Ba ni bane

1K 117 14
                                    

🤵🏻🧕🏻🙎🏻‍♂BA NI BANE 🤵🏻🧕🏻🙎🏻‍♂

   (A heart touching story)
                                
                Nah
      Marubuciyar Zamani

    NABILA RABI'U ZANGO         
       (Nabeelert Lady)

Email.....
nabilalady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey
Wattpad.... Nabeelertlady

*Part*  65&66

Zaune Dadah take a gefen Malanto ita da Gwoggo wacce ana fad'a masu ta baro Lantana ta nufo wajen Malanto domin taga halin da yake ciki. Hannu Dadah ta cire daga tagumin da tayi tana fad'in ikon Allah,  wannan abu kamar magani,  ace daga wannan sai wannan. Gwoggo tace wallahi nima nayi mamaki da aka fad'a mana halin da yake ciki,  bayan ya dawo sallar asuba sai da ya leko muka gaisa ya duba Lantana da jiki amma sai gashi ance ya suma.

Shigowar likita yasa sukayi shiru,  gaishe su yayi kafin ya k'arasa kusa da Malanto,  ruwan da aka sa mashi ya duba, ganin ya k'are yasa ya kashe ya zare dama d'aya za'a sa mashi. Kallon su Dadah yayi yana fad'in kada ku damu zuwa anjima zai iya farkawa,  yaji abinda ya d'aga mashi hankali shiyasa ya suma,  amma munyi masa allura insha Allahu zai tashi lafiya.

Dadah tace Allah yasa,  mungode likita. Fita yayi yana fad'in ba damuwa. Gwoggo tace ni har yanzu basu fad'a mana abinda yake damun Lantana ba,  an dai saka mata ruwa kuma tunda ya k'are suka cire sai magungunan da suka bata amma basu ce komai ba,  har awon fitsari akayi mata sai kace wadda take da juna biyu amma basu fad'a mana sakamakon ba.

Tab'e baki Dadah tayi tana fad'in dama ai Malanto zasu fad'amawa tunda shine maigidanta,  sai mujira ya farka muji daga bakinsa. Gwoggo tace wallahi duk jikina yayi sanyi,  haka kawai nakejin fad'uwar gaba. Dadah tace meye abin jin fad'uwar gaba sai kace wata marar gaskiya?  Murmushin yak'e Gwoggo tayi tana fad'in haba bakomai kawai fad'a nayi.

Tashi tayi tana fad'in bara na koma wajen Lantana ko akwai abinda take buk'ata. Dadah tace bara muje na dubata ita da Zakarin. Gwoggo tace to muje wajen Zakarin sai mu wuce d'akin su Lantanar.

Koda Zakari yaga Dadah duk sai kunya ta kamashi, rabon daya ganta har ya manta. Kallonshi Dadah tayi tana fad'in sannu Zakari Allah ya baka lafiya. Hannu yasa yana sosa kai yace amin Dadah nagode. Gwoggo tace kaci abinci ko?  Zakari yace Malanto ya bani sai dai har yanzu bai dawo ba. Gwoggo tace shima yana can an bashi gado suma yayi. Zakari yace lafiya meya sameshi kuma?  Gwoggo tace ikon Allah kawai. Dadah tace Allah ya k'ara sauki muje wajen Lantanar. Zakari yace nagode ku duba ta.

Lantana ma sai da taji kunya ganin Dadah. Zama Dadah tayi,  bayan sun gaisa ta duba ta. Lantana tace da sauki ya Malanto da jikin?  Dadah tace be farka ba. Lantana tace ai likita yace yau za'a sallame ni ma. Dadah tace to Allah ya k'ara sauki. Tashi tayi ta koma wajen Malanto.

Tana zuwa ta iske ya farka,  saurin k'arasawa tayi tana fad'in sannu Malanto ashe ka farka?  Tashi yayi ya jingina yana rik'e kanshi yace yauwa Dadah yaushe kika zo?  Dadah tace tare mukazo da Mande har ya tafi yana duba ka.

Malanto yace ina amsawa. Zama Dadah tayi tana fad'in wai meyake faruwa har ka suma?  Hawaye ne suka zubo a fuskar Malanto. Dadah tace lafiya?  Cike da damuwa Malanto yace Dadah ina ganin jarabawa arayuwata,  bansan lokacin da zan daina ganin jarabawa arayuwata ba,  gani nake kamar sab'a ma Allah da nayi wajen samuwar Anwar ta hanyar banza yasa nake ganin ba dai-dai ba.

Dadah tace subhanallahi! Haba Malanto,  sai kace ba musulmi ba?  Dan Allah ka daina fad'ar irin wannan maganar kada Imanin ka yayi rauni, duk abinda kaga ya faru da bawa to Allah ne ya shirya masa hakan,  fad'a mani abinda yake faruwa.....

BA NI BANEWhere stories live. Discover now