******
Tsawon sati guda Ado bai sake yunk'urin tare Fatima a hanyar dawowarta daga makarantar islamiya ba, da alamun kashedin tsohonshi ya shige shi. A tunanin Kamal kenan.Duk tsawon satin Kamaluddeen shi yake raka ta islamiya da boko, sannan idan an kusa tashi zaije makarantar har a tashi su dawo tare, ganin Ado bai sake tare ta ba yasa hankalinshi ya kwanta.
Har tsawon sati biyu babu wani abu da ya faru, dan haka ya sakankance ya ci gaba da bilayin neman aiki ita kuma ta ci gaba da zuwa makaranta.A rana ta goma sha bakwai ne da ya kama ranar wata asabar, Fatima ta tafi islamiya da karfe biyu na rana, ana tashinsu karfe shida na yamma ne amma har aka kira sallar magrib bata koma gida ba.
Da farko basu damu sosai ba, amma ganin har an idar da sallar magriba duhu ya fara shigowa misalin karfe shida da minti hamsin hankalinsu ya fara tashi sosai, a d'imauce ya tafi makarantar amma bai tararda kowa ba, makarantar ma a kulle take.
Gidan malamin su Fatiman ya tafi hankalinshi a tashe yana tambayarsa ina Fatima? Abin mamaki da d'aure Kai tabbatar mishi yayi a wannan ranar ma sam Fatima bata je islamiya ba.
Da mugun tashin hankali ya sake bin hanyar daga makarantar zuwa gidansu ko zai ganta, saboda tsabar rud'ewa ma ya manta fatimar mutum ce kuma babbar budurwa, domin sai kallon k'asa yake yi tamkar zai tsince ta.
Yana isa gidan ya iske Ummansu itama hankalinta a mugun tashe, harta fara kuka, ta sake tabbatar mishi Fatiman bata dawo ba.
Kofar gida ya fita ya tsaya yai shiru cikin tunani, hannayensa zube a aljihu, tunani yake ina zaije ya nemi Fatiman?
Ita sam ba yarinya ce mai yawace- yawace ba, kuma ita ba mai irin tara kawayen nan bane balle yace ko ta biya gidan wata kawarta, kuma basu shak'u da danginsu ba balle yace ko can taje.
"To ina zata je???"
Ya tambayi kansa a fili.Tunanin da ya fad'o mishi a zuciya ne yasa ya girgiza kanshi da karfi, da wani matsiyacin gudu ya nufi gidan kamar mahaukaci, a lokacin har an idar da sallar isha'i shi kuwa ko magrib baiyi ba.
Yana zuwa ya fara buga kofar gidan da karfi, duk wanda yaji bugun zai tabbatar babu lafiya.
Kusan duk iyalan gidan sun fito harabar gidan don ganin mahaukacin da yake yi musu wannan mugun bugun, har da shi kanshi mai gidan. Tafasa kawai yake yi yana jiran fuskar wanda zai bayyana, yanzunnan ya shiga cikin gida dan ya samu ya huta amma matsiyatan 'yan maulan nan baza su barshi ya huta ba.
Tunanin da yake yi kenan a zuciyarsa.Maigadi yana bud'e gidan ya fad'a ciki a guje kamar wanda aka jefo, kansu ya nufa gadan-gadan.
Idanunsa cikin na Ado ya kai mishi wata wawan raruma ya watsar dashi a kasa, kanshi yayi da naushi ta ko ina, cikin mintina da basu gaza biyu ba ya hada mishi jini da majina. Duk yanda mai gadi da chairman suke k'ok'arin kwatar Ado a hannunsa sun kasa
"Ina k'anwata..? Dan ubanka ina ka kaimin k'anwata...? Ka fito min da k'anwata kafin in Kashe ka a gurin nan...!"
Ihu yake yi kamar mahaukaci yana maimaita wad'annan kalaman, hannuwansa duk biyu yasa ya shak'e shi kamar zai kashe shi.
Ado sai k'ok'arin k'watar kanshi yake yi, domin ba k'aramin shak'a yayi mishi ba.
Duk abinda Chairman ya rarumo buga wa Kamaluddeen yake yana fadin
"Dan Ubanka sakar shi, sake min d'ana ko ka 'kare rayuwarka a gidan yari"
Kamal ko gezau baiyi ba, saima k'ara shak'e Ado yake yi idanunsa sun kad'a sunyi jajur! Ga dukkan alamu bashi cikin hayyacinsa.Mahaifiyar Kamal da k'anwarsa sai kuka suke yi, dukda dare ne gidan har ya fara tara mutane.
Baiji isowar 'yan sanda ba sai kawai yaji hancin bindigogi a saitin kanshi
"You are under arrest"
Abinda d'aya daga cikin 'yan sandan ya fad'a mishi kenan suna k'okarin banbare hannunshi daga wuyan Ado.
YOU ARE READING
BARA A KUFAI !!
Short StoryDaga jin sunan littafin kunsan duk hasashen mai hasashe bai isa ya hasaso abinda labarin ya k'unsa ba. Sank'ame a cikin wannan labarin sunk'i-sunk'in matsalolin da muke fama da su a wannan k'asar tamu ce. BARA A KUFAI!! Allah ya tsare mu da bara a k...