Ba ni bane

750 52 10
                                    

🤵🏻🧕🏻🙎🏻‍♂BA NI BANE 🤵🏻🧕🏻🙎🏻‍♂

   (A heart touching story)
                                
                Nah
      Marubuciyar Zamani

    NABILA RABI'U ZANGO         
       (Nabeelert Lady)

Email.....
nabilalady5@gmail.com
Facebook...Nabeela Ladeey
Wattpad.... Nabeelertlady

*Part*  37&38

Sosai Anwar yaji tausayin Amal,  lallai tunda yake arayuwarsa bai tab'a jin labarin shak'uwa irin tasu ba,  dole Amal tashiga tashin hankali idan ta samu labarin mutuwar Ammar,  gashi kuma tana fama da mugun ciwo,  a zuciyarshi yaji yana so ya taimaka masu,  duk da zai sha fama kafin ya iya wasu abubuwa na Ammar amma zaiyi kok'ari domin ganin ya taimaka masu kamar yanda suka taimakeshi,  ya sani zamanin nan taimako yayi k'aranci,  yanda yake tsananin buk'atar taimako kuma ya samu masu taimaka mashi dole ma ya amince dasu.

Muryar Alhaji Babba yaji yana fad'in Anwar kaji kad'an daga cikin labarin su *Ammar* da *Amal*,  sannan kaji buk'atar da muke  nema a wajenka,  ko nawa kake so munyi alk'awarin baka matuk'ar zaka taimaka mana,  a wajen Amal kawai kake Ammar,  itace bama so ta fahimci abinda yake faruwa har sai ciwonta ya dai-daita,  idan yaso a hankali sai mu fad'a mata.

Jinjina kai Anwar yayi yana fad'in Alhaji ni bazan amshi kud'in ku ba,  ko iya Muhallin da zaku bani ya isheni,  domin nasan zanyi rayuwa mai 'yanci wadda ban tab'a tunanin samunta arayuwata ba,  dan haka zanyi kok'arin yin abinda ya dace ba tare da an samu matsala ba.

Hamdala gaba d'ayansu sukayi,  babu wanda ya kai su Abbah da Umma farin cikin wannan abu,  hawayen murna kawai sukeyi,  wannan abun da suka samu ya sanyaya masu zuciya akan damuwar rashin Ammar,  domin sun samu biyan buk'ata akan abinda suke so.

Kawu ne yace mungode sosai Ammar. Saurin kallonshi Anwar yayi jin ya kirashi da wani suna. Jinjina kai Kawu yayi yana fad'in dole  ka saba da wannan sunan,  domin kowa dashi zai rik'a kiran ka,  da hakan ne kawai zamu kauda idon kowa akan ku,  sannan maganar karatun ka ina ganin zaka hak'ura da karatun ka kacigaba dana Ammar,  tunda Allah yasa kayi diploma akan Enginearing shi kuma ya karanci building ina ganin babu abinda zai gagareka musamman da yake yanzu aikin Nigeria da ya zama sai ahankali,  sai kaga wani yayi masters akan abu amma ba zai iya tsayawa yayi depending kanshi ba,  kaga kuwa kai zaka iya amfani da karatun wani,  idan ma kana ganin zaka samu matsala akan karatun da bakayi ba zamu iya sama maka karatu na online gashinan anayi idan yaso sai kayi domin ka k'ara sanin komai akan abinda Ammar ya karanta,  domin ance idan zakayi abu gara ace kana da sani akanshi sosai.

Anwar yace hakan bazai bani damuwa ba,  domin dama art na karanta a makaranta,  abinda naso samu kenan Allah beyi ba na karanci wannan fannin,  dan haka wannan ba abun damuwa bane.

Alhaji Babba yace gaskiya naji dad'i sosai,  ubangiji ya bamu sa'a akan wannan abu da zamuyi,  duk da yayi kama da rashin gaskiya amma Allah yaga nufin mu,  ko daga baya ma idan kana son kayi degree akan karatunka duk zaka iya yi domin kai ma kacika burinka.

Anwar yace nagode sosai Allah ya k'ara girma yaji k'an Ammar. Gaba d'aya sukace amin. Abbah yace na rasa bakin magana saboda farin ciki,  mun rasa Ammar gashi Allah ya kawo mana wani, mungode sosai Allah yajik'an mahaifiyarka. Anwar yace amin. Umma tace amma Baba idan Amal ta  farfad'o taga ban-bancin halayya a wajen Anwar bazata zargi komai ba?  Alhaji Babba yace kin kawo magana mai muhimmanci kuwa,  ina ganin tunda Amal tasan sunyi had'ari dole zamu fad'a mata Ammar yayi loosing memory hakan zaisa kowa ma ya ajiye tambayarsa akan canjin halayyar da zasu gani wajen Anwar,  hatta da ita budurwar tashi dole asanar da ita ya samu matsala domin kada taga canji tashiga damuwa,  idan yaso daga baya sai kowa yasan gaskiya nasan zasu fahimce mu.

BA NI BANEWhere stories live. Discover now