Yanda yake ta kai-kawo a tsakiyar falon kamar mai yin safa da marwa shi ya k'ara bayyana tsananin tashin hankalin da yake ciki.
Babbar yatsarsa ya sanya ya sharce wata zazzafar gumi da take tsiyaya mishi a goshi, dukda sassanyar sanyin AC da ya wadaci lungu da sako na babbar falon.
A karo na barkatai ya sake warto d'aya daga cikin wayoyinshi da yai watsi dasu a kan d'aya daga cikin kujerun falon, wata lamba ya lalubo ya danna kira, sannan ya kara a kunnenshi, nan take kiran ya shiga, ya fara ringing alamun samun wanda yake nema a wayar.
Murmushi ya sake alamun fara samun kwanciyar hankali, karo na talatin da takwas kenan yana kiran lambar na'ura tana sanar dashi wayar a kashe take, sai a yanzu yayi nasara kiran ya shiga.
"Halllooooo..."
A ka furta daga can bangaren cikin muryar k'wayancewa.
"Hello... Hello... Killer kana jina...?"
Ya tambaya daga bangarensa muryarsa har tana hard'ewa tsabar damuwar da yake ciki.
Tsawon dakiku goma sannan aka amsa daga can bangaren
"Ina jinka Honorable.. Ya harkoki...?"
"Killer..? Kana ina ne?"
Ya sake tambaya ba tare da ya amsa tambayar da aka mishi ba.
"Ina rami Honorable.. Na nisance ka ne kamar yanda ka bukata.."
Aka sake amsawa da k'yar daga can bangaren, ana magana ana ciccijewa, alamun mai maganar a buge yake, mankas yayi da kayan maye da suke gusar da hankalin d'an Adam.
"Ka saurareni da kyau Killer, an samu matsala.
'Yan sanda sun samu nasarar kama Usher, bisa ga dukkan alamu kuma a shirye yake ya fad'i gaskiya, shiyasa nake so kabi duk hanyar da zaka bi ka kashe shi, Ka kashe shi Killer..! bana bukatar ya sake kwana guda a duniyar nan. Idan ka aikata hakan tabbas zaka dawo kan matsayin sa, sannan zan k'ara maka da kyautar naira miliyan goma.. Da dank'areriyar mota, kuma zan baka 'yanci fiye da yanda kake tsammani..."
'Kit' kiran ya katse ba tare da ya gama maganganunshi ba.
Wata wawuyar murmushi ya sake, domin yana da tabbacin Killer ya gama jin duk abinda yake muradi.
Hurgi yayi da wayar gefe d'aya ba tare da ya duba tsadarta ba, sannan yayi wata mugun sufa ya dira akan kujera yayi d'ai-d'ai, tunawa da yayi matsalarsa ta kusa zuwa k'arshe yasa shi barkewa da wata mahaukaciyar dariya.
Ya san Killer bazai ta6a bashi fad'uwa ba, domin ba wannan ne karo na farko da ya saka shi aiki mai mugun hatsari ba, kuma ya ci nasara, ba tare da yabar wata kafa da asirinsu zai iya tonuwa ba.
A can bangaren Killer kuwa kallo yabi wayar dashi, da ya fahimci ta mutu ne sanadiyyar rashin caji yasa ya aje ta gefe guda, wata wawuyar mik'a yayi yana jin tsananin farin ciki a zuciyarsa.
'K'as.. K'as.. K'us..' Karar da kasusuwan baya da na hannunshi suka bada kenan.
Ya dad'e yana jiran wannan ranar, domin ba tun yanzu ba yake tsananin jin haushin Usher, wanda daga zuwanshi gurin Honorable ya k'wace mishi muk'amin da ya shekara goma yana aiki a wulak'ance kafin ya samu.
Shegen yaro ne Usher, ga d'an banzan kwakwalwa da basira, shiyasa a cikin shekara d'aya da rabi ya zarce kowa a gurin Honorable Lado.
K'wafa yayi, sannan ya cije gefen bakinsa na dama, a zuciyarsa yake tanadin kalolin azabar da zai ganawa Usher kafin ya shek'a shi garin da ba'a dawowa.. Wata muguwar dariya mai barazanar fasa dodon kunne ya fashe da ita, tsawon mintuna uku yana k'yak'yatawa, sannan ya yunk'ura ya mike zaune, daga bisani ya mik'e ya fice daga Kogon dutsen, hannu biyu yasa ya kare ranar da ta haske mishi fuska, kwananshi biyu kenan yana cikin Kogon, ba abinda yake yi sai bankawa cikinshi hayak'i da kayan maye, ba sallah ba salati.
**** **** ****
Tun daga nesa rugugin jiniyar motocin 'yan sandan ya mamaye kan titin da zata sada mutum da asibitin Barau Dikko da ke cikin garin Kaduna.
'Yan jarida suna tsaye cirko-cirko suna jiran k'arasowar motocin, motoci hud'u ne na 'yan sandan, suna fakawa daya daga cikin 'yan sanda ya fito da sauri ya k'arasa ya bud'ewa Kwamishinan 'yan sandan K'ofa.
Yana sa kafarsa a waje cincirindon 'yan jarida suka yanyame shi tamkar tarin k'uda je kowa da irin tambayar da yake jefo masa.
"Yallabai wane bayani zaka yi mana akan wannan mai safarar miyagun k'wayoyin da kuka kama??"
Kusan dukkansu wannan tambayar suke ta maimaitawa suna binshi da sassarfa hannayensu rik'e da abin magana, a hannayen wasu kuma manyan wayoyi.
Su kuwa 'yan sanda sai ture su suke samarwa da kwamishina hanyar shiga cikin asibitin.
"Yallabai... Yallabai... Dan Allah ka bamu bayani ko da ba yawa Yallabai..."
Bai ko juyo ya kalle su ba har ya dangana da cikin asibitin, su kuma 'yan sanda suka kare k'ofar dan kar 'yan jarida su shiga, wasu 'yan sandan kuma suka bishi a baya da sassarfa.
Duk inda ya ratsa kallonshi ake yi, Dakakke kuma tsayayyen jarumin 'Dan sanda ne wanda kallon Idanunshi kad'ai ke kad'a hanjin 'yan ta'adda da masu aikata miyagun laifuka.
Yana isa cikin reception d'in asibitin yaja ya tsaya ya k'urawa makeken talabijin d'in da yake manne a jikin bango ido, yana saurarar labarun duniyar da ake karantawa a daidai wannan lokacin."An kama shararren mai saida miyagun k'wayoyin nan wanda aka fi sani da Usher, 'Yan sanda sunyi iya bakin kokarinsu sun sami nasarar kama mai saidawa mutane kwayoyin sun sakaye shi.
A inda sam bazai samu nasarar gudu ba balle har yayi nasarar tserar da rayuwarsa.
Usher mai safarar miyagun kwayoyi, a jiya ne dai aka samu nasarar damk'eshi bayan bata-kashin da ya gudana tsakaninsa da 'yan sanda.
Wanda a sanadin haka har suka harbeshi a kafa, a yanzu dai yana asibitin Barau Dikko ana jinyarsa, inda 'yan sanda suke jiran farfadowarsa dan su sami muhimmin bayanai daga bakinshi..."
Da sassarfa ya wuce kai tsaye zuwa 6oyayyen d'akin da aka kwantar da mai laifin ba tare da ya tsaya sauraren k'arashen labaran ba."Dan Allah ku kula dashi ina zuwa.."
Abinda likitan ya cewa 'yan sanda fiye da goma da suke tsaye cirko-cirko rike da makamai a k'ofar d'akin kenan.
Ganin k'arasowar Kwamishinan yasa likitan juyawa cikin d'akin suka rufa mishi baya.
Yana kwance tamkar matacce, an mak'ala mishi injin taimakawa gurin yin numfashi, ga k'afarshi guda nannad'e da bandeji, ba zaka taba tsammani yana numfashi ba sai ka ta6a kirjinsa daidai saitin zuciyarsa.
"Barka dai likita, ya jikin nasa?"
Abinda Kwamishinan ya fara tambayarsa kenan bayan sun isa babban ofishin likitan.
"Eh to da sauki dai, a ko wane lokaci daga yanzu zai iya farfad'owa. Bugun zuciyarsa yana tafiya yanda ya kamata"
Gyad'a kai yayi alamar gamsuwa, sannan ya fito daga cikin d'akin likitan yana biye dashi a baya
"Ka kula dashi, Inaso ka ci gaba da kulawa dashi, domin shi d'in da kake gani ba k'aramin mai hatsari bane, zan fad'awa jami'an mu su ci gaba da bada kulawa mai tsanani a kanshi, domin a sashin mu muna matukar neman bayani daga bakinshi.
'Usher' Fitinanne kuma hatsabibin mai safarar miyagun k'wayoyi, sau ashirin da tara muna harin kama shi amma sai ya samu hanyar tserewa, sai jiya Allah ya bamu sa'a a kanshi"
"An gama Yallabai"
Likitan ya amsa cike da gamsuwa, a zuciyarsa yana jinjina k'ok'ari da hazak'ar 'yan sandan, musamman ma Kwashina Sunusi Isa.
"Kana ji Jocob?"
Kwamishinan ya maida hankalinshi kan d'aya daga cikin 'yan sandan da suke tsaye a kusa dashi.
"Eh Yallabai"
Jocob d'in ya amsa da sauri.
"Ka kula dashi, ka kula da duk wani motsi nashi da shige da fice, karka kuskura ka bar kowa ya shiga gurinshi idan ba likita ba, idan nace kowa to ina nufin ko ma waye, komai girman matsayi da shahararsa"
Ya k'arasa maganar cikin sigar zazzafar gargad'i da Jan kunne.
"An gama Yallabai"
Ya amsa da hanzari, ya sara masa cike da
kwarewa.
Gyad'a kanshi yayi alamar gamsuwa ya nufi hanyar ficewa daga asibitin gaba-daya, duk inda ya wuce 'yan sanda ne suke sara masa sannan su bi shi a baya da sauri.Follow
Vote
Comments
Share
KAMU SEDANG MEMBACA
BARA A KUFAI !!
Cerita PendekDaga jin sunan littafin kunsan duk hasashen mai hasashe bai isa ya hasaso abinda labarin ya k'unsa ba. Sank'ame a cikin wannan labarin sunk'i-sunk'in matsalolin da muke fama da su a wannan k'asar tamu ce. BARA A KUFAI!! Allah ya tsare mu da bara a k...