Ba ni bane

1K 91 11
                                    

🤵🏻🧕🏻🙎🏻‍♂BA NI BANE 🤵🏻🧕🏻🙎🏻‍♂

   (A heart touching story)
                                
                Nah
      Marubuciyar Zamani

    NABILA RABI'U ZANGO         
       (Nabeelert Lady)

Email.....
nabilalady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey
Wattpad.... Nabeelertlady

*Part* 15 & 16

*Ina masoya makaranta littafin fitattar marubuciyar nan wato NABILANCY LUV?  Ku garzayo domin ta sake fito maku da wani hamshakin littafi wanda yake kunshe da labarin wata masaurata,  kada ki/ka bari abaku labarin,  littafin yana nan ta farashi,  kada ku manta sunanshi KUYANGA.*


A daren ranar bacci b'arawo ne kawai ya iya d'auke Anwar,  domin zuciyarsa tashiga damuwa akan maganganun Maigari,  bai san loakcin da soyayyar Zeenat tashiga zuciyarsa har haka ba,  da ya rufe ido ita yake gani tana dariya ko kuma tana masa shirmenta. Cike da tunanin ta ya samu bacci yayi awon gaba dashi.

Can cikin dare Zakari ya fito daga d'akinshi,  kasancewar tunda Maman Anwar ta rasu Lantana ta tada fitinar dole araba masu d'aki tunda dai sun girma,  anan Malanto yace shikenan Anwar ya gaji d'akin mahaifiyarsa, shi Zakari yacigaba da kwana a d'akin zaure.

Nan fa Lantana tayi ta bala'i akan dole Anwar ne zai zauna ad'akin zaure saboda bashida gadon Malanto,  ganin abun zai zama fitina yasa Anwar yace abarshi a d'akin zaure shi Zakari ya shiga ciki. Wannan dalilin ne yasa aka raba masu d'aki.

Cikin sand'o Zakari yashiga d'akin Anwar,  alokacin bacci kawai Anwar yakeyi,  haka ya fara bincika masa kaya sai dai duk yanda yaso baiga alamun kud'i ba,  haka ya gaji da bincikenshi ya fita.

Tun fitowarshi daga d'aki Malanto yaji motsi hakan yasa ya lek'o,  akan idonshi yashiga d'akin Anwar har ya fito,  yana jinshi yana tsaki yana fad'in shegen shi kad'ai yasan inda ya aje kud'in,  wallahi da na gansu saina d'auke muga ta yanda zai tafi makarantar.

Murmushi kawai Malanto yayi ya koma ciki,  dama yana zargin Zakari yana da sa hannu wajen sace wad'an can kud'in,  hakan yasa wannan karon yace abarsu hannun Dadah,  sai gashi kuma yaje d'auka kuma bai samu ba.

***

Washe gari bayan da Anwar ya gama shiri ko abincin kari aranar Lantana bata bashi ba,  saboda tunda safe Zakari ya sheda mata baiga kud'in ba hakan yasa take cike da haushinsa. Koda ya gama shiryawa har d'aki ya sameta,  k'asa ya duk'a yana gaisheta amma da kyar ta amsa tana wani harararshi.

Kallonta yayi yana fad'in Gwoggo zan tafi makaranta saura watanni biyu mu gama ayi mani addu'ar samun nasara akan jarabawar da zanyi. Murmushi tayi tana fad'in ashe ka d'aukeni a matsayin Uwa ban sani ba? Idan har kana mani kallon Uwa mai yasa sai yau kazo kasanar dani zaka tafi makaranta bayan nasan ba yau kasan da maganar ba?  Anwar yace kiyi hak'uri na d'auka Malanto ya fad'a maki ne.

Tab'e baki tayi tana fad'in wannan munafukin Uban naka taya zaiso naji wani abu daya danganceka,  to tsaya kaji,  wallahi babu wata addu'a da zanyi maka,  da kake maganar neman sa'a waya fad'a maka sa'a tana biye da kai?  Ai kai da sa'a har abada arayuwarka,  rashin sa'a ne yasa aka haifoka ta gurb'atacciyar hanya,  wallahi Anwar zanso kaji labarinka nasan zakaji d'aci aranka,  babu wata k'addara data sa aka sameka kawai iskanci ne da son zuciya yasa Iyayenka suka haifoka ta wannan hanyar. Dan haka katashi ka bani waje,  kamar yanda Zakari beyi karatu ba kaima babu amfanin da naka zeyi maka.

Murmushi Anwar yayi yace nagode Gwoggo saina dawo,  idan Zakari yashigo ace masa na tafi dan na duba d'akinshi baya ciki. Lantana tace aikin banza,  kuma kada ka sake ka d'aukar mani abinci domin ban dafa da kai ba. Tashi yayi ya fita yana mai kok'arin danne hawayen da suka taho mashi.

BA NI BANEWhere stories live. Discover now