BABI NA HUDU

172 20 0
                                    

Hankalinshi a kwance ya bude kofar Ofis din, sannan ya sanya kanshi ciki, had'eda maida kofar ya rufe.
Yana juyowa yayi arba da hancin bindiga a saitin goshinshi, nan take ya fara rawar d'ari saboda tsabar tsorata da firgiji, idanunsa a warwaje, hanjin cikinsa suka taru suka dunkule waje guda kamar zai saki kashi a tsaye, dakyar yake jan numfashi dan razana, ya d'aga hannunsa duk biyu alamar mik'a wuya da sallamawa.

Gabjejen kato ne yayi saitin kwakwalwarshi da hancin bindiga, idanun k'aton jajur, babu alamun tausayawa ko kad'an! da alamun kiris yake jira ya sakar mishi harsashi a kanshi, da ya wulkita Idanunshi kan kujerar zamanshi na Ofis din kuwa wani gabjejen k'aton ya sake arba dashi a zaune yana wasa da hancin bindiga, ya d'aga kafafunshi duk biyu ya d'ora su akan teburin gaban kujerar, kayayyakin amfanin da suke kai kuwa anyi watsi da su a k'asan Ofis din.

   "Kai likita.. Kar ka 6ata mana lokaci.. 'Dakin da aka kwantar da Usher zaka shigar dani, amma kafin sannan ina so ka kalli nan"

Nan take ya d'auko waya a aljihunsa, ya kunna mishi wani vidio sannan ya danna play.
Tsabar tsorata yasa Dr. Habeeb ya fara sakin fitsari a wando, iyalanshi ne gaba d'aya anyi musu daurin huhun-goro.
Ga wasu gabza-gabzan mutane nan zagaye dasu, kuma ko wannensu rike da bindiga, su kuwa iyalan nashi sai kuka suke yi, gwanin ban tausayi.
'Yar karamar yarinyarshi Zahra tana kwance magashiyan a kasa kamar bata da rai.
Matarshi abar kaunarshi daya daga cikinsu ya damk'i gashin kanta da k'arfi, magana take cikin mawuyacin hali da jin azabar dank'an da aka yiwa gashin ta.

   "Dr.. ka taimake mu dan Allah... ka basu duk abinda suke nema su rabu damu... ka ceci rayuwarmu pls... kaga Zahra ma kamar ta mutu..."
Fuskar babban d'anshi Ahmad dan shekara goma sha uku aka hasko, yana cikin matukar galabaita, baya ko iya daga kanshi sama, an bank'reshi ta baya an d'aure hannuwanshi da igiyar daure shanu, gurin sashin d'aurin sai jini yake fitarwa.

   "Zamu sake su idan muka samu nasarar fitar da Usher daga cikin asibitin nan! Dan haka minti goma ke gare ka ka samar mana da hanya mafi sauk'i na fitar dashi, ammafa idan har ka damu da iyalanka. Idan kuwa baka damu dasu ba.."
Ya d'aga kafad'unsa alamun rashin damuwa ya ci gaba da cewa
    "Kana iya mana gardama ko kuma ka k'i nuna mana inda ka 6oye Usher. Kana so in fada maka irin kisan da zan maka?"

Wani kakkauran miyau ya hadiye 'muk'ut' jikinshi babu inda baya kad'awa, ya jik'e da gumi sharkaf. Idanunsa na zube akan wanda ke zaune kan kujerarshi  hankali kwance, yana ci gaba da wasa da bakin bindigarsa.
*****

   "Dr barka da dare, wanene wannan kuma?"
Inspecter Jocob ya tambayesu a lokacin da Dr Habeeb suke kokarin shiga d'akin da aka kwantar da Usher shi da wannan gabjejen mutumin, shima yana sanye da farar riga irinta likitoci.

Matuk'ar jarumta yayi gurin saisaita muryarshi bayan ya tuno halin da iyalansa suke ciki, sannan ya sanya murmushin yak'e a fuskarsa yace
   "Oh! wannan? Dr. Mansur kenan, shi zai karbi aikin daren nan, shi yasa zan nuna mishi komai kafin in tafi gida"

   "Ok no problem"
Ya amsa da haka sannan ya koma gurin zamansa ya ci gaba da game din da yake yi a wayarsa.

   "Good job Dr."
Ya fad'i hakan bayan sun shiga d'akin muryarsa kasa-kasa.
Shammatar likitan yayi ya makure shi a bango ya toshe mishi baki, sannan ya shak'a mishi hodar iblis a hancinshi, yaja sosai kuwa saboda Tsananin tsoro, minti kadan ya tafi lauu... Ya rike Shi dan kar yayi faduwar da zai ankarar da 'yan sandan da suke waje abinda yake faruwa.

Windon d'akin ya duba sai yaga irin mai bud'ewar nan ne, wanda ake yinsu saboda tsaro, yanda ko da gobara ya kama daga ciki za'a iya bud'ewa a fice ta windo.
Da wannan damar yayi amfani ya fice da Usher dake kwance kamar matacce, bayan ya zazzare duk wasu 'karafa da aka jona mishi.

Minti goma tsakani wasu motoci guda biyu suka shigo cikin asibitin, Killer ne da tawagarsa, sunyi mummunar shiga ta bak'ak'en kaya sun rufe rabin fuskokinsu. Kallo daya za'ayi musu a gano tsantsar rashin imani a tattare dasu. Hannayensu rike da muggan makamai.
Killer yana rike da babban bindiga A.k 47 tsirararta. Burinshi idanshi idanun Usher ya aikashi garin da ba'a dawowa.

Suna shiga reception biyu daga cikinsu suka shak'e mai bada kati bayan sun nuna mishi bindiga
   "Dakin da aka kwantar da Usher zaka nuna mana"
Killer ya tambayeshi bayan ya zaro mishi idanuwa kamar zai cinye shi danye.

Dakyar ya iya d'aga hannu yayi musu nuni da cikin asibitin, domin mugun shak'ar da sukayi mishi bazai iya magana ba.
'Daid'aikun mutanen da suke zaune a gurin kuwa tuni suka fara guje-guje suna neman mafaka dan su tserar da rayuwarsu.

Ba ta su yake ba dan haka suka nufi cikin asibitin suna k'ara gyara rikon makamansu, suna wangale duk dakin da suka yi arba dashi.

A daidai wannan lokacin ne kuma Inspecter Jocob ya ankara da abinda ke faruwa bayan yaji shirun yayi yawa su Dr. Habeeb basu fito daga dakin ba, yana bud'e K'ofa yayi arba da likitan watse a gefe d'aya, da sauri yakai Idanunshi kan gadon da aka kwantar da Usher.
Wayam ba shi ba alamunshi  sai k'arafan da aka jona mishi a zube gefe daya, kuma ba dayan likitan da aka kira shi da Dr. Mansur.

Windo ya gani a bude hakan shi ya ankarar dashi abinda ya faru, da sauri ya fita waje ya sanar da sauran 'yan sandan sannan ya dawo ya dira ta windon don yabi sawunsu, domin ga dukkan alamu basuyi nisa ba.

Farar rigar likitoci ya tsinta gaba da dakin kadan, ya dauka kenan sai yaji harbin bindiga ta cikin asibitin, nan take ya juya cikin asibitin a guje yana kara gyara rikon bindigarshi.

Killer sunyi nasarar gano dakin da aka kwantar da Usher, amma ganin 'yan sanda a kofar dakin yasa suka bude wuta, nan take aka fara musayar wuta da harbe-harbe.

Da tsiya Killer ya samu nasarar shiga dakin, amma wayam baiga Usher ba, sai likita a kwance a kasa, takaici da bakin cikin rashin samun Usher yasa ya sakarwa Dr. Habeeb harbi guda, a daidai lokacin Inspecter Jocob ya sawo kai cikin dakin.

Da matsiyacin gudu Killer yayi wani wawan tsalle ya fice ta windo, Jocob kuwa ya bude mishi wuta, harma ya samu nasarar samunshi a hannu, kamar walkiya ya bace a cikin fulawoyi da duhun dare yana dafe da hannunsa, katanga ya kama ya haye, sannan yayi tsalle ya dire ta baya cikin mawuyacin hali, domin hannunsa sai zubda jini yake yi.

****
Yana samun nasarar haurawa da Usher ta katangar suka saka shi a motarsu, wacce suka aje ta can bayan asibitin, take suka figeta da wani matsiyacin gudu suka harba kan titi, tamkar masu gudun ceton rai.

   "Hello.. Eh komai ya kammala, ku kyale su ku samfe, mu hadu a joint"
Dariya sukayi shi da dayan da yake tuka motar, sannan suka tafa.
Lokaci guda suka juya kujerun baya na motar suna kallon Usher, wanda har zuwa wannan lokacin baisan inda kanshi yake ba.

Suna cikin gudu tayar motarsu ta fashe, zaro ido sukayi a tsorace, karo na farko kenan da hankalinsu ya tashi, gashi basu da safayar taya, kafin suyi tunanin tsaida motar tayar ta fice fit! Nan take motar ta fara watangaririya dasu a kan titi, daga bisani kuma tayi juyin masa sau biyu kofar baya ta bude akai watsi da Usher can bangaren titin, kanshi yayi mugun buguwa da wani murgujejen dutse. shima na bangaren mai zaman banza aka watsar dashi can gefe guda ba tare da yasan inda kanshi yake ba, shi kuwa mai tuka motar saboda ya sanya belt duk juyin masar da motar take yi bata watsar dashi ba, saidai ya dad'e da fita daga hayyacinshi, take motar ta fara ci da wuta.
Karfe goma sha biyu na dare ne a lokacin, babu motoci masu zirga-zirga, sai daidaiku, idan mota daya ta wuce ana daukan lokaci kafin wata motar ta sake giftawa.

   "Ku kuke ganinmu ba mu muke ganinku ba..."
Kb ya fadi haka cike da tsoro a fuska da muryarsa, lokacin da yaji yayi tuntube da wani abu har yana neman kifawa, taga-taga yayi kamar zai kifa amma yayi karfin halin tsayawa daidai, sannan ya haska da tocilar hannunshi mai masifar haske.

   "Kai Baba... Kaga abinda na gani kuwa...?" Ya fadi haka yana haskawa Muver mutumin da yake kwance a kasa magashiyyan.

   "Wannan ai mara lafiya ne Kb, kaga kafarsa ma nannad'e take da bandeji"

Wani mugun tsaki yaja, sannan ya zungure shi da kafarsa, cike da masifa yace
   "Amma kai mugun wawa ne, baka da lafiyar ma saboda kaci kafar kare dole sai ka fito yawo? To idan ka gama hutawar ka kwashe tsamin jikinka ka koma gida.
Baba zo mu ware mu bashi guri"
Kb ya fadi haka yana tangadi, hannunsa rike da kofi cike da koko, wanda suke shafawa a bayan poster sannan su manna a bangon gidajen jama'a.

Shi kuma Muver hannunsa dauke da damin poster da suke mannawa.
   "Haba Kb.. Bai kamata muyi haka ba, ka ga fa kamar ma ba a hayyacinsa yake ba, zo muyi a tara kawai mu watsa shi can gidan, da alamar ma nanne gidansu"
Ya fadi haka yana nuna wani gida da yake can nesa kadan da inda suke tsaye.
Nan take suka kama shi kai da kafa suna ta tangadi kamar zasu kife, saboda duk su biyun a buge suke, dakyar suka karasa kofar gidan, suna tura kyauren gidan kuwa ya bude, sukai watsi dashi a tsakar gidan sannan suka fice.

BARA A KUFAI !!Where stories live. Discover now