tambayan yabata mamaki batasan Lokacin da tace masa ubanka zamuyi anan din,
Bashiri tacika ta dan its rare yaji ta zagesa..

Koda sukashiga matar uncle illu ne maifura suka fara Arba da, broom din da ke hannunta ta aje da faraan ta tace wanake gani haka kaman mai babban suna yau da kanki agari kushigo da ga ciki lale maraba lale, tabarma ta shinfida musu suka zauna sai washe baki take tana farinciki zuwan nasu,
Gaisheta ammi tayi cike da girmamawa sannan zayn ya gaisheta,
Dauke kai tayi ta kalla gefe tace ina wanan gaisuwan naka ai banna amsata Kaje can Kayiwa hajja bilki tunda ita ka dauka mata ni yaushe rabona da kai zaka wani bude katan bakinka kace mun ina wuni,,

Bata rai yayi shima yace wayace miki nima yin kaina ne ammi ne tasakoni gaba da nasan ma gidan nan Zaa zo ai da na kunto karnukan gidana su yayyagamun ke..

Muficinta ta dauko tayo kansa cike da masifa tace walh sai dau yacinye illu da hajja bilki ba dainiba shiyasa ni da azomin dakai gwanda mai gidana adeelu yazo dan ko ba komai yakazo akai akai yaduba ni, banda kai dan masu da mai jan kunne, gafarani malam in wuce nakawoma uwata fura,
Bangajesa tayi tawuce, kyajidashi dai banayi akai kasuwa yafada da sauti dan taji,
Ita dai ammi ba abunda take dai dariya dan sosai dramar sa da maifura ke sata dariya, inda sabo ai sunsaba dan tace ita adeel ne mai gidan ta shikuma sai Dai yayi amarya da hajja bilki wato maman ammi grandma dinsa.... Basu taba zama guri daya basu taba fadan nasuba....

After sun huta ne suka shiga gurin uncle illu dama Tamasa maganan before hand,
Wasa tsakanin kaka da jika suka sha shida zayn kafun ya gangara down to business.
Sosai yama zayn tunsarwa kan kara Dantse wajen kulla da ibadunsa musamman azkar domin yanada babban muhimmanci kuma tsarine ba karamiba sanan yace idan kuje
Gida

asamu ruwa mai tsafta, ganyen magarya koraye masu kyau guda bakwai idan ansamu busasu sunfi sai a Nika azuba cikin ruwan, sai  akaranta suratul Fatiha  acikinsa a dan ringa numfashi yana shiga ruwan,  sai a karanta ayatul kursiyyu, sai a karanta suratul aaraf daga kan aya ta 106 zuwa kan aya ta 122,
Sai a karanta suratul  yunus daga kan  aya ta 79 zuwa kan aya ta 82,
Suratul kafirun kafa daya, falaki da Nasi kafa uku uku, saikuma a karanta wanan
Aduuan
"Allahumma rabbanas azhibil ba'as ashfi wa antash shafi LA shifaa illa shifauk shifaun la yugadiru saqaman " kafa uku.

Sanan zaaiya karawa da wannan aduaan

Bismillahi urqiqa min kullin shaiin  yu'uzika wamin sharri  kullu nafsin Allahu yashfika, bismillahi
Urqiqa kafa uku..
A rubuce yamika ma ammi yace insha Allah taala idan aka karanta wadannan, kuma yaringa sha sau biyu arana da safiya da yamma, yakuma dinga wanka dashi a guri mai tsarki, ko kuma tsami towel yajika da ruwan ya dinga goge jikinsa, insha Allah nan da sati guda kowane irin shirine Allah s.w.t zai karyashi,
kallonsa ya maida kan zayn ka kara dagewa da azkar kaga wanan azkar din safen bakaramin kariyane ga mutumba,

Shidai zayn shiru yayi dan ba duka ya fahimci abunda uncle illu dinba, sihiri a jikinwa yake tambayan kansa, yasan ba mai basa amsa so kawai yaja bakinsa yayi shiru..

Bayan sun koma gidane ammi tabasa umarni akan tanasan  ya maida Farouk company dinsu na abuja then shikuma ya zauna ana kano na week,
Baiso hakan ba amma wanne shi da zai mata gardama.......
...........
*******
Yau tunda ta tashi take jin cikinta na murdanta so bata wani kuzari na fita duk nacin mahboob haka yayi yagama akan ta taso suje hsplt dinsa tare amma takiya...

Kofa taji anbude daga ido tayi dan ganin mai shigowan, haidar ne dauke da abinci, a jewa yayi sanan ya zagayo kan bed din, hands dinta yarike yace Adda miral kitashi kici abinci please for the sake of the baby, mom tace tana son taga kulan please kitashi,
dan jan hancisa tayi tareda mikewa tace yes little panda, dariya suka saka atare,,
A plate tasaka abincin tafaraci, phone dinta ne yafara kara, kallan haidar tayi tace little panda help,
Wayan ya dauko ya mika mata.
Bakuwan number tagani na naija so da kaman bazata dauka ba amma sai ta dauka..
Sallama tayi
Waalaikas salam aka amsa ta daya bangaren,
Sosai taji wani shock ya kamata dalilin voice  din dataji..
Daughter na mai gudun mom dinta akace a daya bangaren,,
Cikin in ina tace am.. mi.. Inn.. a kwana. Um ina wuni..
Lapia lau daughter, ya kwana biyu ya kuma mutane Agadaz.
Aje spoon din tayi takara nutsuwa shikenan na shiga uku zayn ya gano ni I hope amma ba hakuri zata bani ba n koma i have had enough tafada cikin ranta....

Duk wani karfin halinta ta tattaro tace lapia lau ammi kowa lapia, yasu  husna..
Lapia yanzu kalau ammi tabata amsa a takaice saikuma tafara magana cikin nutsu,
Miral naji mai ya hadaki sa mijin ki abun bai mundadi ba and ko kadan banga laipin decision din da kika yanke ba, sabida an zalince ki,
Dazu maamahn ki ta turan numbern da zan sameki,so I decided to call..
. dan ajiyan zuciya ammi tayi tace tsakanin ki da zayn macene tashiga ciki yea aikin sihiri ne, amma inasan kisani bana bayan zayn sabida duk da asirine to da sakaci, yes I mean da sakaci sabida da ace bai yisake ba har ya kula ita yarinyan da haka duk bai faruba..
So daughter ki kwantar da hankalinki inkikace bazaki koma auren zayn ba zan tsaya miki, idan kuma zaki koma I will make sure yasan value dinki,
Nasan kina bukatan hutawa so bazan hanaki zama a niger ba amma kiyi tunani sosai..
For the sake of your unborn baby ..

Wani tarine ya kwace ma miral dan bata yi tunanin ammi tasan tanada ciki ba kuma batasan ayi linking ma zayn zancen cikin...

Dan dariyan manya ammi tayi tace kina mamakin nasan kina da ciki ba to da innon ki nafara waya so she told me. And guess what am very happy janga jinin zayn mt first grand son.and don't you worry nasan bakisan zayn yasan dashi huh? To Kar kidamuu namiki alkwarin bazaiji abakin kowa ba sai naki,

Kunya ne yakama miral sosai a hankali tafurta ammi na gode, thank you I really appreciate. Sosai ammi takwantar mata da hankali...

Tun lokacin da kowa yasan whereabout nata sai wani kwanciyan hankali ya zoma, lapia lau zata kira ammi da maamah suyi tahira kaman ba abunda yafaru tana getting in touch da kowa, amma banda gogan....
*****************************************
Zayn ne kwance kan bed din ammi yayi pillow da laps dinta, idonsa lumshe suke kaman mai bacci, kana kallansa kasan yana ciki yanayin damuwa, dan mikewa yayi zaune ya kalla ammi ya marairaice murya yace ammi wlh nagaji da jiran a nemo min inda miral take, nasani nayi mata laipi I've wrong her na mata abunda banyi tunanin zanmataba, amma ammi I wasn't in my right sense, wani hawaye ne yafito masa hannu yasaka yana goge su..

Wani tausayinsa taji ya shigeta almost 8 months kenan da karyewan asirin jikinsa ana abundaya kullum cikin ma ammi kuka yake shi matansa. Akwai Lokacin da kwata kwata yadainacin abinci saida Tamasa wuta wuta tukkuna yadan fara tsakuran wani abun company dinsa kuwa duka yasakarma Farouk both kano da abj dan gaba daya yatare gurin ammi,. Haka zaije gun maamah yayi ta rokanta akan shi matansa, amma ammi tace kul kar akuskura afadamasa...

Jawo hannunsa ammi tacike da rarrashi, tace ka kwantar da hakalinka zayn indai Allah yayi da cigaban zaman ka da miral bawanda zaihana.....

Abinci tasaka husna ta kawo masa, gaba tasa kashi yaci da dan dama...

Vote , share , comment and follow
Chuchujay

MEERAL💗 (completed) Editing Where stories live. Discover now