Ba ni bane

1.1K 130 12
                                    

🤵🏻🧕🏻🙎🏻‍♂BA NI BANE 🤵🏻🧕🏻🙎🏻‍♂

   (A heart touching story)
                                
                Nah
      Marubuciyar Zamani

    NABILA RABI'U ZANGO         
       (Nabeelert Lady)

Email.....
nabilalady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey
Wattpad.... Nabeelertlady

*Part*  71&72

Tun asalin abinda suka aikata ma Uwani da Dadah sai da Lantana ta bada labari,  hada asirin mallakar da suka yima Mahaifin Uwani da yanda suka yima Malanto asiri ya auri Lantana da yanda Boka ya biya buk'atarshi da ita da sauran abubuwan da tayima Uwani har zuwa mutuwar ta da yanda take kuntata ma Anwar sai da ta basu labari.

Shiru tayi tana sakin ajiyar zuciya sai kuka takeyi. Gaba d'aya jikin mutane yayi sanyi,  wasu da dama hawayen tausayin Malanto,  Uwani da Anwar sukeyi,  yayin da wasu haushin Lantana da Gwoggo ya cika zuciyarsu,  ji suke ina ma abasu dama su k'addamar masu.

Wakilin Maigari ne yace kina b'ata mana lokaci,  domin baki k'arasa bamu labarin abinda ya faru ba.,  munji Mahaifin Zakari,  shima wannan cikin Ubansu d'aya da Zakarin?  Kai Lantana tashiga girgizawa tana wani irin kuka,  baza ta iya bud'e baki ta fad'ama mutane 'Danta ne Mahaifin yaron ba.

Duk yanda akayi da Lantana akan tayi magana kasawa tayi,  k'arshema zubewa tayi k'asa tana wani irin kuka tana rik'e kirji. Zuciyar musulunci tasa wasu daga cikin mutane suka fara tausayin Lantana,  yanda take kuka dole zuciyarka ta tsinke.

Malanto kanshi duk'ar da kai yayi hawaye suna zubo masa,  yasan Lantana tayi masa mugun abu, amma ayau sai yakeji dama ya rufa mata asiri domin yana aiyana irin kuncin da takeji acikin zuciyarta ayanzu,  sai dai yana so ya kawo gyara agarin shiyasa yakeso kowa yasan abinda tayi ko dan a wanke Uwani daga zargin da ake masu.

Shiru Anwar yayi yana kallon Lantana hawaye a saman fuskarshi,  a hankali ya juya wajen da Zakari yake,  tun d'azu daya duk'ar da kai har yanzu be d'ago ba,  duk wanda ya ganshi yasan yana cikin wani irin yanayi,  hakan da yayi sai Anwar yaji mugun tausayinsa,  duk da yasan Zakari baya sonshi amma ayanzu sai yake jin tausayinsa,  yasan shima yasha tsangwama acikin mutane,  amma na Zakari yafi nashi,  meyafi bakin ciki ace Boka shine mahaifinka?  Lallai Zakari yana cikin damuwa.

Maigari ne yayi gyaran murya hakan yasa kowa ya natsu,  kallon 'yan sanda yayi yana fad'in ku tafi da ita,  ayi mata horo mai tsanani har sai ta amsa zata fad'i amsar da aka tambayeta.

" *NI NE ZAN BADA AMSAR TAMBAYAR KU.*" Da sauri mutane suka juya suna kallon Zakari daya tashi tsaye yana hawaye. Gyara zama Maigari yayi yana fad'in muna jinka. A firgice Lantana ta mik'e tana fad'in Zakari ban amince maka ka fad'i komai ba,  laifi ne mun riga mun aikatashi bai kamata ka fad'i komai ba, na yarda a yanke mani hukuncin daya dace amma kada kayi magana.

Murmushin takaici Zakari yayi ya kauda kai,  bega amfanin b'oye komai ba,  lokacin da taje wajen Boka yayi mata cikinshi batayi tunanin ya shi zaiji ba duk ranar daya san Boka ne mahaifinsa?  Dole ya fad'i wannan maganar domin kowa yaji.

Gyara tsayuwa yayi yana fad'in *NI NE MAHAIFIN ABINDA YAKE CIKIN UWATA!* Gaba d'aya wajen sai da ya amsa jin abinda Zakari ya fad'a,  hayaniya ce ta kaure awajen kowa da abinda yake fad'a,  duk yanda Maigari yaso ayi shiru kasawa yayi,  dole ya kyalesu kowa yacigaba da fad'in abinda yake bakinsa.

Anwar jiyayi kamar ya nutse saboda kunya,  wai Matar Mahaifinsa ce ake ma wannan tonon asirin agaban mutanan da yake so ya auri 'Yarsu, da yasan haka zata kasance daya taho shi d'aya domin ya rufe wannan bakin sirrin,  da gefen ido ya kalli Amal sai ganinta yayi ajikin Umma tana hawaye. Duk'ar da kai yayi yana wani irin kuka. Saddik da jikinshi yayi sanyi yasa hannu ya rik'o Anwar yana bashi baki.

BA NI BANEWhere stories live. Discover now