Ba ni bane

1K 86 3
                                    

🤵🏻🧕🏻🙎🏻‍♂BA NI BANE 🤵🏻🧕🏻🙎🏻‍♂

   (A heart touching story)
                                
                Nah
      Marubuciyar Zamani

    NABILA RABI'U ZANGO         
       (Nabeelert Lady)

Email.....
nabilalady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey
Wattpad.... Nabeelertlady

*Part* 9 & 10


Koda suka koma gida bayan sunci abinci haka aka shafama Amal maganin da Malan ya bata kafin sukayi mata duk abinda ya dace sannan suka kunna mata karatu. Sai da tayi bacci kafin Ammar yabar d'akin yayi ma su Abbah sai da safe ya wuce d'akinsa cike da tausayin Amal.

Koda ta tashi washe gari bata ji komai ba,  kamar yanda taji jiya hakan ne ya faru da ita yau. Sosai sukaji dad'i anan Abbah ya kira Malan ya fad'a masa. Malan yace zuwa yanzu ya isa ku tabbatar da abinda nake zargi,  amma ko menene zuwa gobe idan kuka zo zamu k'ara tabbatarwa,  domin rashin nuna alamunsu akwana biyu ba yana nuna cewar sun barta bane,  dan haka dole musan dalilin su na shiga jikinta kuma a magancesu gaba d'aya.

Abbah yace mungode Malan,  insha Allahu goben muna nan zuwa. Sallama yayi mashi ya kashe wayar. Anan yayi masu bayanin abinda Malan yace. Umma tace ikon Allah,  ko ina Amal ta samo aljanu ita da ba makarantar kwana tayi ba? Abbah yace ai su aljanu ba dole sai a makaranta ake samun su ba,  duk inda muke suna nan Allah ne kawai yake karemu sannan muma mu kiyaye,  idan mukaje goben zamuji komai ai. Ammar yace Allah yasa muji alkhairi.  Sukace amin.

***** *****

Zaune Anwar yake a k'ofar gida shida Malanto. Anwar ne yace Malanto Dadah tace anjima kaje ka amso kud'in an kawo mata. Malanto yace kai amma naji dad'i,  amma bazan amso su ba,  ka tashi kaje ka fad'a mata ta barsu awajenta goben idan zaka tafi sai ka biya ka amsa,  kaga wancan karon har cikin d'akin ka akaje aka d'auke kud'in wanda ko shakka babu nasan Zakari ne ya d'auke su,  amma saboda rashin gaskiya sai Lantana tace *Ba shi bane*,  kaga yanzu idan na amso su ana iya k'ara d"aukewa.

Anwar yace haka ne,  bara naje na fad'a mata to. Malanto yace Anwar meyasa baka fad'a mani abinda ya faru da kai jiya ba? Duk'ar da kai Anwar yayi bece komai ba.

Malanto yace kaima kasan ko ka b'oye mani dole ne naji,  wani ma kodan ya bak'anta mani rai yana ganina zai bani labari,  tun daga bakin hanya na samu labari,  haka ina zuwa gida Lantana da zancen ta tarbeni,  amma ganin bakayi mani magana ba yasa nima nayi shiru.

Anwar yace Malanto meye amfanin na fad'a maka? Babu abinda hakan zai haifar maka sai b'acin rai,  naji dad'i alokacin daya kasance baka nan,  tunda komai yawuce kawai kacire komai aranka.

Malanto yace ka k'ara hakuri kaji Anwar,  wannan abun da yake faruwa da kai ba laifin ka bane amma kuma gashi kana cikin damuwa,  duk abinda ya faru mune da laifi da muka kawo ka duniya ta haramtacciyar hanya,  naso tun kafin a haifeka mu zubar da cikin ka sai Uwani tace bata yarda mu aikata kisan kai ba...... Shiru yayi yana goge hawayen da suka zubo mashi kafin yacigaba da fad'in k'adddara ta riga fata,  Allah ya rubuta dole kazo duniya kuma ka rayu,  amma har mutuwa ta bazan tab'a daina kallon wad'an da suka kasance silar faruwar hakan ba.

Shiru yayi yana kuka kamar k'aramin yaro,  hannu yasa ya dafe saitin zuciyarshi da yake masa ciwo a duk lokacin da yake kok'arin tuna abinda ya faru shekarun baya da suka wuce. Da sauri Anwar ya tashi yashiga gida ya d'ebo masa ruwa. Sai da yasha ya saki ajiyar zuciya. Zama Anwar yayi shima yana goge hawayen fuskarshi yace Malanto wannan abun yariga ya faru,  bazamu tab'a goge abinda ya faru ba,  dan haka bana so ka sake tada wannan maganar,  domin duk lokacin da zakayi ta sai kashiga wani yanayi,  kuma hakan zai iya haifar maka da matsala,  na rasa Mama bana fatan kaima na rasa ka,  nine dai kake so ka bama labarin abinda ya faru to na yafe maka,  tunda dai Allah yasa nasan asalina bani da damuwa akan hakan,  addu'ata d'aya Allah ya bani abinda zan kyautata maka.

BA NI BANEWhere stories live. Discover now