Ba ni Bane

1.4K 89 6
                                    

🤵🏻🧕🏻🙎🏻‍♂BA NI BANE 🤵🏻🧕🏻🙎🏻‍♂

   (A heart touching story)
                                
                Nah
      Marubuciyar Zamani

    NABILA RABI'U ZANGO         
       (Nabeelert Lady)

Email.....
nabilalady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey
Wattpad.... Nabeelertlady

*Part* 3 & 4

Zaune Malanto yake yana rik'e da hannun  Mahaifiyar Anwar shima idanuwanshi sun cika da kwalla. A hankali Mama tace Malanto ga amanar Anwar nan,  kafi kowa sanin irin zaman takurar da Anwar yake a cikin wannan garin,  haka Allah yaso Anwar zai zo duniya ta haramtacciyar hanya,  bamu da ikon canza K'addararsa,  addu'a ita kad'ai ce abinda zamu cigaba dayi masa,  nasan tawa tazo k'arshe,  gaba d'aya nauyin kula da Anwar zai dawo kanka,  gashi kai kuma ba mazaunin gida kamar ni ba,  ina rok'on alfarma awajen ka,  kada ka bari Anwar yayi kukan rashi na,  nasan da kamar wuya ka iya kare Anwar daga sharrin matar ka,  amma ina rok'on ka amatsayin ka na maigida daka kula da Anwar,  yanda yake da burin yin karatu na roke ka daka barshi ya kammala ko wannan ne daya fara tunda ya kusa gamawa,  wannan abun shi kad'ai zamuyi masa ya zamo gatansa,  domin azamanin yanzu kud'i sune maganin komai,  idan Anwar ya same su zasu rage masa wani zafin,  domin ina tausaya masa a duk lokacin da zai fara neman aure,  ayanzun ma da ba auren zeyi ba kana ganin yanda kowa baya son ya ganshi tare da d'iyarsa,  dan haka ka daure ka barshi yayi ilimi,  koda ba wani hali ne damu ba amma Anwar tsayayyen namiji ne,  zai iya sana'a domin ya samu kud'in makaranta.

Tari ne ya sark'eta hakan yasa tayi shiru. Matsowa Anwar yayi yana kuka ya rik'e d'ayan hannunta yana mata sannu. Malanto yace *UWANI* kidena fad'ar haka,  ciwo ba mutuwa bane,  insha Allahu dani da ke zamu taimaki Anwar yayi ilimi,  kuma kema zakici moriyar ilimin Anwar,  dan haka bara naje na samu Malan Habu yazo mu kaiki asibiti.

Hawaye ne suka zubo mata tana girgiza kai,  dan maganar ma ta kasa fitowa. Cire hannunsa yayi ya tashi yana fad'in Anwar gyarata bara naje na dawo.... Yana fita Anwar ya fara kok'arin saka mata hijabi ajikinta. Rik'e masa hannu tayi tana fad'in Anwar kaji tsoron Allah a duk inda kake,  kada k'uncin rayuwa yasa ka canza halayenka masu kyau i zuwa marasa kyau,  nasan kasan cewar kai d'in ba d'an halak bane,  amma duk da haka baka tab'a tunanin yi mani magana akan asalin labarinka ba,  kamar yanda nasha fad'a maka tabbas Malanto shine mahaifinka,  sai dai ba da aure muka sameka ba,  wata mummunar K'addara ce da sharrin makiya  yasa muka sameka ta hanya marar kyau,  amma koba yanzu ba wata rana Malanto zai warware maka komai,  kuma bana fatan kace zaka d'auki wani mugun mataki akan wad'an da suka aikata mana haka,  kamar yanda mukayi hak'uri kai ma ina so kayi hak'uri,  insha Allahu zaka samu ingantacciyar rayuwa mai kyau,  Allah zai jibanci lamuran ka,  kai dai ka rik'e gaskiya kuma ka rik'e Allah zakaga sakayya.

Hannu Anwar yasa ya goge kwallar data zubo mashi yace Mama ki daina fad'ar haka,  insha Allahu bazan tab'a canzawa daga yanda kika sanni ba,  zanyi kok'arin k'arawa akan yanda kika sanni,  kuma bazaki mutu ba, zaki rayu dani kuma wata rana zan jiya maki dad'i.

Murmushi Uwani tayi tana kallon Anwar hawaye suna zubowa daga idanuwanta. Shak'uwa ta farayi hakan yasa Anwar yayi saurin tashi yayi waje domin ya d'ebo mata ruwa. A bakin tukunyar ruwan yaci burki ya d'aga yana kok'arin kwalfo ruwa akofi,  sai dai abun haushi babu ko d'igin ruwa a ciki,  da sauri ya nufi k'ofar d'akin Lantana da kofin domin ya samo mata ruwan sha.

Jin sallama da k'arfi yasa Lantana ta fito a fusace domin ta gane muryar Anwar. Tsaye ta iskeshi yana hawaye,  kugu ta rik'e tana jiran taji abinda zai ce..... Dan Allah Gwaggo ki bani ruwa Mama ce bata da lafiya Malanto yaje kiran malan Habu su kaita asibiti gata can sai shak'uwa takeyi alamun tana buk'atar ruwa.

BA NI BANEWhere stories live. Discover now