Ba ni bane

1K 103 16
                                    

🤵🏻🧕🏻🙎🏻‍♂BA NI BANE 🤵🏻🧕🏻🙎🏻‍♂

   (A heart touching story)
                                
                Nah
      Marubuciyar Zamani

    NABILA RABI'U ZANGO         
       (Nabeelert Lady)

Email.....
nabilalady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey
Wattpad.... Nabeelertlady

*Part*  61&62


Likitoci ukku ne suka taru akan Amal suna kok'arin ceto rayuwarta dan bugun zuciyarta baya tafiya dai-dai,  ga numfashinta yaki tsayawa yanda akeso. Sosai likitan ta ya firgita da yanayinta kasancewar bata tab'a irin haka ba. Sun kwashe kusan awa d'aya kafin suka samu bugun zuciyar ya fara dai-daita,  amma duk da haka da sauri take bugawa,  numfashinta kuma ya koma yanda ake so.

Umma ta rasa inda zatasa kanta,  jikinta sai rawa yake idanuwanta har sun kumbura saboda kuka, sosai take tsoran rasa Amal kamar yanda ta rasa Ammar. Abbah ne ya kamota shima duk yashiga damuwa,  ba dan namiji bane shima da yayi kukan don zuciyarsa cike take da damuwa,  dama irin wannan ranar yake tsoro,  tun bayan da Ammar ya rasu suka tsara wannan abun be tab'a zaman lafiya da zuciyarshi ba,  ko bacci yazo wannan ranar kawai yake tunanin zuwanta,  kullum addu'arshi Allah yasa idan ta tashi zuwa tazo masu da sauki,  sai gashi tazo a wannan yanayin,  fatanshi d'aya Allah ya tashi kafad'ar Amal.

Anwar kuwa tunda suka zo ya samu waje ya zauna, haka ya duk'ar da kai hawayen tausayin Amal suna zubo mashi tare da makomar soyayyarshi agareta,  yasan yanda ta gane ya yaudareta da wuya ta amince dashi idan ya fito da buk'atarshi. Wayarsa ce tayi k'ara yana dubawa yaga Saddik ne,  bayan ya d'auka ya sheda mashi halin da ake ciki,  Saddik yace gasunan zuwa suna tare da Aneesah ma. Anwar yace sai kunzo.

Bud'e k'ofar da Amal take ciki akayi hakan yasa gaba d'ayansu suka mik'e jiki a sanyaye suna kallon likitocin. Ganin sunyi hanyar office yasa Abbah yaja Umma suka bi bayansu.

Suna shiga d'aya daga cikin likitocin ya dafa Abbah yana fad'in Alhaji ka kwantar da hankalin ka Yarinyar ka tana kan samun lafiya domin munyi nasarar dai-daita numfashinta,  bugun zuciyarta ma ya ragu sosai akan lokacin da kuka zo.

Abba yace likita a wane mataki ciwon zuciyarta yake yanzu? Zama likitan yayi yana fad'in gaskiya zuciyarta ta d'an samu rauni a dalilin bugawar da tayi sakamakon firgicin data shiga,  haka zalika alokacin ta samu sark'ewar numfashi wanda ya jowa mata suma,  sannan jinin data zubar ya fito ne daga zuciyarta,  dan haka dole sai mun kwantar da ita ta samu taimako sosai kamar na sati d'aya,  idan mukaga da sauki ina ganin ba sai an fitar da ita ba,  amma idan matsalar tacigaba gaskiya shawarar da zan baku gara akaita india ayi mata aiki,  gara tun da wuri ayi saurin tarbar abun,  kasan d'an Adam akoda yaushe zai iya tsintar kanshi cikin jarabawar Allah,  idan irin haka zai cigaba da faruwa da ita gaskiya zuciyarta zata iya bugawa lokaci guda wanda hakan zai iya  jawo ta rasa ranta,  shiyasa nace idan babu sauki gara kuje ayi mata aikin wanda nasan bazai kasance mai wuya ba saboda abun baiyi tsanani ba.

Jinjina kai Abbah yayi yana fad'in matuk'ar Amal zata samu lafiya babu matsala afitar da ita shine zaifi,  kuma hankalin mu zaifi kwanciya domin wata rana ba'asan abinda zai iya samunta ba. Likita yace wannan haka yake,  amma kucigaba da addu'a idan Allah ya so ta sai kaga ta samu lafiya cikin ikonsa. Abbah yace Allah yasa haka likita,  nagode sosai. Likita yace babu damuwa,  yanzu an kaita d'akin da zata zauna wanda babu kowa aciki sai ita d'aya,  kuma munyi mata allurar da zata d'auketa har zuwa nan da kwana ukku kafin ta farka domin hakan ne zaisa zuciyarta ta samu hutu dan kada ta tashi ta rik'a tuna abinda ya faru da ita ba tare da zuciyar ta dai-dai ta ba,  dan haka zaku iya tafiya nan da kwana ukku sai ku dawo.

BA NI BANEWhere stories live. Discover now